Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 67

Chapter 67

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na ɓakinciki da jin zafi, yanzu irin wannan mutunen ne na haihu da shi? Ina baƙincikin da ya kasance uban Noor sam, ɗa na be yi dacen uba ba, dan haka ban zan nuna masa ko kuma faɗa masa cewar Jibril ne ubansa na gaskiya ba. “Bana neman mata Naj, Aisha ce kawai na ke taraiya da ita ma kuma na daina na tuba, cocaine ɗin ma akwai dalili shanta da na ke, amman na ji kamar kin yi wata magana, na ji kin ce ɗa me kike nufi akwai abunda ya kamata na sani ne?” Ganin yadda yake matsowa yasa na yi hanzarin miƙewa tsaye har ina ɗauke numfashi, shi kuma yana ta kallona kamar mai karantar abu a fuskata, sai takowa yake har sai da ya kowa daf da ni...! “Ina da ɗa ko Nawwara...?” ____________________________________ Zaku ga wasu kalmomin kamar ba a ƙarasa ba wasu kuma ana mistakes da yawa ana dai akwai errors or omissions a ciki, hakan yana faruwa ne saboda rashin editing, idan har na ce zan tsaya editing zai ɗauke ni tsawon lokaci ban yi updated ba domin editing ya fi bani wahala fiye da typing. Fatar zaku fahimta kuma zaku min uzuri 🙏 FOLLOW ME VOTE COMMENT SHARE *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee* 4⃣0⃣ JIBRIL POV. “Ee kana da ɗa” Shine kawai abunda Jibril yake son jin ya fito daga bakin Nawwara, wani irin bugawa zuciyarsa take da sauri, ido cikin ido yake kallon Nawwara tsantsar gaskiyarta yake son ganewa, yadda ta saki baki tana kallonsa shi kansa yasan subul da baka ta yi, yadda take numfashi yake karantar da shi irin faɗuwar gaban da ke ranta. “Kana da ɗa mana ƴaƴama zan ce, ba ka auri Aisha ba ta haifa maka ƴaƴa, na tuna ai tun kamin ka aureta ma ta samu ciki, wanda kake labarwa abokinka farinciki fal a ranka, kuma bayan ita maybe ka ƙara auren wasu matan sun mahaifa maka ƴaƴa ko kuma ka musu cikin shege” Lumshe ido ya yi ya haɗe yawun dake bakinsa ya dunƙula hannunsa ya matse sosai kamar zai dake, har ga Allah baya jindaɗin kalamanta, duk lokacin da ya tuna rayuwarsa ta baya yana jin babu daɗi ballr kuma ace ita ce da kanta take tuna masa da wannan, hakan na karantar da shi cewar ba zata taɓa yafe masa ba kuma ba zata manta ba. “Ina cikin da na barki da shi?” Ya faɗa yayinda da buɗe idonsa da suka rine suka yi ja sosai. “Cikin da ka kace ba naka ba ne? Ai na zubar domin ba zan iya ɗaukar shege a cikina ba” “Ba zaki iya zubarwa ba, ba zaki iya kashe rai ba ko da kuwa ɗan shegen ne da gaske” Kallonsa ta yi sai ta yi murmushi. “Ashe kai da kanka ka san ba ɗan shege na ɗauka a cikina ba, amman ka ce ba naka ba ne ka haɗa hotona da hoton wani namiji wanda ban taɓa sanin inda ya fito ba, saboda kawai kana neman rabuwa da ni? Da na dawo da ciki sai suka kira da karuwa wannan dalili yasa na zubar da cikin” Ta faɗa hawaye na fitowa daga idonta fuskarta kuma ɗauke da murmushi. Wani irin ƙuna yake ji a cikin ransa, zuciyarsa zafi take kamar an kunna masa wuta, yana jin rashin kyautawa a duk lokacin da ya tuna abunda ya aikata mata, tabbas yanzu ya yarda akwai wawanci, shashanci a tare da shi, duƙursawa ya yi ƙasan guiwoyinsa ya kama Hijabinta sa gashi yana hawaye. “Dan Allah Nawwara ki yi haƙuri dan Allah ki yafe min” “Daman na faɗa, saboda ka riƙa neman yafiyata yasa ka cilasta min aiki a tare da kai” “Ba dan haka ba ne Nawwara, saboda na samu kusanci da ke, ina sonki sosai Nawwara” “Ni kuma bana son ka, bana kaunarka Jibril” “Na sani” Ya fada yana hade maganarta ciki da dacin rai. Zaunawa ta yi shi kuma ya mike tsaye na koma office dinsa, sam be gamsu ba shi da tsakaninsa da Nawwara ba, tabbas ya bar ta da ciki kuma ya san ba zata iya zubar da cikin ba. ‘Ta haife shi, idan har babu haihuwa tsakamina da ita mi zai sa ta yi wannan maganar?’ Shine abunda zuciyarsa take ta raya masa, wayarsa ya dauka ya kira Siraj bugu biyu Siraj ya yi picking. “Siraj ina son kasa a bincika min duk wani abu da ya shafi Nawwara, akwai da a tsakanina da ita Siraj kasa a abincika min” “Okay” Daga haka ya kashe wayar ya kira Abbah, sai da ta dade tana ringing sannan ya dauka yana kiran sunansa. “Hello” “Jibril” “Abbah ina wuni” “Lafiya kalau ya aiki?” “Al-hamdilillah, Abbah akwai da tsakanina da Nawwara” “Waya fada maka?” “Ita ta yi subul da baka” “Kaje gidansu ko? Bana fada maka karka je ba” “Ban je ba, Abbah a nan kamfanin take aiki” “How when?” Ya kwashe komai ya fada ma Abbah amman be fada masa zance ya cilas mata aiki a tare da shi ba. Abbah ya yi shiru kamar mai tunanin abunda zai ce. “Abbah we're meant to be” “Kana son ta ka saketa? Bana son ka zama cikin irin mazan nan da ake fada Jibril ni yanzu ko wani aure ban yarda ka kara yi ba sai ka gane kuskurenka” “Wallahi Allah Abbah na canja zan zauna da Nawwara zama na tsakani da Allah ba zan taba sakinta ba, Abbah ita kadai ce take so na tsakani da Allah” “No ba yanzu, kuma na fada maka karka kuskura taka kafarka gidan nan” “Tau Abbah ba zan yi ba, amman da Mahaifiyata tana da rai da ta roka min kai ka amince, rashinta ne yasa na rasa komai, ba ni da mata ba ni da ɗa sai kai kadai kai kuma ka kasa fahimta ta” Yana fadar haka ya kashe wayar ya aje saman table, sai ya dora hannayensa saman table din ya dafe kansa ya dinga rusar kuka kamar karamin yaro. Kuka yake sosai kuka ina zai saka kanshi, kuka neman mafita, be san mahaifiyarsa ba domin be tashi tare da ita ba, amman yana jin zafin rashinta kamar yanzu ta mutu ta barshi, ji yake ina ma tana raye da yanzu ta roka masa Nawwara ta yafe masa, ta shiga cikin lamarinsa ta gyara masa komai, be taba jin zafin rashin mahaifiya ba kamar yau. Hannunsa yasa ya janyo aljihun table din da take zaune ya dauko hoton wata matashiyar mata mai kama da shi yana ta kallonta yana kuka kamar mace. Kuka ya yi sosai har sai da ya soma jin kamar jiri yana dibarsa sannan ya tashi ya shiga bathroom ya wanke fuska ya dawo ya dauki ruwan freezer ya sha, sai ya dora gorar saman freezer ya nufi kofar fita. Ko da ya fito Nawwara na zaune tana duba abubuwan da suke cikin computer, ya samu thirty seconds yana kallonta mugun burgeshi take gani yake a duk duniya babu wata mace da ta kaita daraja da kima da kuma kyau, ji ya yi kamar yaje ya rumgume kamkam a kirji, sai dai yasan ba shi da wannan damar. Karasa ya yi inda take yana kallonta da manyan idanuwansa masu kamar madara kamar

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});