Chapter 2
Chapter 2
na haskawa a fitila anjima” Cewar Inna, ni kuma na amsa da “Okay” Tare da unƙurin tashi na cire hijab domin alwala. Ko kamin na yi alwala na gama, har sun cinye tuwon abun ka da masu jin yunwa. Bayan na gama Sallah Magariba Habiba ta miƙo min ɗan tuwo can laƙe ga kwano. “Gashi nan ke da Noor” Karɓa nayi na aje a gabana. Sai ga Baba ya shigo yana faɗin. “Bari naje gidan ciyaman na jirashi, ko Allah zai na samu wani abu, sai mu karya da safe” Wani abu naji ya zo ya tsaya min a zuciya, wanda ya saba tsaya min a duk lokacin da Babanmu zai je yawon maula. Ina jin lokacin da Inna ta ce “Allah ya tsare” Habiba kuma ta ce “Baba ga tuwon dawa” “Ina aka samo tuwo?” “Nawwara ce ta samo gidansu Maman Nura” “Ku cinye, sai na dawo” “Allah ya bada sa'a” Da Amin ya amsa, sannan ya fice. Ni ko na aje carɓin da ke hannuna, na miƙe tsaye ina amsa sallamar Noor. “Momy a ci abinci gidan Maman Hajara, tace na faɗawa Mama Habiba ta zo ta ɗauki tuwo, Momy har da kifi a miyarsu” Duk dariya muka sa masa, daman Noor be iya cin daɗi ba, komai ya ci sai ya bada labari. Yasa hannunsa aljihu ya ciro batir ɗin ya miƙawa Inna, sai ya sake saka ɗayan hannunsa a aljihu ya fiddo kifi ɗan tsito ya miƙa min. “Momy ungo na rage miki, ci ki ji” Kai na girgiza masa. “Cinye abun ka nima zan je can na ci” “Yarinya ya ƙare ai” “Ni ce yarinya?” Na tambaya ina nuna kai na, sai ya sa dariya yana tsalle. Haka rayuwarsa take ba duk abu ne yake damunsa ba, ko da bai fahimcin inda duniyar ta dosa ba ne oho. ______________________________________ As i said bayan ZAGON K'ASA zan yi RAI BIYU kuma free. 😍 How do you like my surprise 🤔 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣ Bayan mun yi sallah isha'i Inna take labarta min irin dukan da ka yi ma Noor a makarantar islamiya yau saboda rashin biyan kuɗin sati biyar. “Momy duba nan bulala ya kwanta min” Ya faɗa yana nuna min hannunsa fafaren idanuwansa na cika da hawaye. Abun ka da farin mutun bulalar ta masa ja sosai kwanci jini ya kwanta a hannunsa. Hannunsa na kama ina murmushi. “Ai lada kuke samu idan aka dake ku” “Ni ba zan sake zuwa ba, Malam Usman azzalumi ne” Ya faɗa yana taɓe pink lips ɗinsa. Sai na yi saurin rufe masa baki. “Ba a zagin malami Noor kar na sake ji” Habiba ta bige min hannu. “Wallahi bar shi ya faɗa in ba zalumci ba miye na dukan ƙaramin yaro kamar Noor, ai dai yasan babu kuɗin ne da yanzu an bada, ji yadda ya bugar masa fatar hannu har ta yi ja, yaro ba a saba dukansa gida ba haka kawai wani ƙato zai dake shi” Taja hannunsa suka fita waje ta shimfiɗa tsohuwar tabarma suka zauna, ni kan murmushi ne nawa, masifa ai Habiba ta iya ta har ta gaji musamman akan Noor duk wanda ya taɓa zai ga babu kyau. Baba be shigo gida ba sai goma har da kwata a lokacin har Inna ta soma bachi, balle kuma Jamila da Sakina ba mota, daman su da anyi sallah isha'i suke bachi. Ni da Habiba ne kawai ba mu yi bachi ba, sai Noor da ke faman ƙirga taurariya, ina daga cikin ɗaki Baba yayi sallama, Habiba da Noor da ke waje suka amsa masa. Motsin rufe ƙofar gida da Baba ke ƙoƙarin ne ya tashi Inna daga ɗan guntun bachi da ta fara. “Malam ka dawo?” Ta faɗa tana gyara ɗaurin ɗankwalinta, shi kuma ya amsa mata fuskarsa da damuwa sosai. “Na dawo amman ban samo komai ba” “Ciyaman ɗin be dawo ba ne?” Inna ta sake tambaya. “Ya dawo amman be fito ba kuma be ce mu shigo ba, sai kawai aka rufe gate” Kai na girgira kana ka ce “Ai ba zaku samu ba, zai ce kullum kuna zuwa kuma masa maula a ƙofar gida, wata rana wulaƙancin ma sai ya fi haka, ni Wallahi Baba da ma zaka ji shawarata da ka daina zuwa gidan kowa roƙo yana zubar da mutunci da ƙimar mutum take” “Zuwan ne ai ya zame mana dole tun ba babu wata sana'ar yi mai ƙarfi, tsaran icce ne ba kullum ake samu ba, jarin kuma mun cinye rayuwa ta yi tsada yanzu, dole sai mun haɗa da haka indai kana gida babu wanda zai ɗauko ya aiko maka. Ga ɗari na ranto gurin Malam Sahabi, da safe a karya” Ya ciro naira ɗari a aljihunsa ya miƙawa Inna. Baba yana da gaskiya ba ko wane mai kuɗi bane mai zuciyar tausayi da taimako mafi yawansu kansu suka sani. Unƙurawa na yi na tashi, na nufi ɗakinmu da muke kwana a ciki. Ganin haka yasa Habiba ta shigo da Noor sai ta koma ɗakinsu Inna ta taso da su Jamila da Sakina. WASHE GARI... Bayan na yi sallah asuba na zauna ina askar na safe da na saba yi a duk lokacin da na gama Sallah. Misalin ƙarfe bakwai da rabi Jamila taje ta siyo mana koko na naira ɗari, aka rarraba haka nan aka sha gayarsa ba tare da suga ba muka sha. A lokacin ne Sakina ta yi ma Noor shirin makaranta, ta kama hannunsa shi da Jamila tana cewa sai sun dawo. Har ya tafi sai ya sance hannunsa daga na Sakina yazo a guje yayi min kiss a goshi, sannan yayi min bye-bye yana dariya suka fice. Ban san inda ya samo wannan dabi'ar ba, ni dai nasan ban taɓa masa sumba idan zai je makaranta ba, ban kuma saba masa idan zai fita ba, amman shi yana yawan min a duk lokacin da zaije Makaranta. Sallama muka ji ni da Habiba dake saka wandon makaranta. “Daga ji Malam Hamisu ne, yabi ya takura mana akan kuɗin haya da be taka kara ya karya ba, baƙin Azzalumin banza mugu mtsss” Ta ƙarasa tana jan tsaki. Na tada kai na kalleta. “Kowa a gurin ki Azzalumi Habiba, ina laifin mutumen yana ɗaga mana ƙafa dai-dai gwargwado ke kin san da wani gurin ne da yanzu an koremu, amman kowa ki riƙa kiransa da Azzalumin hakan be dace ba sam” Kamar jira take sai tayi cikina da faɗa. “Kowa Azzalumine Nawwara na faɗa, waya kula da halin da muke ciki har ya damu kowa dai kansa ya sani, na faɗa kowa na duniyar nan Azzalumi ne” Tana kaiwa nan ta saka farin hijabinta ta ɗauki jakarta ta fice ina mata Allah ya shirya. Bayan ta fita na tashi ya leƙa ɗakin Inna dan yi mata ina kwana. “Lafiya ƙalau Nawwara Allah yasa dai kin sha kokon dan nasan halin fa” “Na sha Inna, har sai da na raga” Na faɗa ina dariya, sai ga Baba ya shigo. “Baba ina kwana?” “Lafiya ƙalau Nawwara an tashi lafiya” “Lafiya ƙalau, ya lafiyar jikin” “Alhamdullilah, Hamisu ne ya zo na ce yayi haƙuri har zuwa satin sama, sai dai ya ce daga wannan ba zai ƙara ɗaga mana ƙafa ba” Ya faɗa yana zama kusa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119