Chapter 106
Chapter 106
mana” “Amin Amin shiyasa ake son ka yi taka tsantsan da mutanen duniya ai” Tayi min wani kallo sai kuma ta mike tsaye tare da daukar jakarta ta yi min sallama ta fice. Inna ta zo ta zauna kusa da ni tana fadin “Ki yi hankali da wannan ma domin kin san ba yarinyar arziki ba ce” “Na sani Inna amman Allah ya fita kuma shi zai tsare mu” “Haka ne” Firar Siraj muka bijiro da ita, a nan nake labarta Inna wasu abubuwa da bata sani a lokacin da ina aiki tare da shi, mun dade muna fira mutane kuma nata shigowa suna mana barka da dawowa ga Noor a tsakar gida yana da game da dayar wayar Jibril daya bar masa ya buga game kamin ya karba. Bayan sallah magariba Bilal ya kira ni i was very surprised da na ga kiransa domin rabon daya kirani har na manta, gabana ne ya shiga faduwa sosai sai kuma tsoro ya kamani kamar ba zan daga ba sai kuma na daure na dauka, na yi tunanin wata maganar zai fada min sai ya ce min gashi nan kofar gida na fito. Sai da na canja Hijab din da ke jikina sannan na sanar da Inna itama kanta ta yi mamaki, ni dai jikina a sanyaye na fito. Sai na same shi a daidai inda ya saba tsayuwa yana jingine da ginin gidanmu sanye da kananan kaya. “Assalamu Alaikum ” Sai ya dago ya kalleni, sai kuma ya yi murmushi. “Kin tsorata ko sarkin tsoro?” Na yi shiru ban ce masa komai ba, sai ya sauke ajiyar zuciya ya ce “Ki yi hakuri da duka abubuwan da suka faru, na so naje ganin Noor asibiti sai dai ban samu dama ba, saboda Mama ta furta cewar bata yafe min ba idan na taka asibiti ganin Noor ke ko waya na kira na tambaya jikinsa bata yafe min ba, wannan dalilin ne ya hanani zuwa ganinsa” “Ba komai, Mama tana hujja ai nima kuma ban kyauta ba” “Babu abunda kika na rashin kyautawa, face fifita son Jibril akan nawa da kika yi” “Haba Bilal karka dauki zigar mutane mana duk wanda ya fada maka haka ya yi maka karya” “Ba fada min aka yi ba, gani na yi da idona” “Babu abunda ka gani Bilal kawai kana son ka yi amfani da wata damar ne ka ci min fuska” Sai ya gyara tsayuwarsa ya kalleni “Ki rantse min da Allah a yanzu nan babu son Jibril a zuciyarki!” Sakin baki na yi ina kallonsa sai idanuwa suka cika da hawaye, na kasa karyata kaina balle kuma na karyata shi, Allah yake son na rantse da shi taya zan yi rantsuwa akan abunda ba ni da tabbaci ni kaina a yanzu ba zan iya cewa akwai son Jibril a zuciya ko babu abu. “Kin gani? Kina son shi har gobe Nawwara, dan haka karki yaudari kanki, wannan dalili yasa na ke jin kamar ba zan iya aurenki ba saboda zuciyarki tana gurin Jibril ko da na aureki gangar jikinki kawai na aura” “Wannan ne kawai dalilin?” Na tambaya hawaye na bin fuskata. “Ba wannan ne kawai ba, mahaifiya bata son ki Nawwara kowa ma a gidanmu baya son ki sai ni, wani lokacin abunda iyaye basa so babu alheri a cikinsa, and ko na aureki ba zamu taba jindadin zaman aure ba abubuwa za su yi ta faruwa wadanda ba zasu mana dadi ba. Ban yarda Jibril ya fini son ki ba, amman na yarda son ki yafi yima Jibril illa sama da ni, Nawwara Jibril yana da ciwon zuciya wanda zata iya bugawa a kowa lokaci ta rasa ransa kuma ke kadaice maganin wannan ciwon nasa, na san zakiyi mamakin inda na ji ko? Na samu labarin ne ta hanyar abokan aikinmu da muka yi aiki a kamfaninsa tare, idan na aureki a yanzu na shiga tsakaninki da muradin zuciyarki kuma na shiga tsakanin Noor da Jibril na raba masa hankali gida biyu, Last two weeks da suka wuce Jibril ya kirani muka hadu a Shukura Hotel da shi, kin san abunda ya yi min? Gafarata ya nema akan abubuwan da suka faru kuma ya rokeni da na rike masa dansa amana kuma na tarbiyantar da shi, da za ayi gasar son ki Nawwara da ni zan zama gwani kuma zakara, amman a wannan lokacin sai da na raina kaina saboda tausayin Jibril da ya kamani, saboda ya canja Nawwara saboda ke mutumen da baya kallon kowa da kima amman har ya nemi ya yafe masa kuma na masa alkawarin ba zan bari komai ya samu dansa ba, har ma ya yi ikirarin mayarda ni aikina, but yanzu idan baki aureshi ba kin san irin halin da zai shiga? Wata kila rayuwarsa marar kyau zai koma yi, kuma Noor ma ba zai ji dadi ba domin a yanzu ya saba da mahaifinsa, ya kamata ace shi ma yasan dadin mahaifa kamar ko wane da, Dukan abunda Jibril ya yi miki abaya ya yi ne a cikin jahilci yanxu kuma ya dawo yana neman yafiyarki ya kamata ki yafe masa he deserved a second chance so that ya gyara duka laifin da kuskuren da ya yi, kuma shi ya fi cancanta da ya zauna da ke a yanzu saboda ya goge miki zargin da duniya take miki, kuma zaki samu ingattaciyar rayuwa ke da iyayenki wacce ni ba zan iya baki ita a yanzu ba, ko da zan iya baki sai nan gaba amman shi yana da abun duniya wanda ya kamata ace kema kin jidadi kuma kin more hakurin da kika yi, Abu na karshe da zan fada miki shine, dukan mu ran mu a hannu Allah yake, amman masu ciwo irin na Jibril basa dadewa a duniya, kuma Jibril be da wanda zai iya tsawata masa a yanzu sai mahaifin da bashi da lokacinsa, ga jarabasar cin amanar da Siraj yayi masa wannan kadai ya isa yasa ki tausaya masa, ina son ki Nawwara amman son da nake miki na ki samu farinciki ne bana na aureki ba yan uwana da iyayena su saki a gaba, kuma ina son ki auri Jibril ko dan saboda Siraj da Zinatu, domin idan baki aureshi ba mamaki ya auri Zinatu wanda baki san iya abunda hakan zai haifar ba” Hawaye nake babu kakkautawa kamar yadda shi ma yake. “Kar tausayin wani yasa ka cutar da kanka kuma ka cutar da ni Wallahi ina son ka Bilal ina sonka sosai” “Na san kina so na, amman ko mun yi aure zamu yi ta samun matsala ne kawai Nawwara, kuma ina da kishi sosai ba lallai ne muji dadin zaman aure ba, na san yanzu ba zaki fahimta ba, amman a nan gaba kadan zaki gane gata ne na yi miki kuma na yi ma kaina, ni dai zan bi zabin iyayena wanda ina tunanin Allah zai bani wacce zan so siye da ke saboda na yi ma iyayena biyayya, kuma in da rabon na aureki sai kiga na aure ki din gaba” Durkusa na yi a gurin na hade hannayena ina rokonsa “Ka yi ma Allah da annabi ka aureni Bilal zan iya jure duk wani cin fuska da wulakanci da zaka min ko na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119