Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 59

Chapter 59

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

can kiran bashi da muhimmanci” Na faɗa ina ɗauraye kayan da ta fara wankewa, a hankali na ji ta kira sunana. “Nawwara? Kwana biyu nan kin chanja kamar akwai abunda ya ke damunki, ki daina barin damuwa a ranki ki riƙa sanar da ni abunda ya kamata na sani tun wuri” Na tsayar da abunda na ke na kalleta. “Babu komai Inna, kawai ina tunanin Noor ne da makomarsa” “Makomar Noor tana hannun Allah da kuma shi kansa, ki daina damuwa da matsalarsa idan ya girma zai nemi mahaifinsa da kansa ko kuma shi mahaifin nasa ya nemeshi, amman ki daina damuwa arzikinki Noor na mijine ba mace ba” “Amman ni Inna ina ganin kamar ba zan iya ƙyale Noor yaje gurin mahaifinsa ba, bayan wulaƙancin da ya masa ya yi min sai kuma ace na yarda na bada ɗan gaskiya ba zan iya bari Noor ya kusanci wannan mugun mutumen ba” “Ko da ya gane kuskurensa ya nemi yafiyarsa? Ba a shiga tsakanin ɗa da uba Nawwara yanzu kin ga duk wannan abun Noor be san da shi ba aiko abun farincikin ki idan har yau Allah ya kawo babansa ya nemi ɗansa da kansa” Idona ya cika da ƙwalla. “Amman Inna kamar akwai ƙwaruwa a ciki, ku kuka raini yaron nan sai kuma a ɗauka a miƙawa uban bayan uban be san darajarsa? Gaskiya ni ba zan iya yafe masa ba” “Ban ce ki yafe masa ba kuma ban ce karki yafe masa ba, amman bashi ɗansa kan dole ne indai har ya buƙaci haka, yara su tashi a gidan iyayensu maza yafi daraja da ƙima fiye da iyaye mata, ke kanki zaki fi jindaɗi na san ba zaki so Noor ya yi agolanci ba, saboda ba ko wane uba ne yake son a kawo masa ɗan wani a gida ba, ba duk miji ba ne zai so ki ya so ƴaƴanki, ni kuma ba burina ki yi ta zama a gida ba bana da natsuwa Nawwara har sai kinyi aure kin zauna ɗakin mijinki” “Amman ai be zo karɓan ɗansa ba kwata-kwata be taɓa sakashi a ido ba, kuma irin wannan mutumen kike goyon bayan na bashi ɗansa?” Na faɗa ina kuka, ji nake kamar da gaske rabani za'ayi da ɗana. “Misali ne kawai na ke baki, ba wai na tabbatar zai zo ba ne, amman zuwansa yana da muhimmanci Nawwara domin zai wanke zargin da mutane suke miki, kuma Noor zai san waye ainahin ubansa na gaskiya” “Ni gaskiya zan maida Noor gurin Gwaggonsa” “Wace Gwaggonsa kuma? Zumuntar uwa suka haɗa ko ta uba da zaki ɗauki yaro ki kai mata saboda kawai kin auri yayanta? Faɗa min abunda kike ɓoyewa Nawwara ko shine yake kiranki?” “Ni ma ban sani ba, amman Inna Noor zai iya rayuwa ko babu babansa a kusa da shi ko da ma ace Ubansa ya mutu” “Allah ya kyau” “Amin” Na amsa ina kuka sosai har da mazina. Ban gama wankin ba sai da aka yi azahar, a lokacin su Sakina suka dawo makaranta, Noor da ciwo a ƙafarsa wai yaje buga Boll ya buge da dutse har jini ya fita. A ranar ba tare da shi suka je Islamiya ba saboda ciwon ƙafan, da suka dawo ne suke labarta mana wai yau sun yi babban baƙo a makarantar su har ya saka gasar karatun sirratul nabiy wacce ta yi ta ɗaya za a bata gida ta biyu kuɗi dubu ɗari biyar ta uku kuma dubu ɗari biyu da hansin, kuma su uku kawai aka zaɓa Sakina sai wasu ƙawayenta biyu. Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindaɗinta har tana addu'ar Allah yasa Sakina ta ci, ya yinda ni kuma na ke ta tunanin kamar ba gasar Allah da Annabi ba ce. JIBRIL POV. Shi kansa ya san ya cancanci a yaba masa akan namijin ƙoƙarin da ya yi na ɗauriyar sauraren kalma mai tsada da Nawwara ta furtawa Bilal. Sai dai tun daga lokacin baya jin sukuni har yanzu, kalmar kawai yake ta ji a kunnensa tana masa yawo kamar wanda zai haddace sautinta. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” Shine abunda ya fi furtawa a duk lokacin da yaji abun ya haye masa zuciya. Safa da marwa yake ta yi a ɗakin ya kasa natuwa guri ɗaya. “Am so so sorry Naj am so so sorry please forgive me” Ya furta yana janye hannun rigarsa sai ga sunanta shimfiɗe a ɗamtsensa da tattoo, shafa gurin ya shigayi ya lumshe ido sai ga hawaye. “I love you so much bana son na zama wani kalar mutum Ya Allah help me” Zaunawa ya yi bakin gado yana ta tunanin abunda zai fissheshi, can ya miƙe tsaye ya saka hannunsa ɗaya ya saka aljihu ya fiddo wayarsa ya danna number Nawwara, haka ya jera mata kira biyar bata ɗaga ba sai ya sake kira na shida ya bar wayar saman madubi ya fita zuwa kitchen ɗan haka wa ƙansa tea. “Hello Momina tana banɗaki idan ta fito zan faɗa mata” Noor ne yake maganar sannan ya katse kiran jin ba a amsa masa ba, a daidai lokacin Jibril ya dawo ɗakin ɗauke da kofin tea, wayar ya sake ɗauka ya duba sai ya ga anyi picking, da sauri ya sake kira sai aka kashe ya sake kira aka sake kashewa sai kawai ya yanke shawarar aika mata da saƙon karta kwana wato sms. Da kansa ya tsara rabutun ya tura mata sannan ya jefar da wayar ya miƙe tsaye ya nufi window yana ta kurɓa tea ɗin zuciyarsa na mugun zafi, ji ya yi ba zai iya jurewa ya aje kofin ya nufi wani ɗakin, da shigarsa ya ɗauko wani akwati ya buɗe ya ɗauki ƙwanƙwaƙo ƙarami ya buɗe sai ga cocaine cikin wata farar leda da sauri ya ɓasge ledar ya zuba garin a hannu yana shaƙa kamar ba gobe. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @KhadeejaCandy *Dedicated to My Asmee* 3⃣7⃣ Ina fitowa daga banɗaki na zauna saman tabarma da na tashi sai Noor ya miƙon wayata da ke hannunsa. “Momy gashi an kira na ɗauka amman ba ayi magana ba” Ina karɓar wayar na duba sai na ga number Jibril number nan ce da ya saba kirana da ita. “Ka yi magana?” “Ee amman ban ce ance komai ba, sai na ce idan kin zo zan faɗa miki sai na kashe” “Na shiga uku Noor miyasa ka yi magana?” Hankalina ya tashi sosai zuciyata na ta raya min Jibril zai gane cewar Noor ɗansa ne. “Momy ban ce komai ba” Ya faɗa ganin yadda duk na bi na rikice, kai na gyaɗa masa naja shi zuwa saman ƙafafuna na zaunar da shi na rumgumeshi, muna haka wayar ta ƙara ringing ina dubawa na ga Number Jibril sai na kashe wayar gaba ɗaya, gabana sai faɗuwa yake, zuciyata na nuna min Jibril zai uya zuwa gidan nan a yanzu ko anjima saboda ɗansa. Unƙurawa na yi na tashi sai ga Jidda ta shigo bakinta ƙumshe da sallama, sai jikina ya ƙara yin sanyi har na ke ganin kamar ita ma tare take da Jibril. “Noor tashi kaje ɗaki yi sauri” Sai da ya gaisheta sannan ya tashi ya nufi ɗakin, ita kuma ta zauna kusa da ni tare da dafani. “Ki kwantar da

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});