Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 34

Chapter 34

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zan ji a gurin Jidda domin bata ɓoye masa komai da ya dangance ni. Ko da na shiga gida wayata na ta ringing ko da na duba sai naga baƙuwar number, kamar kar na dauka sai kuma na ɗauka tare da sallama, sai na ji ba a amsa min ba kuma ba a ce komai ba har na tsawon lokaci, hakan yasa na sake sallamar nan ma shiru har sai da na duba wayar naga mai kiran be kashe ba, na sake karawa nayi sallama a karo na uku ba amsa min ba kuma ba a ce komai ba, hakan yasa na kashe wayar dan da alama mai kiran yana son sauraren muryarta ne kawai duk da ban san ko wanene ba. WASHE GARI... Misalin bakwai da rabi saƙon kamfanin ya sake shigowa, nan ma ban karanta ba na goge, na shigaba da haɗa abun karinmu da nakeyi. Sallamar baƙuwar murya yasa na ɗago daga gaban murhun da nake na amsa mata ina mata kallon rashin sanin, sai da ta gaisheni sannan ta matso kusa da ni ta aje min leda biyu dake hannunta ta ce “Wai gashi inji Ya Mustapha ya ce abawa Nawwara, kuma wai yana mata sannu da jiki” Har na buɗe baki zance mata ta ɗauki kayan ta koma da su sai ga Inna ta fito daga ɗaki tana amsawa kamar tasan ni ba zan amsa ɗin ba. “Mashallah ki ce an gode Allah ya saka da alheri, jiki kuma ya yi sauƙi sosai” Da wannan budurwar ta juya ta koma wacce nake san ran riƙonta ake a gidansu Mustapha domin iyayensa shi kaɗai suka haifa. Tana fita na ɗauki kayan na fice na bar Inna tsaye tana kallon ikon Allah domin nasan idan har na ce yarinyar ta ɗauki kayan ta koma dasu a gabanta ba zata bari ba, amman yanzu bata san mi zanyi ba dole ta saka min ido. Ina fita na yi karo da shi a ƙofar gidanmu sai ya ɗanyi nisa da gidanmu kaɗan yana sanye da jallabiya, daga inda nake tsaye na jefa masa ledodin na juyo abuna. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣3⃣ “Me kika yi kenan?” Ina shigowa gida ta jefo min wannan tambayar, da fari na tsaya tunanin abunda zan ce mata sai kuma daga baya na yanke shawarar faɗa mata gaskiya. “Mayar masa da abunsa na yi, bamu da buƙatar taimakoshi” “Amman Nawwara ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, mutumen da ya tsinceki gefen titi ya taimaka miki ya kaiki asibiti garin Allah ya waye kuma ya aiko ganinki shine zaki mayar masa da kayansa? Wannan wace irin rayuwace Nawwara? Mi yake damunki? Wulaƙanta ɗan'adam? Kuma mutun kamar Mustapha yaron da babu wanda ya isa ya nuna masa ɗan yatsa amman har kike ƙoƙarin ci masa zarafi?” Yanayin fuskarta da kuma lamanta na fahimci ranta ya ɓace sosai akan abunda na yi, ni kuma na marairaice mata kamar zanyi kuka. “Inna kin san waye Mustapha ana yaba masa da neman matan banza, dan me zai kawo min abu na karɓa, bayan ban san manufarsa a kaina ba” Ta ƙaraso kusa da ni “Shiyasa na ke son ki lallaɓa da shi ku rabu lafiya, da baki watsa masa kayansa ba sai ki amsa ki masa godiya in yaso daga baya sai ki nemi ya rabu da ke” “Zan kiyaye nan gaba” Da wannan muka raba na nufi murhu na cigaba da hura wuta, ita kuma ta koma ɗaki tana cewa Sakina ta zo ta siyo mana ƙosai. Har na dama kumun tunani ɗaya ne a raina, na faɗawa Inna gaskiya game da Mustapha ko kuma na barwa cikina, idan ma na faɗawa Inna amfanin me zai mata? Idan kuma na bari ban faɗa ba ni amfanin me haka zai min? Ina cikin wannan tunanin naji muryar Namiji yana sallama a ƙofar gidanmu, bayan naji tsayawar mota da kamar minti huɗu, dakan uku-uku gabana ya yi duk da ban san ko wanene ma. Ko da na bar gaban murhun Jamila har ta kai waje, sai gata ta dawo da sauri tana kirana. “Anty wai ki zo ana kira a waje” “Waye?” “Wanine” Mustapha na fara kawowa a raina, amman da shi ne ai Jamila ta sanshi da shine ai ba zata ce wani ba. Miƙewa na yi tsaye na tare da bokitin da na dama kunun na nufi ɗakin Inna na aje mata sannan na ɗauki Hijabinta na saka na nufi ƙofar gida gabana sai faɗuwa yake musamman da na yi arba da mutumen dake sanye da rigar kamfanin da kuma hularsu, tun kamin na masa sallama shi ya fara min tare da faɗin sunana. “Khadija Musa Kafinta” “Sunana ne” “Zaki saka hannu a nan sai na baki saƙon da aka aiko miki” “Bana da buƙata ka mayarda saƙon, kuma ka faɗawa shugabanku ya dakatar duk wani saƙo da suke aiko min bana da buƙata” Sakin baki mutumen ya yi yana kallona, kamin ya barshi tsaye a gurin nayi shigewata, zuciyata cike da tunanin abunda ke cikin saƙon a lokacin na riƙa da na sanin ƙin karɓa da na yi domin sosai na so naga abunda aka rubuta, sai dai kuma ta wani babin bana da buƙatar duk wani abu daya dangancin Jibril idan har na saka masa fuska tabbas zai sake nuna wasa da ni kamar yadda ya yi a baya. Wani mugun murmushi na samu kaina da yi lokacin da na tuna hawayen da na gani a fuskar Jibril, ashe zai iya zubar da ƙwalla saboda ganina har ya riƙa hannuna ya shafa a fuskarsa, mace da ya ce kashe yafi ta daraja a gunsa, lallai akwai babban labari a cikin hawayensa, domin ba kasafai Jibril ya ke nadama akan abunda ya aikata ba. “Kee... Lafiya kike murmushi ke kaɗai kuma?” Tambayar da tayi min ta dawo dani daga duniyar tunanin da na tafi har na yi dariya na matsa kusa da ita na rumgumeta. “Ina sonki sosai Mamana” “Waye ya zo yanzun kuma?” “Daga kamfanin da nake aiki ne, suka aiko saƙo amman ban karɓa ba” “Saboda me?” “Nasan babu komai a ciki sai wulaƙanci” “Ai da kin karɓa kin duba wata ƙila zai miki amfani” “Ya riga ya tafi” “Allah ya kyauta” Sai duk muka amsa da Amin. Bayan mun gama karyawa, su Sakina suka shirya suka tafi makaranta tare da Noor, sai dai gabana nata faɗuwa saboda ina ganin kamar wani abu zai faru da ɗana. Sai da suka je makarantar suka dawo sannan hankalina ya kwanta. Can da yamma sai ga Jidda ta shigo gidanmu da manyan ledoji, daman ta saba a duk lokacin da nake rashin lafiya sai ta riƙo min wani abu take zuwa gidanmu dubani, sai dai abunda ya ban mamaki siyayar da ta yi min ta fi ƙarfin Jidda duk da nasan sun fimu rufin asiri. Bayan sun gama gaisawa da Inna ta ƙasaro inda nake zaune ta dire min ledojin tana zolayata kamar yadda ta saba. “Gawa ta ƙi rame, kin ƙi ki mutu mu ci gado” “Mutuwata ba yanzu ba yarinya sai ke da danjinku kaf kun ƙare” Sai duk muka saka dariya har Inna dake ninkar kayan da na wanke ɗazu na su Jamila. Mun sha fira sosai da Jidda daga bisani na

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});