Chapter 70
Chapter 70
ni ya zo. Bayan sun tafi Inna ta zaunar da ni tana ta fada min maganganu akan rayuwa da kuma hakuri, ganin irin kuka da na ke. “Na hakura Inna amman ni fa ba zan taba komawa ba” “Babu wanda zai cilas miki komawa, amman ko dan ɗan dake tsakaminku ya kamata ace kun yafi juna” Tashi na yi na fita na koma dakinmu na zauna na yi kuka sai da na koshi sannan na shirya na fito na yi ma Inna sallama. Gidansu Jidda na nufa da Mamanta muka fara gaisawa sannan na shiga dakinta sai ta juya min baya tana dannar wayar da ke hannunta. Ban damu ba na zauna gefen katifarta na soma mata magana. “Jiya na yi mafarkinki Jidda, na yi mafarkin Mustapha zai cutar da ke” Tayi banza da ni kamar bata ji ni ba, ganin hakan yasa na tashi zan fita sai ta kira sunana. “Nawwara” Hawaye na gani a idonta. “Yi hakuri” Dawowa na yi na zauna sai na dafata na fashe da kuka sosai, kwantar da ni tayi kafadarta sai da na yi kuka na gaji sannan na labarta mata abunda ya faru tsakani da Jibril da kuma iyayesa da suka zo gidanmu. “Ki kara hakuri Nawwara ba gashi kin fara ganin sakamako ba, ni dai abunda na ke so ki yafewa Mustapha” “Zan yafe masa” “Amman..... Zaki iya” Sai kuma ta yi shiru. “Tashi kije karki makara” Ta fada, ni kuma na tashi sai ta rakoni har kofar gida sannan na fice ita kuma ta koma. A hanya na hadu da Mustapha ina tunanin ita ta fada masa gani nan na fito, sai ya sha gabana da motarsa sannan ya bude ya fito, sai kuma ya kasa ce min komai sai kallona yake. “Na yafe maka Mustapha ka dauka kamar komai be faru ba, amman zan gargadeka karka sake shiga hanyata, dan Allah dan Annabi ka fita hanyata” Ina fadar hakan na kama gabana na cigaba da tafiyata na barshi nan tsaye yana ta kallona. Har na yi kamar na bi ta gurin gidansu Bilal duk da na san by this time yana gurin aiki, sai kuma na bi hanyar da na saba bi. Na isa gurin aikin da misalin sha biyu saura kwata, yau ma atamfar roba ce a jikina da gyale. Kai tsaye na wuce gurin aikina zuciyata cike da son ganin Bilal, sai dai ban san takamaiman inda yake aiki ba. Ina isa kofar ta bude min, office dina na fara gyarawa sannan na shiga na shi Office din baya cikin hakan na nufin be shigo ba kenan, sai na na gyara komai sannan na fito, ko da na dawo nawa Office din wato office din farko wayata na ringing alamar kira ko da na duba sai na ga Number Zinatu da fari na yi mamakin da sunanta ya yi appearing a wayata sai dai tuna Rabi data karbi wayata tace za a saka min numbers mutane kuma nima a basu tawa yasa danna picking na kara a kunne. “Nawwara dan Allah ki sauko hawa na biyu yanzu” “Me zanyi?” “Dan Allah dai ki sauko Bilal yake nemanki” “Okay” Cikin hanzari na fita na shiga lifter, a hawa na biyu na sauka komai na gurin glass ne ma'ana wani ma'aikacin yana iya hango dan uwansa, haka na rika duba sunayen da ke gurin har na kai ga wanda aka rubuta Bilal Usman na tura na shiga, sai na samu dakin cike da mutane duka tsaye wani katon cake na gaban Bilal da wuka a jiki, Ina shigowa sai hankalinsa ya dawo kaina kamar marar gaskiya, sam baya farinciki kamar ba shi suke yi ma wakar happy birthday ba, kasa jurewa na yi sai idanuwa suka cika da kwalla, shi kuma ya gagara karbar cake din da Zinatu take kokarin kai masa a baki. “Happy birthday my dear” Shi kuma hankalinsa gaba daya a tashe yake ni kawai yake kallo. __________________________________________ Masu son ganin Jibril da Mustapha da Bilal da Nawwara ku kwatantasu a idonku, ni dai iya abunda na sani Bilal ya fi su kyau 😜 #COMMENT #VOTE #SHARE #FOLLOW. kalmomi dubu hudu na yi🙄 dan haka har na jibi ne wannan 👻 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @KhadeejaCandy *Shafin yau na ku ne Maman Hannep Novels Group, Rai Biyu Fan's Group Khadeeja Candy Novels Group*❤🖤 4⃣1⃣ Tana daf da kai masa cake din a baki sai ya yi saurin rike hannunta. “No thanks” “Haba Bilal sai ka ce wani abu yau ne birthday ka fa” Sake kai masa a baki da karfi har tana shafa masa ragowar da yake hannunta a fuska tana dariya ita da mutane da suke cikin office din. Sannan ta juyo ta kalleni “Karo mana Nawwara let's have fun” “No ina da aiki a ciki, Happy birthday Bilal” Na fada idanuwa cike da kwalla, sannan na juya na fito hawaye na bin fuskata. Ban yi nisa a tafiyarba na ji muryarsa yana kirana ni kuma na kara sauri kamin ya karo inda nake har na shige lifted, ina sauka hawa na biyar na shige Office ina kuka, ko mintuna ban yi da zama ba sai gashi yazo gurin kofar, ina kallonsa ta computer na ki budewa sai kuka na ke har ga Allah na ji zafin wannan abun, da ya gaji da tsayuwa ya kirani, ban daga ba har ta yi ringing ta gaji ta katse, haka ya jera min kira har guda goma sha uku ban dauka ba, be bar gurinba sai da Jibril ya karaso sannan ya yi hanzarin barin gurin, ni kuma na yi saurin tashi na share hawayena, sai dai hakan be hana shi fahimtar kuka na yi ba. “Good morning” Na fada ina a tsaye idanuwa a kasa muryata na bayyana kukana, a maimakon ya amsa min sai kawai ya karaso gaban table dina yana kallon fuskata. “Me kike yi ma kuka?” “Ba komai” Na fada idanuwa na kara cika da kwalla. “Fada min mana waya taba ki?” “Babu” “Aikin ne baki so?” Na kasa amsawa sai hawaye nake. “Mi Bilal ya zo yi nan? Miyasa kika ki bude masa?” “Ba komai” Ya daki table dina. “Dole ne ki fada min abunda yasa Gimbiyata zubar wannan hawayen mai daraja da tsada” Ya fada kamar ba shi ya yi maganar fuskarsa babu alamun wasa sai ma kara hade rai da ya yi “He's just come to apologise” “Apologise for what?” “Yau ya yi birthday, shine ya yi celebration tare da Zinatu” Kallona ya tsaya yi sosai kamar mai karantar abu a fuskata, sai kuma ya kyalkyale da dariya har sai da office din ya dauka gaba yana amsa amonsa. “Wow wow so that's means Zinatu ya ke so ba ke ba? Daman can ba saurayinki ba ne ko? Ko kuma...” Ganin yadda na ke hawaye yasa shi saurin rufe baki yana gintse dariyar da ke cinsa. “Okay calm down Naj-Babe i will talk to both of them” Yana fadar hakan ya nufi office dinsa sai cigaba ya ke da dariyar, kamar cikinsa zai fashe. Ni kuma na zauna a gurin hawaye na ta min zuba zuciyata kuma na mugun zafi. JIBRIL POV. Be shigo office din da dadin rai ba, amman wannan labarin na ya faranta masa rai. “Excellent” Ya furta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119