Chapter 89
Chapter 89
ce idan mun shiga gidan mutane mu daina hawa musu kan kujera, kuma wasu mutane fada suke idan aka hau musu kujera” Noor ya fada yana kallon Jibril da ya risino da kansa ya dauke ya dora saman kujerar ya rumgume ya lumshe ido, jikinsa ya yi sanyi sosai taya za a ce yana da irin wannan kudin amman ya kasa bawa dansa kulawa ta musamman da har wani abun na duniya zai burgeni ya kasa hawa? Shi ai iyayensa sun bashi kulawa taya ya kasa bawa dansa? ‘Lokaci be kure ba yanzu ma zaka iya he's still a boy’ Wata zuciyar ta amsa masa wanda hakan yasa shi jin sauki, har ya bude ido ya kalli hoton Nawwara da Noor ke nuna masa. “Laaaa ji Momy can” “Kai ma za a maka naka ina son ka sosai Noor” Noor ya dago ya kalleshi ganin ya yi masa abunda ba a saba masa ba, wato kiss shi dai yana ma Momysa amman ita bata masa jara ma Mama Habiba wani lokacin tana masa kiss idan ya yi abun kirki. “Me kake so ka ci?” “Bana jin yunwa a yanzu sai anjima, amman akan wacan abun zan ci” Ya fada yana nuna dinning area da aka kawata da farin dinning table da aka kawata da farin cabinets mai kyau da kuma freezer da ke hade da cabinets din har baka iya banbancewa. Jibril ya shafa kansa yana murmushi. “Idan ma a saman dakin nan kake son cin abinci Noor zan dora ka ka ci, ka saki jikinka nan gidanku ne” “Da gaske?” Ya gyada masa kai. “Har da Momy nan zata zo mu zauna? Kuma da Inna?” Ya sake gyada masa kai yana murmushi, sai Noor ya sauka saman kujerar yana kallon falon bakinsa har kunne hakuran nan a watse bakauye ya shigo gari. “Can ina ne?” Ya nuna Kitchen. “Jeka ka gani” Sai ya mika hannunaa ya riko hannun Daddynsa “Aa zo muje tare dai” “Idan na rigaka isa ba zan bari na shiga ciki ba idan kuma kai ka rigani isa ba zaka bari na shiga ciki ba, ka yarda?” Ya daga kai yana dariya, sai suka fara yar tseren gudu shi da Jibril da yana lakkame da hannunsa mai ciwo, da gangan Jibril ya bari Noor ya riga shi isa sai duk suka rika dariya Noor har da tsalle, abunda ya dauki hankalin babansa sosai yana kallonsa kamar ya hadeyeshi saboda Kauna. Suna fitowa daga kitchen din suka sake rigangan shiga bedroom haka suka bi suka zagaje gidan Jibril ya nuna masa ko ina har Swimming pool, a Garden sai da Jibril ya hau icen guava ya katso masa sannan aka sauna lafiya. “Acan za a saka maka lilo” Jibril ya fada yana nuna wani bangare na Garden din, sai Noor ya zaro ido. “Da gaske” “Eh har dakinka za a maka daban, a saka maka komai da komai har da tv ka da games” Dadi ne yasa Noor ya rumgumeshi yana dariya, sai kuma ya dago kai ya kalleshi “Sai gobe zamu je mu lallabata sai ta dawo nan mu zauna, mu a nan zamu kauna har gobe ko?” Ya daga masa kai, sai Jibril yasa hannunsa ya daukosa suka nufo falo, saman kujera ya zaunar da shi ya yi masa hotuna kala kala har da video sannan ya kunna masa tv ya saka masa kids channel sai yazo ya dauke ya rumgume suna kallon tv tare. NAWWARA POV. Tsayawa na yi kallonta saboda na tantancewa idanuwa ita din ce ko kuwa wata ce mai kama da ita, idan har ita dince to gaskiya ta canja sosai fuskarta ta yi kala biyu fari da kuma wani farin na daban, ga wata uwar rama da ta yi fuskarta ta matse sosai. “Na san zaki yi mamakin ganina Nawwara, kin yi kokari da baki manta fuskata ba duk tsawon wannan lokacin” “Taya zan manta fuskar da ta kwace min yan ce a gidan aurena? Fuskar da mijina ya fifita sama da tawa” “Ashe har yanzu a akwai soyayyar Jibril a cikin zuciyarki tun da har za ki iya kiransa da sunan mijinki” “Miya kawo ki gidanmu? Taya kika zo me kike nema a gareni?” “Wacce daga cikin ukun tambayar ki nan zan fara amsawa?” “Duka zaki amsa min kuma ki tashi ki bar mana gida” “Zan tafi Nawwara gidanku ya yi min yawa da zama, amman ina son ki bani lokacin ki ki saurari abunda zan fada miki ko kuma na ce zan rokeki” Kamar ba zan zauna ba, sai kuma na zauna saman gadon Inna ina kallonta da jiran abunda zai fito bakinta. “Na san za ki yi mamaki ganina a wannan lokacin kuma a cikin gidanku, abun da ya fi ko wanne mamaki ma taya aka yi yarinyar da ke Abuja ta zo har sokoto kuma ta gane gidanku ko” “Ba abun mamaki ba ne Jibril zai iya fada miki” Na fada mata kai tsaye, sai ta yi murmushin da ke nuna cewar maganar ta soketa. “Mai zai sa Jibril ya fada min inda kike bayan ya gargade da cewar na fita daga rayuwarsa? Rabon da na saka Jibril a ido shekara biyu da rabi kuma saboda ke Nawwara” “Ni kuma?” Na tambaya da mamaki sai ta gyada min kai. “Ke fa, sai bayan ya rabu da ke ya gane yaudarar kansa yake da cewar baya son ki, ni kaina a wacan lokacin na san yana sonki ko da kuwa baya son ki tau ya san kimarki domin baya taba bari wani ya fadi wata magana marar dadi gareki a gaban idanunki ko bayan idonkin ciki kuwa har da ni” “Ban tambayeki labarin abunda ya wuce ko abunda zai zo gaba ba, dalilin zuwanki kawai nake son ji” Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleni idanuwanta raurau ta ce. “Yafiyarki na zo nema Nawwara” “Ai ni baki min komai ba” “Na yi komai Nawwara, na tozarta aure na yi amfani da dama ta na ci mutunci auren wata taya Allah ya zai bar ni na gina tawa rayuwar auren a cikin kwanciyar hankali? Bayan ban so yar'uwata abunda na so wa kaina ba? Kaddarorin rayuwa sun yi ta faruwa da ni Nawwara wanda na ke sa ran saboda na ci mutuncin aurenki ne, a iya sanin da kika min ina budurwa har yau ina nan haka ban yi aure ba, a lokacin da muke soyayya da Jibril muna tsaka da maganar aure sai kawai babansa ya cilasta masa aurenki, a wacan lokacin Jibril sai yake ganin kamar idan ya rabu da ni be aureni ya ci amanata, da wannan damar na yi amfani na dauke masa hankali, ni da kaina na rika jan ra'ayinsa har muka fada kogin aikata alfasha wato zina, a tunani wayewa ce na yaudari kaina sosai da sakewa namiji jiki tun kamin ya aureni, ba ni da tufafin sakawa sai na tsiraici gyale ma irin wanda zai bayyana siffar jikina na ke sakawa saboda na dauki hankalinsa, haka duniya ta yi ta yaudarata har muka tsufa a kogin alfasha ban ankaro ba, bayan Jibril ya rabu da ke sai na bijirowa da Jibril maganar aurenmu abun mamaki sai ya ki amincewa, kin san dalili? Saboda ya riga ya san ni a ya mace tun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119