Chapter 81
Chapter 81
da gaske ba ne? Miyasa ba zaku so abunda na ke so ba? Miyasa kuka gagara ganewa?” Magana yake kamar ba shiba har numfashinshi na hawa wani kan wani, kamin ta kara cewa wani abu ya tashi rai a bace ya bar mata falon. NAWWARA POV. Ba jidadin zuwan Mustapha ba domin ban fiye son yana shige min ba, bana son wata alaka tana shiga tsakanin ni da shi, dan ban yarda mutum ya cuceni kuma ya dawo ya ce zai rabe ni ba Jibrrma dan babu yadda zan yi ne. Bayan fitar Mustapha da mintuna talatin na kalli Jibril fuska a daure na ce. “Ina son na kwanta dare na yi fa? Kuma ka san Inna tana waje kai take jiran ka fita” “Ba zan je ko ina ba, a nan zan kwana tare da da na” Ban yi mamakin furucinsa saboda cocaine yake sha mahaukacin mutum komai zai iya ai, musamman idan ya samu guri in ban da rainin hankali daga kawai na bashi damar ganin Noor sai kuma ya soma yi min katsalandan a lamurrana. Tashi ya yi ya fita hakan yasa na bishi baya saboda na samu damar fada masa maganganun da ke bakina, ina fita na samshi bakin kofa a ashe ni yake jira. “Daga Bilal har wannan dan iskan yaron bana son su sake zuwa gurin da na” “Baka da damar da zaka shardanta min wanda zai so gurin da na da wanda ba zai zo ba, kai yanzu ko kunya baka ji ka kira Noor da danka? Har kana ikirarin kar wani ya zo dubashi?” “Yes da na ne, alakar da ke tsakaninku daban babu ruwana a ciki” “Ni na haifi yarona a hannuna ya girma baka da wannan hujjar Jibril, kuma ko zaka wulakanta kowa ban da Bilal saboda ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarta ni da dana, shi Noor ya sani a matsayin Uncle dinsa ba kai ba, da kuma ba naka ba ne nawa ne” “Ko tau zamu gani” Na watsa masa harara, ina kokarin juyawa na koma cikin dakin sai ya fisgoni da karfi ya dawo da ni “Ban yarda ki kwana da shi ba, Inna zata kwana da shi i don't trust you” Dariya na farayi saboda abun ya bani dariya sosai. “I'm laughing it's funny very funny” “Ba wasa nake miki ba Inna zata kwana da shi ba ke ba, idan ba haka ba, ni zan kwana da shi” “Ban ga dalilin kwana tare da dan da ka kira da shege ba? Kai baka ma jin kunyar yanzu ka kira shi da danka?” Hannu ya daga kamar zai dakeni sai kuma ya juya baya ya dafe kansa da hannu daya. “Na dake ni mana, ai ka saba cin zarafina ko? Ka saba yi min wulakanci a gaban kowa, na yi min cin mutumcin da ya fi ko wanne ai ba ka hada hoto da na wani ba? Ka fadawa iyayena cewar ni karuwa ce..” “Enough...!” Ya fada a tsawa ce har sai da hankalin wanda duk wajen dakin ya dawo kanmu, wadanda suke cikin daki kuma suka fito waje, sai dai hakan be sashi fasa fadan abunda zai fada ba. “Ya isa haka Nawwara ya isa haka, wace irin zuciya ce dake haka? Ke kan wace irin mace ce me ke damunki miya ke cikin kanka? Miyasa kika zabi nanata maganganun nan a ko yaushe ne? Kin san abunda yake raina? Kinsan bakinciki da yake raina? Ban isa na wuce wannan kaddarar ba shiyasa na aikata but abunda kike yi babu tausayi a ciki Nawwara, am lemme tell you abunda kike ba burgewa kike ba kokarin kashe rai kike, kokarin rusa wata rayuwar kike kuma babu abunda zai sa na canja daga manufata” Yana gama fadar hakan yaja hannun Noor ta da fito waje suka koma cikin dakin, Inna hango Inna take na rufa masa baya rai na a bace. Noor na ganina ya yi saurin sakin Jibril ya dawo guna cike da tsoro, dan Noor ya tsani ganin ana fada. “Da na ni ya sani ba kai ba, karka sake shiga rayuwarsa” “Dole na shiga rayuwaraa saboda ni ne asalin ubansa” “Yes ubansa ne kai na gaji da boyewa” Na juyar da Noor ina nuna masa Jibril. “Ka ga wacan? Ba Uncle din ka ba ne shine asalin ubanka Baba Faruk ba babanka ba ne rika ka kawai ya yi, wacan azzalumin ne mahaifinka, shine wanda ya ce kai ba dansa ba ne, da aka haifeka be yanka maka rago ba, kuma be san zafinka ba...” Ban karasa na naji an dago ni an sauke min kyakyawan mari har biyu a fuska, wanda ya haddasa min daukewar wutar cikin kaina tare da ganin wadansu kanana taurari.. ___________________________________ Ku yi hakuri da wannan guntun page din 🙏 Mutane da suke cewa kar Nawwara ta yafewa Jibril sai ta musguna masa kuma su ke cewa Nawwara ta cika tsauri da yawa wai zuciya kamar ta kafiran farko 😂 Ni dai nawa ido 👁👁 [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣6⃣ Zafin marin ya haddasa min ganin duhu a idanuwana, sai na kyabta idon sau biyar sannan na ga Inna dake tsaye tana hararata, Noor kuma ya fashe da kuka ya rike min kafafu da dayan hannunsa. Hawayene suka soma zuba a idanuwana ina dafe da kuncina, sai na juyo na kalli Jibril da shi ma idanuwansa ke cike da kwalla, juyawa ya yi ya bar dakin ba tare da ya ce komai ba, sai da yaja kofar dakin sannan Inna ta soma fadamin maganganu marar dadi. “Ina miki kallon mai hankali ashe baki da hankali, abunda kika aikata a yanzu ya fi abunda Jibril ya yi ma Noor shekarun da suka wuce, miye abun burgewa a cikin fadar irin wannan maganar a gaban idon dansa? Wane irin kallo kike son dan sa ya masa? Kina tunanin burgeshi zaki yi? Ki haddasawa danki tsanar ubansa da kanki? Idan ke baki son shi karki shiga tsakanin uba da da, Wallahi da Noor zai girma a cikin talaucin da ya fi wannan kuma daga baya ya hadu da mahaifinsa dole ne sai ya masa biyayya saboda haka Allah ya ce. Wace irin zuciya ce da ke Nawwara, ke baki ma Allah laifi ya yafe miki ne? Wa kika fi? Idan ma ba zaki yafe masa ba ai ba sai kin shiga tsakaninsa da dansa, Wannan ba halinki ba ne Nawwara kuma ba halina ba ne ba kuma halin Babanki ba ne, ban san inda kika dauko wannan bakar zuciyar ba” Tun da ta soma maganar na lumshe ido hawaye na cigaba da min zuba, sai na ji ta fisge Noor daga rikon da ya yi min ina bude ido ta nuna min hanyar fita. “Fita ki bar dakin nan” Na bude baki zan yi magana ta daga min hannu. “Bana son jin wata magana daga bakinki ki fice kawai kije gida” Juyawa na yi kafafuna da nauyi zuciyata kuma da rauni na fito daga dakin ina share hawayena. Kowa kallona yake ni kuma na ki na kalli kowa na fito ina wata tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na nufi bakin gate din asibitin. Miyasa kowa ya kasa fahimtata? Miyasa ni kadai na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119