Chapter 57
Chapter 57
sai tambayarta da kuma abunda ta faɗa min ya dawo min a rai, ya aka yi ta san Jibril ya wulaƙanta har haka? Ko dai shi ya faɗa mata ne? Idan har shi ya faɗa mata wannan yana nufin shi ya turota kenan? Amman taya zai turo ta bani shawara akn karna koma aikin kuma. “Lafiya kuwa Zinatu ta zo?” Ya ɗago daga tunanin da na ke na kalli Inna ina ƙirƙiro murmushi tare da nufar inda take zaune na zauna. “Ba komai ta zo ne akan aikin nan wai yau ban je ba na faɗa mata se gobe shine wai bata son ina wasa da aikin ne” “Nawwara be kamata ace kina ɓoye min wani abu ba, ni fa mahaifiyarki ce, bana son noƙe-noƙen nan da kike haka kuka yi ke da Habiba har ta Allah ta kasance” Rumgumata na yi ina murmushi. “Wallahi Inna maganar aikice ta zo ta bani shawara, babu wani abu kin ji na rantse miki” Hakan yasa hankalinta ya kwanta, ni kuma na zari Hijabi na nufi gidansu Jidda. A tsakar gidansu na sameta kwance saman tabarma ta yi rufa da zane da alama bata jindaɗi duk ta rame kamar ba ita ba. Da mahaifiyarta muka fara gaisawa sannan na nufi inda take hankali a tashe, hannu na kai na taɓa jikinta sai na jishi da ɗan ɗumi. “Tun yaushe ne baki da lafiya?” “Shekaranjiya, maleria ce ke damuna” “Allah ya baki lafiya, Wallahi ban sani ba sannu” Kai ta gyaɗa min sai ta miƙo hannunta ta kama nawa hannu ta jimƙe a sosai ta lumshe ido sai hawaye, a take hankalina ya tashi ji nayi kamar itama tafiya zata yi ta barni ban san lokacin da na fara nawa kukan ba, sai Maman Nura tasa mana dariya wai daman mu ƴan raki ne idan muna ciwo. Ban bar gidan ba sai da na yi sallah magariba a nan, ko da na dawo gida kaina na ta ciwo saboda kuka da na yi a gidansu Jidda. Da kaina na labartawa Inna rashin lafiyar Jidda, ita ma kanta bata jidaɗi ɓa domin ta san yadda na ke da Jidda kuma ta san irin halin da Jidda take shiga idan bani da lafiya. “Zata ji sauƙi ai kin san maleria yanzu yadda take ma mutane balle Jidda da rakin tsiya, Allah ya sauwaƙe sai gobe zanje na dubata” “Amin amman gaaskiya tana jin jiki domin ta rame sosai jikinta kuma da zafi kamar ba a mata allura ba” “Allah ya bata lafiya, ai malaria yanzu sai an sha allura sosai ake tashi” Na tashi cikin rashin kuzari na nufi ɗakinmu. Washe gari da wuri na tashi kamar kullum bayan su Sakina sun tafi makaranta ni kuma na shirya cikin wata doguwar rigar yadi na yi ma Inna sallama tare da faɗa mata zanje gurin aikin sannan na saka Hijabi na fice. Gidansu Jidda na nufa dan duba lafiyar jikinta, una tafe ina ta mamakin tun jiya ba mi yi waya da Bilal ba be kirani ba ni kuma ina tsoron kiransa saboda ban saba ba kuma ban san hali da yake ciki ba, sai dai gaskiya a kwana biyu nan da ya saba min da kiran yasa ni jin babu daɗi. Na yi mamakin ganinta ƙofar gidan tare da Mustapha suna magana duk da ban san mai suke magana akaiba na samu kaina da tsoro sosai saboda sanin wanene Mustapha. Daga ita har shi ido suka ƙura min ganin irin kallon tuhumar da na ke musu, ba ma kamar shi da natsu guri ɗaya kamar na rikice da ganina. “Kin san waye Mustapha a unguwar nan Jidda karki yarda ya yaudareki” Na faɗa ina kallon Jidda da idonta ke cike da ƙwalla, shi kuma sai ya yi saurin girgiza kai yana faɗin “Wallahi ba abunda kike tunani ba ne Nawwara” Ni kuma na watsa masa wani shegen kallo. “Mi na ke tunani miye bana tunani? Kasan na san waye kai ka gwadani baka samu ba shine zaka dawo gurin ƙawata? Ko kuma bayan ka gama da ita ne ka dawo kaina?” “Babu komai a tsakanina da shu Nawwara nan ma ya zo ne saboda ke...” Cewar Jidda hawaye na mata zuba. “Saboda ni ko? Ki cigaba da biye masa har ya kaiki ya baro, waya sani ma ko ya lalata miki rayuwa kema” Ina faɗar haka sai na juyo na kamo hanyar dowowa, zuciyata cike da zargi kala-kala. Sai da na yi nisa sosai na kai bakin titi ina ƙoƙarin tare Napep sai ga Mustapha ya sha gabana da Mota ya fito da sauri ya fuskance ni. “Wallahi ba abunda zargi ba ne, na canja na Nawwara Wallahi na miki alƙwari ba zan sake yin wani abu marar kyau ba” “Ka dawwama a cikin abunda kake aikatawa ko kuma ka tuba babu ruwan Nawwara a ciki wannan farincikin iyayenka ne da kuma masoyanka, Kuma dan Allah ka fita daga hanyata mahaifiyarka ma ta yi mana cin mutunci saboda kai tace muna zugaka kana ci mata mutunci akan gida, dan Allah ka ƙyale karka sake jamin wani bala'in gida dai zamu tashi mu bar maka abunda very soon In Shaa Allah” “Ba ni na siye gidan ba Nawwara, wani ne ya siya sunansa Jibril ya ce shi mijinki ne” Mamaki ne ya cikani. “Ina ka ganshi?” “Malam Haruna ne ya faɗa min na je na sameshi yace shi mijinki ne” “Daga kai har shi baku da hankali, Kuma na faɗa maka ka fita hanyata” ina kaucewa ya sake shan gabana. “Nawwara mi zan yi ki yafe min mi zan yi ki yarda da ni? Faɗa min ko minene zan yi Nawwara ki yafe min?” “Zaka iya dawo min da Habiba?” “Wanda ya mutu baya dawowa kuma...” Sai na tari Numfashinsa. “Tau ba zan taɓa yafe maka ba” Ina faɗar hakan na kauce na cigaba da tafiyata na bar shi nan tsaye yana kallona fuskarsa kamar wanda zai fasa kuka. Na yi sa'ar samun Napep da wuri, ko da na isa gurin aikin takwas da ƴan mintuna, tun a bakin gate na haɗu da Amina abokiyar aikina, a tare muka ƙarasa ciki muka rubuta suna tare har tana cemin yau kan munyi latti ita tama daina ganina kwana biyu ina wasa da aikina, nikan dariya kawai na yi na ɗauke kai na nufi gurin aje Hijabina sannan na muka shiga ciki tare. “Khadija Musa Kafinta” Daf da za mu shiga lifted na ji an kirani sai muka waigo tare, wata ƙabila ce ta kira sunan nawa tana sanye da suit. “Please Follow me” Sai da muka haɗa ido da Amina sannan na bita ita kuma ta shiga Lifted, wata lifted muka nufa muka shiga tare sannan ta danna 5 lifted ta rufe muka fara tafiya. Ni dai ban kalli inda take ba itama bata ce da ni Uffan har muka isa sannan ta fita nima na fita muka doshi wani gurin daban. Ina hango inda na bi shekaranjiya na shiga office ɗin Jibril na yi tunanin kalwaɗowa zata yi mu shiga office ɗin sai naga mun iso wani ƙaton ɗaki mai cike da computers da kuma files. Muna shigowa sai matar ta juya ta fita wannan abokin nasa ya miƙe tsaye yana ɗaukar documents ɗin dake gabansa ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119