Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 110

Chapter 110

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da baki muke son jin amsarki ba da shiru domin ke bazawara ce ba budurwa ba, cewar kin amince shi zai tabbatar mana da cewar kin amince haka Annabi ya ce” Dago kaina na yi na kallesu dukansu ni suke kallo amsata kawai suke son jin... [11/18, 10:07 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣8⃣ Kaina ya yi nauyi sosai ta ya zan iya watsa kasa a gaban manyan mutane kamar wadannan? Mi zai biyo baya idan na ce ban amince ba? Wane irin fahinta Baba Sulaiman da Baba Dahiru zasu min? “Ban zata zai aiko da wuri haka ba, shiyasa ban fada muku ba” Na fada yayinda nake maida kaina kasa. “Yanzu dai ba wannan ba, kin amince ko baki amince ba?” Baba Dahiru ya tambaya. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na amsa. “Na amince” “Al-hamdulillah, Allah ya miki albarka Nawwara kin ceci rai” Abunda ya fito daga bakin Mahaifin Jibril kenan fuskarsa shinfide da farinciki. “Tashi ki koma gida” Cewar Baba Sulaiman, haka na taso kamar marar lakka a jiki na fito daga gidan na nufo gida, tun a hanya kuka ya fara kamani amman ban yarda na yi ba sai da na iso gida, ina shiga na fashe da kuka kamar an min mutuwa. “Lafiya miya same ki?” Inna ta tambaya tana rike da tsintsiya. Faduwa na yi zaune. “Inna wai iyayen Jibril ne suka zo neman aurena?” “Ban gane suka zo neman aurenki ba” “Mahaifinsa ya turo da wasu mutane ya ce ni nace su zo, wai su nema masa aurena, shine Baba Sulaiman da Baba Dahiru da Baba Audi suka kirani suka tsareni suna tambayar wai na amince ko aa” “To mi ya faru?” “Na ce na amince” “Shine kuma kika zo nan kina kuka” “Ni bana son shi Inna ba zan aureshi ba” Sai Inna ta nuna ni da tsintsiyar da ke hannunta. “Wallahi kin yi kadan karyar karya take Wallahi, wato ni gani ice mai dadin zama shine zaki zo nan kina min kukan ba zaki aureshi ba ko? Ni da kika raina ai miyasa baki fada musu tun can ba” “Baba Audi zai iya yanka ni” Na fada cikin kuka. “Oo to sai ni da nake rarrashin ki zaki xauna kina min kuka kamar yadda karamar yarinya ko?” “Wallahi ko an daura auren nan ba zan tare ba” “Tashi kije gasu can ki fada musu tun basu tafi ba, ko kuma ni na yafa mayafina na je na fada musu kina nan kina kukan ba zaki yi auren ba” Jin haka yasa na yi saurin tashi na shige dakin Inna dan nasan duk Baban Audi ko Baba Dahiru suka ji wannan maganar na shiga uku yanxu bayan na ce na amince kuma na ce ban amince ba ai zasu ce ina musu wasa da hankali. Kuka na yi sosai dakin Inna rayuwar da zan yi gidan Jibril nake hangowa, taya zan rayu da mutumen da ya wulakanta ni? A yanzu ma zai iya kara wulakanta ni saboda yana ganin a bagas ya same ni kamar wacan lokacin, kuma zai yi ta tunanin ina son sa wanda hakan zai bashi damar sake wulakantani kuma na san har duniya ta nade Jibril ba zai taba sanin mutuncina ba. Sai da yamma Baba Sulaiman da Baba Dahiru suka zo gidan tare da kwalaye minti da cingan da sauran abubuwan da ake kawo wa na baiko, suka labartawa Inna abunda ya faru, ta nan nake jin sun yanka sadakina dubu talatin abokin Abbah ya biya dubu dari kasa, kuma sun saka kwana shida da suka rage na aurena da Bilal sun maye gurbinsu da Jibril. Baba Sulamain har dadi yake ji wai yafi son haka ta yadda Bilal kawai da familynsa zasu ji an daura min aure. A daren ranar kasa bachi na yi sai na kwana ina raya daren da sallah nafila da karatun qur'ane Allah na mikawa lamurrana har yanzu ban cire rai daga auren Bilal ba. JIBRIL POV. Tunda su Abbah suka kama hanyar gidansu Nawwara gabansa ke ta faduwa yana sauraren irin amsar da zasu dawo da ita, Abbah na kiranshi ya tsaya karanta addu'a sannan ya daga zuciyarsa cike da fargaba. “Kana ina?” “Ina gida Abbah” “Ka zo gida ka same ni yanzu” “Abbah bata amince ba ko?” “Ta amince har mun biya sadaki kuma kwanakin da suka rage na wacan da bata aura ba aka maida da naka” Rudewa ya yi yana tsaye ya zauna sai kuma ya sake tashi tsaye. “Abbah are you serious?” “Ah wasa na ke da kai? Ko wasa ake da lamarin aure?” “No no i mean thank you gani nan zuwa” Abbah ya kashe wayar yana murmushi. Sai Jibril ya fadi ya yi ma Allah sujudar godiyar, sannan ya mike tsaye yana wani irin dariya kamar mahaukaci har da jjjiga jiki, zuwa can kuma ya fara rawa takawa ya farayi a hankali a hankali kamin ya fara yi da karfi har da su kada kwankwaso, sai kuma ya yi tsalle ya fada saman kujera. “Oh my God i just can't believe this Al-hamdulillah Allah” A take ya fara hango irin rayuwar da zasu yi da Nawwara idan aka daura musu aure, ya dade yana ta ayyana irin jindadi da gatan da zai nuna mata sannan ya tuna cewar Abbah yana can yana jiranshi kuma yau zai bar garin. Cikin hanzari ya fita gida, zuciyarsa fari kal saboda farinciki, har ya yi kamar ya kira Nawwara sai ya tuna da riske yayi mata sai ya fasa dan yasan tana nan tana fushi da shi. Ko da ya isa ya samu su Abbah na cin abinci shi kan ko ruwa kasa sha ya yi saboda farinciki, rabon da ya yi farinciki irin wannan har ya manta, kallo daya zaka masa ka gane yana cikin farinciki. Wasu batutuwan Abbah ya tattauna da shi akan auren bayan ya fada masa yadda komai ya gudana. Sannan suka tsaya tsara yadda za ayi. “Zan ba Hajiya ta hada mata kayan sawa na tufafi da komai da komai da ake, kai kuma sai ka bata kudin da zata yi hidima da wuri saboda kar lokaci ya kure, na fadawa iyayemta bama son komai, saboda haka idan an daura aure sai ka fara gyaran gidan kamin nan da wata daya ka gama sai ta tare” “No Abbah a cikin week din nan ma za a iya komai a kudi ne matsalar kuma da an bada kudi za ayi komai a cikin lokaci, kuma ba dole sai furniture ba dole sai anyi order a abroad ba a nan ma Kano Kaduna ma za a iya samu na wajen, Abbah na fi son ana daura auren ta tare ranar gudun kar wani abu ya shiga” Abbah ya dan tsaya kallonsa ya so ya fahimce cewar cilastawa Nawwara yayi sai kuma ya tuna da irin son da yake mata ko da ita din bata son shi ba matsala ba ne. Su yi maganganu sosai akan auren da kuma yadda za a tsara komai, ciki har da zancen da Jibril ya bijiro da shi cewar baya son a yi masa taso sosai gurin daurin auren domin ba kowa yake son a sanarwa ba. Bayan sun gama Jibril ya raka Abbah da babban yayansu da

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});