Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zuwa gurin ƙofa to my surprise sai ga Jidda ta shigo rike da kaya niƙi-niƙi a hannunta. “Har kin farka?” Da ni take magana amman idonta yana kan Mustapha da kamar akwai wani abu a ƙasa. Ƙarasa ta yi ta aje kayan da ke hannunta ta zo ta dafani, sai na kaɓe mata hannu idanuwa cike da ƙwalla zuciyata kuma har wani fisga take kamar zata fito. “Me kuke yi a nan” “Suma kika yi a hanya, sai Mustapha ya ganki ana neman inda za a kaiki shine ya kwaso ki ya kawo asibiti” Kai tsaye ta bani amsar, Mustapha kan tuni ya yi mutuwar tsaye saboda kalaman da na masa. “Ya akayi kika sani?” Na tambaya yayinda da hawaye suka sauko daga idona suka wanke min fuska. Sai da ta kalli Mustapha sannan ta kalleni ta ce “Mustapha ne ya faɗa min” Dauƙe kai na yi na cigaba da tafiyata na ƙi kula kiran da take min har na fice daga ɗakin. ‘Taya Mustapha yasan alaƙar da ake tsakanina da Jidda? Miyasa be kira wani daga cikin gidanmu ba kira Jidda?’ Shine abunda na ke ta saƙawa a raina ina tafiya, Jidda na bina da kira. ‘Amman kuma ai bata san illar da Mustapha ya yi mana ba, bata san aibunsa a garemu ba’ Tuna wannan yasa na tsaya har na saka Hijabina na danne Hannuna ina jiran ta ƙaraso. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣2⃣ “Haba Nawwara abunda kike ba shi da kyau Wallahi na san kin tsani masu kuɗi amman wannan mutumen fa taimakonki ya yi ban san abunda bawan Allah nan ya yi miki ba duk kin bi kin tsaneshi, haka sam be dace ba, ni kaina na tuhumesa lokacin da ya zo har gida ya faɗa min na ce miyasa be faɗa ba gidanku ya ce yana gudun zargin ne kuma da na zo nan asibitin na tarar mutun biyu da suka kawo ki tare, Wallahi babu wani abu Nawwara dan Allah ki kwantar da hankalinki” Shine abunda Jidda ta faɗa lokacin data ƙaraso kusa da ni. Mustapha kuma na daga can nesa da mu ya sako min ido kamar zai cinye ni. Kallo ɗaya na yi masa na ɗauke kai ba tare da na ce da ita komai ba na cigaba da tafiyata, zuciyarta na mugun bugawa kamar zata faɗo. Tare muka fito da Habiba a har bakin gate ɗin Specialist hospital dake sokoto, motar Mustapha ce ta sha gabanmu be ce komai ba ya miƙa hannu daga inda yake zaune ya buɗe mazaunin baya. Jidda ce ta iya riƙa ganbun motar ni kan ko kallo bata isa ban na kauce mata na cigaba da tafiyata har na tsada mai adaidaita na shige ina faɗa masa inda zai kaini, yana ƙoƙarin tashi sai ga Jidda ta dakatar da shi ta shigo tana min masifa wai abunda na ke bana kyauwa, ni dai ban kulata ba saboda na san bata san zafi da irin ƙiyayyar da raina ta Mustapha ba, tun da ban taɓa faɗa mata cewar shine mutumen da ya yi sanadiyar muturwar ƴar'uwata ba. A gurin da aka saba saukeni na ce ya ajeni na saka hannu aljihu na ciro kuɗi a bashi sai a lokacin na tuna da hoton Habiba da na baro a wacan baƙin kamfanin da bana fatar ko a mafarki na sake zuwa, gaskiya na ji babu daɗi sosai domin shine kaɗai hoton Habiba da nake da shi a yanzu wanda take da girmanta, ta ɗaukeshi ne lokacin da zata yi canjin makaranta daga Hafsatu zuwa Nana girl's, abunka da takala ba hotone a gabanmu ba sai idan wani abun ya tashi na dole sannan muke zuwa yin hoto. “Ina wayata?” Na tambayi Jidda bayan mai adaidaita ɗin ya bamu canji, hannu tasa cikin jakarta ta ɗauko wayar ta miƙa min. “Gashi” Ina karɓa na sa kai gabana muka cigaba da tafiya tare. “Gaskiya halinki bashi da kyau Nawwara, idan har baki yabawa Mustapha ba to ba zaki zageshi ba” “Ce miki ya yi na zageshi?” “Ko baki zageshi ba kin faɗa masa magana marar daɗi domin alamu sun nuna haka, ban san abunda bawan Allah ya yi miki ba, ko dai akwai wani abun ne?” Na tsaya ina kallonta “Wai miyasa kika damu ne Jidda?” “Saboda ya taimakeki, da be kawo ki asibiti ba da Allah kaɗai yasan halin da zaki kasance akan hanya” “Da barina ya yi akan hanyar mota ta takani ko kuma mutane suka ɗaukeni suka jefar a bola, da ya fi min farinciki sama da ɗauko da ya yi ya kawo asibiti, dan Allah ki tattara duk wani abu da ya danganci maganar nan ki ajeta a gefe” Na tada kai na cigaba da tafiyata har na isa gida ban waiga na kalli Jidda dake gefena ba. Ita ce ta faɗawa Inna abunda ya faru da kuma irin abunda na yi ma Mustapha har Inna da kanta ta dinga ganin rashin kyautawa da kuma faɗar abunda na yi ba halina ba ne. Ni dai ban iya cewa Inna komai ba tun da nasan ita ma ban faɗa mata cewar shine mutumen da ya yi ma Habiba aika-aika ba. Tufafin jikina na cire na saka a murhu na ƙone tare da Hijab ɗin duka na haɗa na ƙone saboda mutun biyu Mustapha da kuma Jibril tsakanin su ba zan iya banbance wanda zuciyata ta fi tsana ba. Ina gaban Murhu Inna ta fito daga ɗaki jin ƙauri ta saka salati. “Lafiya kike ƙone kayan aikin kuma Nawwara mi yake damunki?” “Inna sun koreni dan haka bana da buƙatar wannan kayan” “Garin ya wani abun kika yi?” “Ban yi komai ba, saboda kawai na daɗe ban je ba” “Ba kince Bilal ya faɗa musu baki da lafiya ba?” “Wai basu yarda ba shugaban Kamfanin ne bashi da mutunci” “Allah ya kyauta ya baki wani” Ta faɗa cikin muryar da ke nuna bata jidaɗin haka ba. Ƙarasowa ta yi kusa da ni ta riƙani ta tayar tsaye. “Tashi gaban hayaƙi, bari na saka miki ruwa ki yi wanka” “A'a zan iya Inna” “Babu ƙarfi jikinki Nawwara baki ga yanxu kika dawo daga asibiti ba” Da kanta ta haɗa min ruwan na shiga banɗaki na yi wanka, bayan na fito na ɗauki buta na yi alwala na shiga ɗakinmu sai na samu Inna zaune tana yanka min albasa a wake da shinkafa, saboda ta san ina son na saka albasa da tumatur idan zan ci wake. “Gashi nan idan kin gama sallah sai ki ci, bari na kawo miki ruwa” Ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar fita ni kuma sai na yi saurin dakatar da ita. “Haba Inna kina ta min abu sai kace ƙaramar yarinya ni ya kamata ace ina hidima dake ba wai ke ki yi da ni ba” Tsayawa tayi jikin ƙofa tana murmushi tare da wasa da wuƙa da kuma ragowar albasar dake hannunta ta ce. “Nawwara ji nake kamar da nayi wani sakaci kaɗan rasaki zanyi, ɗazun da baki dawo a lokacin da kika saba dawowa ba hankalina ya tashi sosai, ba san yadda zanyi ba idan har na rasaki bayan na rasa Habiba, kuma kina a matsayin RAI BIYU a yanzu ni da kuma ɗanki, shi ma ya damu da be ganki ba

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});