Chapter 6
Chapter 6
ta buɗe yayinda ni nake zaune ina karatun ƙur'ane. Ina jin lokacin da ta zauna kusa da ni sai dai ban kalleta ba har sai da na kai ƙarshen ayar da na ke karantawa, sannan na rufe ƙur'anen ina ambatar sunanta “Jidda” “Na'am Nawwara, jiya cikin dare na ke jin abunda ya faru kuma kin san Abba baya bari mu fita da dare, da gaske ne?” Na ɗaga mata kai hawaye na bin fuskata. “Baba ba zai yi sata ba, sai dai idan wani sheri ne aka masa” Cikin kuka na zayyana mata abunda Inna ta faɗa mana. A take ta fashe da kuka. “Nawwara ki yi haƙuri jaka ƙaddara take zuwa wani lokacin, yanzu bari na je na shirya sai muje mu ganshi” “Babu ko naira hannuna Jidda” “Ina da ɗari uku zasu ishemu” “Tau Jidda na gode” Miƙewa ta yi tsaye ta fice, ni kuma na tashi na nufi ɗakin Inna, gaisheta na fara yi sannan na faɗa mata yadda muka yi da Jidda. “Tau bari na jira har ku dawo sannan muje” Tashi na yi na koma ɗakinmu na cire tufafin jikina na ɗaura zane na ɗibi ruwa a robar da muke wanka na shiga banɗaki na yi wanka da ruwan sanyi. Tufafin jiya na ɗauka na saka ban damu da shafa mai ba, domin ba kwaliyarce a gabana ba, sai takwas har da ƴan mintuna sannan Jidda ta dawo, baƙar abaya ce jikinta sai jan mayafi, hannunta ɗauke da kular abincin. “Nawwara zo muje” Abunda ta faɗa kenan tana shigowa. Inna ce ta rigani fitowa tana gaisawa da Jidda. Sannan na fito sanye da hijabi. “Jidda sai yanzu?” “Yi haƙuri dan Allah taliya na tsaya dafa masa” Ta faɗa cike da damuwa. Jidda ƙawar arzikice dukan abunda ya dame ni kamar ya sameta ne, tana damuwa sosai da duk abunda ya shafi rayuwarta, shiyasa bana da ƙawa a duniyar nan da ta wuce Jidda. Tare muka fita tana min bita kan haƙuri da yarda da ƙaddara, ni ko bana iya cewa komai sai hawaye da ke min zuba, ganin haka yasa ta daina maganar domin tana ƙara min ƙarsashin abun ne kawai. Tun da muka shiga Napep har muka fita ni da ita babu wanda ya ce Uffan, gabana ya faɗi sosai lokacin da muka doshi station ɗin wata ƙila saboda ban saba ba ne ko kuma ina fargabar ganin halin da Baba yake ciki ne. Jidda ta lura da hakan shiyasa ta wuce gaba ta bar ni a baya saboda kawai ta ƙarfafamin guiwa. Ƴan sanda da yawa muka tarar a gurin, ta kuma ɗai-ɗaikun jama'a waɗanda nake sa ran suma sun zo kan nasu matsalar ne, muna shirin tambayar sai na hango Baba Sulaiman wato ƙanen mahaifina da kuma yayyunsa. Cikin rashin kuzari da raunin zuciya na ƙarasa kusa da su idona na zubar da ƙwalla. Baba na zaune saman tebur fuskarsa a buge jini har ya dasƙare masa saman kai da alama tun jiya suka dake shi ko kuma da dare. Ƙasa na zauna kusa da shi na riƙe masa ƙafafu kasancewar shi yana zaune saman banci ne tare da ƴan'uwansa. Kasa kallona yayi wannan baya rasa nasaba da kukan da na ke wata ƙila baya son kuka a gaban jama'a ne. Kwanon ɗumame na gefen da na zauna nasan su Baba Sulaiman ne suka zo da shi. Tsawar da Baba Ayuba ya katsa min ne yasa ni tsagaita kukan da nake har na dawo hayyacina. “Ai yanzu sun yarda za su bada belinsa amman wai sai an bada dubu ashiri” Cewar Baba Salisu yayan Baba. Ni ko na dafe kai ina sauke ajiyar zuciya, ko yanzu tsugune bata ƙare ba, ina zamu samu wannan dubu ashirin ɗin. ‘Oh Allah mun gode maka’ Na faɗa a raina ina ta ƙoƙarin tare kukana. A nan Baba Sulaiman yake faɗa mana yadda matar take son a je kotu, wai ashe dpo ɗin station ɗin ne ƙanen wacce aka yi ma satar. Bamu ƙara minti goma a gurin ba, wani ɗan sanda ya zo yana faɗa mana lokaci yayi. Duk miƙewa muka yi tsaye a nan na samu kallon bayan mahaifina kasancewar ba shi da riga ne, babu komai sai kwancin sanduna, yanayin yadda baya son motsa jikinsa kaɗai ya isa ya karantar da kai jikin na masa zafi da ciwo ne. Ban san lokacin da kuka ya zo min ba, na rumgume bayansa ina mai jin kamar na yi tsuntsuwa ni da shi mu ɓace daga gurin gaba ɗaya. “Mahaifinku be yi sata ba Nawwara, kuma be taɓa yi, ki gamsar da ƴan'uwanki da wannan” Abunda Baba ya faɗa min kenan, ni kuma na ƙara ƙanƙanme shi. Hankalin duk wanda ke gurin sai da ya dawo kaina saboda kukan da nake, babu tausayi haka ɗan sanda nan ya tisa ƙetar Baba gaba suka wuce da shi ciki. Ni kuma Jidda ta rumgume muka riƙa kuka tare. “Haba Nawwara akan ki farau? Miyr haka wuce kuje gida, mu zamu koma can zamu san yadda za mu” Cewar Baba Sulaiman. Ƙarfin hali na yi na riƙa hannun Jidda muka fito tare, a nan Baba ya Ayuba yake faɗa min wai a tura Sakina ko Jamila ta karɓo mana ɗumame. Har muka iso gida kuka na ke, Jidda ce ta iya tsayawa ta zayyana ma Inna abunda ya faru. Ba laifi na ga farincikin Inna wata ƙiƙa saboda sun yarda zasu bada belinsa ne. Bayan Jidda ta wuce Sakina ta je karɓo abincin, ni kuma na tashi na nufi ɗaki kaina na mugun ciwo, abincin da aka karɓo ma ban iya ci ba, kamar yadda Inna da Habiba suka kasa ci duk da kasancewar muna jin yunwa. Ni dai ina cikin ɗakin har aka kira sallah azahar, bayan na yi sallah na nufi ɗakin Inna, a nan take tambayata Habiba. “Bata ɗaki na ɗauka tana nan ma” “Bata nan ƙila ta je baban gida” Haka kawai gabana ya faɗi zuciya ta riƙa nasalta min kamar ba can ta je ba. Babu wani hirar kirki tsakani na da Inna saboda bana son labarta mata halin da na samu Baba duk da kasancewar idanuwana sun saka goge hoton abunda suka gani. Misalin huɗu da rabi Baba Sulaiman ya shigo gida yana faɗar an haɗa dubu shida da ɗari takwas abun da ƴan'uwa masara son zumunci, taya za a ce duk yawan familyn Babban gida ace dubu shida kawai aka haɗa. Takaici da baƙinciki ya hanini cewa komai haka na koma cikin ƙarƙashin iccen dalbejiya na zauna. Ɗari da hansi ya cire a cikin kuɗi ya miƙawa Sakina wai su saye wani abu su ci. Inna kuma ta saka Hijabinta suka fita tare wai zasu je station ɗin su kai musu ko zasu karɓa. Ni dai nasan wahala ce kawai zasu yi, ƴan sanda da basa da imani, kuma sun ce dubu ashiri ya za'ayi su karɓi dubu shida. Noor ne ya zo ya zauna kusa da ni yasa hannunsa yana share min hawayen da ban san sun zubo ba. “Momy ki daina kuka” Murmushin ƙarfin hali na yi na shafa kansa. Kan Habiba na fara hangowa ta leƙo sai ta koma ta laɓe, hakan yasa ni miƙewa tsaye ni nufi ƙofar, ƙaton hijabinta ne na islamiya a jikinta, sam babu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119