Chapter 14
Chapter 14
ba ko gidan ba su ji ba ne” “Minene?” “Cewa aka yi wai kin mari Mustapha” Habiba ta yi min wani kallo tana jiran ta ji abunda zai fito bakina. “Ba wai ba ne na mare shi ɗin ɗazu” Habiba ta riƙe baki “Ashe da gaske ne” “Na ɓoye ne saboda na ga kamar ran Inna ya ɓace” Jidda ta kama hannuna. “Ke ko miya kaiki? Miya haɗa ku?” Shiru na yi ina tunanin irin amsar da zan bawa Jidda, domin bata san shine mutumen da ya yaga rigar mutuncin Habiba ba, a lokacin da abun ya faru ban labarta mata ko wanene ba kawai dai na faɗa mata cewar Habiba ta siyar da mutuncinta ta kawo dubu ashirin. “Ba komai kawai wai dan Mai Napep ya tsaya a bakin hanya shine ya zo yana mana rashin mutunci, ni kuma na mare shi” “Aka ce mari har uku wai, ai ƙara da kuka mareshi basa ganin mutuncin kowa a unguwar nan” Na zaro ido “Ɗaya ne kaji mutane da canja magana kuma, wai yanzu zancen nan har ya kai miki” “Wallahi ina zaune gida aka kawo min shi, wai ƙawata ta mari Mustapha, ai ko ni kika mara sai zancen ya zagaye unguwa balle kuma Mustapha guda” Dariya na yi, domin a yanzu duk wani tsoro da ke raina na ɗazu ya gushe. Labarin kamfanin na ɗaukowa Jidda ina ta faɗa mata yadda abubuwan suka, ita kanta da bata je gurin ba sai da abubuwan suka burgeta saboda yadda na tsaya na tsara mata komai kamar anyi a gabanta. Har muka ci firarmu da Jidda muka suɗe Habiba bata saka bakiba, Jidda kuma bata bar gidanmu ba sai da ta yi sallah magariba sannan na rakata sannan na dawo. Shikafar ɗazun na ɗauko na ɗumana na zuba mana muka zauna gaba ɗayan mu muka ci, ban da Inna da daman nata daban ake zuba mata balle kuma yau da ta ce ba zata ci ba. Muna cikin cin abincin nokiyar da ke gefena ta yi ringing, abun ka da wanda ya daɗe ba shi da waya tun da na saka layin ba a taɓa kirana da shi ba. Number Waje ma'ana ba nunber nigeriya ba ce, cikin rawar jikina na ɗauka dan nasan mace ɗaya zata iya kira na da wannan layin wato Salima “Hello Ƙawata” Sai ta amsa min daga ɗayan ɓangaren. “Ƴar'uwata, kin jefar da ni kullum ina kiranki bata shiga” “Wallahi bana da waya ne a yanzu, wannan ma ara min aka yi na saka layina” “Allah sarki ya gida? Ina Baba da Inna?” “Sai dai Inna tana nan lafiya ƙalau, Baba kan Allah ya yi ikonshi” “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yaushe? Miya same shi” “Rashin lafiya kwana biyu” Na yi ƙarya saboda ba kowa zaka iya faɗawa dalilin mutuwar Baba ya gasgata cewar Baba be yi satar ba, duba da yadda muke fama da rashi. Bayan ta yi min gaisuwa ta yi ma Inna sannan ta yi ma Habiba, Sakina da Jamila sannan suka maido min da wayar. “Kin rasa RAI BIYU masu muhimmanci Nawwara mutuwa mai ɗaci , kin rasa Abban Noor yanzu kuma Babanki Allah ya baki ikon ɗaukar wannan lamarin” “Amin Salima na gode” “Inshallah idan na dawo Nigeria zan zo har nan na yi miki gaisuwa” “To Allah ya yarda” Daga haka muka yi sallama, na amsa mata da to ne kawai ba dan na gamsu zata zo ɗin ba, duk tsawon zaman da muka yi da ita bata taɓa tako ƙafarta sokoto ba ai ba zata taɓa zuwa ba. Da gudu Noor ya zo gurin yana ƙoƙarin karɓar wayar. “Momy waya baki waya? Momy kira min Gwaggota Murja kin ji” Haka yake idonsa idon ganin waya, baya da magana sai ta a kira masa Murja wato Ƙanwar mijina wacce ya shaƙu da ita sosai. “An ya ma sun ji maganar rasuwar baban ku kuwa?” Maganar Inna tasa na ɗago kai na kalleta. “Ina zasu ji tun da ba a nan suke ba kuma babu waya a lokacin” “Ya kamata dai kan ki faɗa mata” “Bari na mata please Call me dan ba ni da kati gaskiya” A take na aikama mata please Call, ko minti biyu ba a ƙara ba sai gata ta kirani, mun gaisa sosai sannan na bata Inna, ita ta labarta mata cewar Baban mu ya rasu, ta shiga ɗimuwa da kiɗima sosai, har da kukanta kamar Babanta ne ya rasu. Bayan ta yi min gaisuwa ta faɗa min zata shaedawa sauran ƴan'uwan margayi Sadiq zasu zo har sokoto su yi min gaisuwa, duk ƙoƙarin dakatar da ita da na yi akan zuwan sai ta nuna min sam ba zai yiyu sai ta zo, ai daga sokoto zuwa Kebbi ba wani nisa ba ne. Sun daɗe suna waya da Noor sannan bashi yaranta suka yi magana sai ta kashe. Takwas da rabi wayar Bilal ta shigo, ina ɗauka ya shaida min yana waje. Sai da na faɗawa Inna sannan na tashi na saka Hijab ɗina na fita. Jikingine da ƙofar gida na same shi, ina masa sallama ya amsa fuskarsa da murmushi har wani ƙyali take. “Nawancy” “Bilal” Sai yasa dariya. “Ina jin daɗin ki kira sunana yana mugun daɗi a bakinki” Na yi murmushi ina rausayar da kai. Bayan mun gaisa ya bijiro min da fira cikin har da zancen marin da na yi Mustapha, sai na nuna masa ya yi min ba dai-dai ba ne shiyasa. Sai tara da rabi muka yi sallama. WASHE GARI.... Yau kan ba laifi dukanmu mun tashi cikin walwala, Sakina da Jamila tuni suka wuce makaranta, Habiba ma shirin makarantar ta ke, ni kuma ina gyaran gida, Inna kuma na ɗaki tana bachin safe. “Nawwara canjin kuɗin Koko yana nan ƙarƙashin fillo, Inna ta ce a siye ruwa” Cewar Habiba tana tsaye riƙe da littafan makarantarta. “Yau Fanfan ba zai zo ba ne hala?” “Yau kwana biyu be zo ba, ruwan da muke amfani da su sun ƙare, ƙara a siya da wuri idan ma ya zo kin ga kaɗan kawai za mu ɗebo” “Allah ya bada sa'ah” “Amin na tafi” Fitarta da kamar minti biyar, wata matashiyar yarinya ta shigo sanye da dogowar rigar atamfa da wani minafukin gyale a kafaɗa, sallama ta fara yi na amsa mata. “Assalamu alaikum” “Wa'alaikissalam” “Sannu ina kwana?” “Lafiya ƙalau” “Dan Allah nan ne gidan Musa Kafinta?” “Nan ne, lafiya?” “Lafiya ƙalau, Sunana Shafa Ibrahim ni ƴar jarida ce ina aiki da jaridar Arewa a yau, tare da abokin aikina na ke ina son mu tattauna da iyalansa ne akan abunda ya faru” Ta ƙarasa tana miƙa min katin shedarta. CANDY ✍️ *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy RIJF Mama A'i, ke da kika tafi ba ki yi sauri ba, mu da mika rage ba mu yi nawa ba. Allah kasa mutuwa ta zama hutu gareki Allah ya miki rahama ya gafarta miki kurakuranki. I will never forget you. Allah kayi mana kyakkyawan ƙarshe. 1⃣2⃣ Na kai hannu na karɓi cati na duba, sunanta ne da kuma hotonta a jikin catin hakan ya tabbatar min da cewar lallai ƴar jaridar ƙwarai ce. Na mayar mata da katinta. “Ba mu san komai a kai ba, waya faɗa miki nan gurin kuma?” “Jama'a ne suka kwatanta min, kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119