Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 45

Chapter 45

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya turo mu gida ni da Salima, bayan ya cika mana bayan mota da abinci, a lokacin an haifi Sakina har ta soma wayo. Watan mu ɗaya muka garin Abuja saboda sabo sai zaman sokoto ya yi ma Salima wuya, ni kan ban so haka ba, sai dai babu yadda zan yi tun da mun zo tare dole mu koma tare, bayan mun koma sa sati ɗaya na sake dowa, Alhaji Dahiru ne yasa ka Ya Jamal ya rakoni har gida, sai dai wannan karon tafiyar Jirgi muka yi saboda Ya Jamal ya ce ba zai iya bin mota ba zuwa sokoto. Kwanansa ɗaya ya koma, ni kuma na zauna a nan har na tsawon wata uku a lokacin Mahaifina yana sana'ar siyar da itace a ƙofar gida, wata rana mu cinye ribar wata rana kuma Allah ya buɗo mana, haka muke ta faɗi tashin rayuwa ga masu neman aurena sai fitowa suke. Kwatsan Alhaji Dahiru ya kira ya ce a sanar min ya samo mana gurbin karatun lafiya a ƙasar burtaniya wato London, cikin sati ɗaya na shirya na koma Abuja, duk wani shirye-shirye ina can aka yi shi, bayan kamar wata ɗaya da ƴan ƙwanaki aka kammala komai, sai da na koma gida na yi bankwana da su Inna a lokacin ne Yakunbo ta so tanani zuwa saboda a ganinta kamar za a siyar da ni ne ko wani abu makamancin haka. Kamar na mafarki na fara karatu a City, University of London, a ƙasar da ban taɓa mafarkin zuwa ba, ƙasar da nake ji a labarai da kuma jaridu, burtaniya ƙasar turawa ce wacce bata da matsatsi akan addinin kowa a wacan lokacin, ba ko yaushe nake irin shigarsu ba wato shigar ƙananan kaya, nafi saka doguwar rigar atamfa ko abaya sai na samu ƙaramin ɗankwali ko hula na yi rolling kaina da shi. Ɗakin mu ɗaya da Salima da kuma wata tsohuwar ɗaliba makarantar wato Farida, wacce ƴar asalin hijar bauchi ce, cikin ƙanƙanen lokaci muka saba da Farida duk da kasancewar ba gurin karatun mu ɗaya ba. Ranar da muka fara zuwa lab wani babban likita muka tarar ɗan Nijeria dan asalin garin Kaduna, wato Doctor Jibril Bashir Makama, sai da ya fara gabatar mana da kansa sannan na soma bamu darasi tare da nuna mana wasu abubuwan a zahiri. Tun da idona suka sauka akansa sai ya tafi da imani da duk wani tunani da natsuwata, Jibril na da kyau da ba zaka iya tantanshi aa cikin ƴaƴan turawa ko larabawa, fatarsa fara ce fes ga shi da tsaye hancinsa ya sauko a ƙasan hancin an yanka masa madaidaicin baki, fuskarsa na ɗan faɗi, yana da manyan ido sai dai ba fararene ba, suna da surkin ja ƙaɗan, a gefen wuyansa tattoo ɗin taurara ne aka jera masa har cikin bayansa. Hankalina baya kan abunda yake ƙoyar da mu yana kansa, duk wani ƙyabtawar idonsa ƙirgawa nake, ina haɗɗace yadda bakinsa yake motsi da turansa da yake watsowa kamar baturen burtaniya, duk bayan daƙiƙu sai na lumshe ido saboda ƙamshin turarensa da ya cika lab ɗin. Murmushi nake masa ba tare da na san ina yi ba, har sai da ya katsa min tsawa. “You deaf...” A firgice na dawo hayyacina cike da kunya, ƙasa-ƙasa na ke kallon wata abokiyar karatuna Katherine Williams wace ke sonim dariya ita da wasu da dake kusa da ni. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣9⃣ Tun daga lokacin bana da tunani sai na shi, mafarkina ma nasa ne, duk wani abu da zai kusantar da ni gareshi na kanyi ƙoƙarin aikatashi, duk hanyar da zan ganshi ita na ke bi, duk da na lura da babu ruwansa da sha'anin kula wasu matan na daban hakan yasa na fara tunanin ko yana da mata ne. Salima kanta ta lura da yadda nake ta rawar jiki da son ayi zancesa, idan kuma wata macen ta kalleshi sai naji kamar naje na shaƙeta, a gurin Salima na ke samun labarinsa, kasancewar ta sanshi farin sani wai ɗan abokin Daddy ne, na yi mamakin da ban san shi ba duk tsawon zaman da na yi a gidan, duk da kasancewar na san Mahaifinsa amman ban taɓa kawowa zuciyata cewar shine ɗansa ba, sai dai duk wani mummunan hali nashi na wulaƙanci da rashin son mutane ta hanyar Farida na ke jinsa saboda ta rigamu zuwa makarantar duk wani abu da ya danganceshi ta san shi sosai. Salima ce take labarta min cewar Jibril shine ɗa na uku a gurin Mahaifinsa, kuma ɗa na farko a gurin mahaifiyarsa kasancewarta Amarya, yana da Step mother wacce ita ce ke da ƴaƴa da yawa kuma ita ta riƙashi a hannunta ya tashi, a gurin haihuwarsa Allah ya karɓi ran mahaifiyarsa wannan yasa mahaifinsa yake sonsa kuma yake tausayinsa domin ko da Jibril ya buɗe ido be san mahaifiyarsa ba sai step mother. Wata ranar da muka yi practicing akan thigh surgery, ya yaba min sosai kuma ya nuna jindaɗinsa akan yadda na maida hankali sosai, a ranar kasa bachi nayi saboda farinciki duk bayan minti ɗaya zuwa biyu uku fuskarsa na ke gani. Hakan yasa na ƙara maida hankali akan karatuna, da muka samu hutu sai muka soma shirin ziyarar gida kasancewar dkanmu munyi marmarin gida saboda haka muna samun hutun muka shirya muka dawo gida. Bayan mun dawo Abuja da kwana biyu na fara shirye-shiryen zuwa gida sokoto domin ganin iyayena, ranar da anje gurin kitso na dawo sai Daddy ya aiko yana kirana. A ɓangaransa na sameshi tare da Momi Aisha wato Hajiyarmu, da sallama na shiga bayan na gaishesu sai na maida kaina ƙasa ina wasa da carpet zuciyata cike da son jin dalilin kiran nawa, da farko na yi tunanin akan tafiyata ne sokoto ko kuma karatu. ‘Wata ƙila zai ce na haƙura har sai mun sake samun wani hutun ne ko kuma wani abun’ Haka na yi ta saƙe-saƙe na kamin na ji abunda Daddy yake faɗa. “Nawwara ko akwai wani wanda kike so? Ko kuma iyayenki suke son haɗa ki da shi?” Na yi mamakin da ya yi min wannan tambayar, a take Jamal ya faɗo min a raina na fara tunanin ko ya faɗawa Daddy wani abun ne, ko shiyasa tun da na zo ban ganshi ba. Cikin natsuwa da ladabi na ɗaga kai na kalleshi na ce “A'a babu Daddy” “Mashallah” Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciyar da ke nuna ya jidaɗin hakan, ya gyara zamansa yana fuskanta ta sannan ya ce “Alhaji Bashir Makama aminane a tare muka taso tare muke duk wani abu da ya shafi siyasa ko kasuwanci, sai dai shi be cika zama a garin Abuja ba shiyasa ba ki wayeshi sosai ba, yafi zama Kaduna wato mahaifarsa sai kuma garuruwan da yake gabatar da kasuwancinsa. Few days ago mun tattaunada shi akan ɗansa, yana son haɗa zuri'a da ni, ni kuma na duba a cikin ƴaƴana na ga babu wacce ta dace da shi sai ke, na yi hakan ne ba dan komai ba sai dan sama miki rayuwa mai kyau da nagarta, na san idan har kika auri ɗansa zaki ji daɗi sosai, saboda yaron yana da aiki ba irin ƴaƴan masu kuɗin nan ba ne shashashu kuma yana son yaronsa sosai,

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});