Chapter 1
Chapter 1
[11/10/2019, 1+234 803 588 3279: *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy This Novel Is Free. But After This Free Book, Comes Payed one. 1⃣ “Bana son na yi aure a gidan da za'a saka min gadon dubu ɗari biyu da hansin su riƙa girmamani suna ganin girman da ganin mahaifina yana da rufin asiri, na fi son na yi aure gidan da za'a saka min gadon miliyan uku su dinga ganin mahaifina talaka ne suna raina min wayo. Ma'ana dai har yanzu ina kan bakana na auren mai kuɗi fiye da talaka!” Na yi dariya ina sauraren zance ko burin Jidda da ta saba nanata min a duk lokacin da muke zancen aure da ita. “Ƙawata ba za ki taɓa ganewa ba, kin fiye maida zancena shirme Wallahi Nawwara rayuwar nan ɗa muke sam bata dace da mu ba” Dariya na sake yi a karo na biyu kana na dube ta irin duban na nake mata a duk lokacin da nake son ta ɗauki zance na muhimmancin. “Kina da yawan buri Jidda kamar yadda nima nake da shi, sai dai duk da haka na ki be kai nawa ba, gwargwadon rufin asiri Jidda kuna da shi, amman kina tsawwalawa rayuwarki akan son aure mai kuɗi, ba ko wane kuɗi ba ne na halak, ba ko wane mai kuɗi ba ne bane mutumen arziki, da da yawanzu basa darajanta talaka basa ganin girman iyayen matansu, basa kunyar taka kowa saboda suna ganin suna da kuɗi. Wasu masu kuɗin maneman mata ne Jidda, ke da kike matarsu sai su wulaƙantaki musamman idan suka sa ke ɗin ba kowa bace, nafi sha'awar auren takala ɗan'uwana mai ilmi da ganin ƙimata, mutumen da zai taimake ni na gyara lahira ta, kuma na inganta rayuwar yaro na, ya mutunta iyayena ko da bayan raina, ni iya wannan ya wadatar da ni matuƙar yaƙar yana da halin da zai iya ciyar da ni” Jidda ta dafani a lokacin da ta lura da hawayen da ya sauko daga idona ba tare da sani ba har sai da ta yi min magana. “Share hawayenki Nawwara, nasan abunda kike ji, amman rayuwar nan da muke ciki ne bata da daɗi, ka tashi cikin talauci ka girma a haka kai ma kana son sauyin rayuwa, kana son ka taimaki iyayenka, karatu nan ma fa Nawwara ba zai yiyu ba idan babu kuɗi, idan baka da kuɗi kai ba kowa ba ne, yadda aka ga dama haka ake takaka, babu mai son takala sai Allah” Na yi murmushi ita kuma ta amsa kiran da Mahaifiyarta take mata ta tashi. Na san yadda ƙawata take ji haƙiƙa rayuwar talauci babu daɗi, sai dai ni har yanzu rayuwar masu kuɗi bata burgeni saboda nasan yadda take, ba ko wace ƴar takala ce ke auren mai kuɗi ta jidaɗin rayuwaba, ko da kuwa ya aje mata banki ne a cikin ɗakinta. “Kin gani ko kullum baƙin tuwon dawa sai na masara babu wani sauyi, ni Wallahi rayuwar nan ta isheni, ni ina tausayin rayuwar yarana idan nayi aure zasu tashi suna cin tuwon dawa duk suyi baƙi, ke Wallahi Nawwara da kwana ɗari da talaka ƙara kwana ɗaya da mai kuɗi” Jidda ce take wannan maganar, yayinda take dire kwanon samira mai ɗauke da ƙatowar mulmular tuwon dawa da miyar kuka, agabana. ‘Allah sarki rayuwa ku har kun samu tuwon dawa’ Na faɗa a raina, a fili kuma sai na ce. “Aifa sai ki yi mitarki kuma ki ci tuwonki dan ni dai a ƙoshe na ke” Jidda ta wara ido tana min kallonta na iskanci wanda ta saba min a duk lokacin da aljannun rashin mutunci suka hau kanta. “Maman Nura, Maman Nura yi sauri ki zo” Nayi saurin kai hannu ina rufe mata baki jin tana kiran mahaifiyarta, nasan wata ƙulalliya zata ƙulla min. “Jid” Ban yi furucin ba sai ga Maman Nura a cikin ɗakin wato mahaifiyar Jidda. “Maman Nura tace gida zata je da shi” Jidda ta faɗa sai Maman Nura ta ce “To bari a ƙara mata” Da sauri na ce. “Wallahi ƙarya take min Mama, ban ce ba” Juyowa ta yi ta watsa min wata uwar harara kamar zata zo ta fanɗareni da mari, kana ta nuna ni da yatsanta. “Kin gani Nawwara wannan halin naki yana ɓata min rai, kina rage ƙima idona, ko abu kika tarar a gidan nan ba zaki ɗauka ki kai gida ba, ni da Mamanki ba ɗaya ba ne ko? Allah wata rana sai na ƙwaɗa miki mari idan kina min irin wannan iskanci, fitsarriya” Ta juya a fusace ta fice. Ni ko na kaiwa Jidda duka. “Kin haɗa ni da ita kin jidaɗi” “Ai nasan idan ba haka na yi miki ba, ba za ki co shi ba, marar mutunci, ni idan naga abu a gidanku tambaya nake ba ɗauka nakr na tsire ba” Na girgiza kai ganin yadda take magana da tsire baki. “Allah ya shiryaki Jidda” “Amin Wallahi, idan Allah be shirya ni ba ai na shiga tara bama uku ba, Jidda ai sai Nawwara” Bayan Maman Nura ta ƙaro min tuwon na taso Jidda ta rakoni ƙofar gida, a lokacin ana kiran sallah magariba. A bakin ƙofar gidansu ta karɓe tuwon. “Kawo zan bawa Nura ya kai miki, kinga su idi can ƴan sa ido, ko Sallah ba zasu tashi su yi ba” Ta taimaka min matuƙa, domin nima kaina ina jin kunyar fitowa da kwano a wani gida saboda ƴan sa'idon unguwa masu zaman kashe wando, zaman ƙirga atamfarki da kuma inda zaki je ki dawo. Sallama nayi mata tare da sai da safe sannan na kama hanya, bayan nayi nisa sai na hango Nura tare ɗauke da kwanon tuwon, sauri na ƙara dan bana son ya cin ma, nasan halin Nura zai iya cin min a hanya ya ce karɓi tuwonki. Lokacin da na shiga gida har sai da na ɗan tsaya a bakin ƙofa jiransa, tuƙuna ya ƙaraso na karɓi tuwon yana mita ya juya ya koma, ni kuma na shiga gida ina doka sallama. “Amin wa'alaikissalam Nawwara” Ya faɗa yana aje butar da yayi alwala, sannan ya ɗauki tsohon rediyonsa da ke aje ya miƙa min. “Shiga da wannan ɗaki” “Tau Baba, Allah ya tsare” “Amin, Amin” Ya faɗa yana kallon kwanon tuwon da ke hannuna, kamin yasa kai ya fice. A ɗaki na samu Inna ita da Habiba da Sakina, da mai sunan mama, wato Jamila da muke kira da Ummi. “Wai Allah na” Na faɗa ina ƙoƙarin zama kusa da Inna. “Nawwara kin dawo?” “Eh ga tuwon dawa Maman Nura ta haɗo ni da shi” “Tau Allah ya saka mata da alheri, zuba ki ci tun safe rabonki da abinci Nawwara” Na tada kai na kalli Inna. “Ai ni matuƙar zaku ci, ko ban cin ba bana jin komai, amman idan na ci ku kuna jin yunwa hankalina ba zai kwanta ba, Habiba zuba ma Baba da Inna sai ku cinye sauran” Inna ta ce “Sai fa kin ci, ai ƙara su ma ɗazu Babanku ya samo naira hansi na basu suka siyo garin kwaki suka saka gishiri suka ci” “Habiba zuba min kaɗan, ina Noor wai?” Na tambaya ganin baya cikin ɗakin. “Na aike shi ya samomin batir gurin Hajara wai mu samu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119