Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sanda na take masa baya. Na yi baƙin cikin haɗa ido da shi domin a yanzu ko mutuwa ban tsana kamar yadda na tsanesa ba, da saninsa aka yi ma mahaifina komai saboda ƴar'uwarsa har suka kashe shi. Bayan fitarsa Baba Sulaiman ya shigo yana mana bayanin yadda abun ya wakana lokacin da suka isa station ɗin. “Ko da muka je dpo baya nan, muka faɗawa ƴan sanda da ke nan, sai suka ce wai matarsa ce ta danka ta zo ta tafi da shi da ɗansa, Ayuba ya ce ai ba shi da ɗa namiji ma, kuma jiya mun zo nan kuka hana mana shi, sai suka ce bayan tafiyar mu matar da ɗansa suka zo suka tafi da shi, a gurin aka riƙa rigima wai su zayi ma ƙazafi, ɗayan su har da barazanar a barshi ya harbe mu, da suka ga abun na mu bana wasa ba ne yasa suka kira dpo, yana zuwa ya rufe su da faɗa, yasa aka tuɓe kayan ƴan sanda da suka yi aikin dare aka shigar da su cell, ya bamu dubu ashirin ɗin sai kuma ya biyo mu nan yana ƙara ba mu haƙuri” Baba Dahiru yaja tsaki. “Allah ya waddaran ƙasar nan, ai daga gani da saninsa aka yi komai, kuma babu matakin da zasu ɗauka, Allah dai ya isar ma ɗan'uwanmu kawai” Ni kaina jikina be bani za a ɗauki wani matakin ba, saboda na san mahaifina ba kowa ba ne a cikin unguwarmu balle kuma a gari. Maƙocin mu ne yayi ma Baba wanka saboda Inna ta kasa duk da kasancewar ta iya raunin zuciya be barta ta iya masa wanka ba, ban tabbatar da mai rai ba a bakin komai ya ke ba sai da aka ɗauko karaga aka saka gawar Baba aka fita da shi waje dan yi masa Sallah. Allahu akbar shine abunda na iya faɗa a zuciyata, na kwantar da kaina jikin Jidda hawaye na bin fuskata. Baba ya samu mutane sosai daman mutumen mutane ne, kuma wannan abun da ya faru ya ƙarawa mutane ƙaunarsa, har wasu na baranar idan ba a ɗauki mataki ba zasu ƙona station ɗin. Bayan an kai shi makocinsa suka dawo, mazan unguwa na ta shigowa suna mana gaisuwa, ciki har da Bilal da Babansa. Mutanen da suke zuwa mana gaisuwa kamar turo su ake, maza da mata ta ko'ina gaisuwa suke zuwa mana suna yi ma Baba addu'ah, maƙota kuma na ta kawo mana abinci, sai kuma gidan Baban gida da suka haɗa kuɗi duka siyo mana buhun shimkafa. Can da yamma Baba Sulaiman ya shigo yana tambayar mu ko ana binsa bashi. “Sai dai a tambaya guraren da yake zama amman Malam be cika cin bashi ba, shi dai bar shi da zuwa gidan ciyaman neman kuɗi” “Toh zamu bincika, Alhaji Sani ma ya zo nan yace yana muku gaisuwa” “Toh muna amsawa, Allah ya bada lada” Baba Sulaiman ne yayi ta ɗawainiya da mu tun da Baba ya rasu har ranar da aka yi addu'ah ukunsa. A daren ranar sai gidan ya zame nama wayan kamar Baba be taɓa wanzuwa a cikin gidan ba. Ina daga cikin ɗaki na hango Habiba ta ɗauki tabarma ta je ta shimfiɗa gurin da Baba yake zama ta kwanta. Tausayinta ne ya kama ni na unƙura na tashi naje kusa da ita na zauna, sai ta ɗago kai ta kalleni. “Nawwara” “Na'am” Na amsa mata ina danne tausayinta da ke raina. “Yanzu ya zan yi Baba ya yafe min? Na yi tunanin Baba zai rayu na roƙi gafararsa wata rana” Hannu na kai na ɗaga kanta na ɗora saman cinyata yayinda fuskarta ke fuskantar ƙofar ɗakin Inna, cikin ƙarfin hali da dauriya na soma mata magana. “Idan har Allah ya yafe miki, to Baba ma ya yafe miki, amman Habiba kin ga abunda kika aikata be amfana miki komai ba, tun da kuɗin ma be amfana komai ba, da kin yi haƙuri da baki siyar da mutuncinki ba” “Wallahi Nawwara ban ɗauka Baba zai mutu ba, a tunani zai rayu ne, kuma ni ina ganin kamar bamu da wata mafita sai wannan” “Da sata kika je kika yi Habiba ko kika yi bara, zai fi wannan abun da kika aikata” Shiru ta yi tana shesshekar kuka, yayinda ni nake hawaye. Can ƙasa-ƙasa ta soma magana. “Masu kuɗi suna da kuɗi Nawwara amman basa taimako, babu ruwansu da matsalar mu, idan mun ci babu ruwansu idan ba mu ci ba sai dai mu mutu” Ajiyar zuciya na sauke cike da gasgata zancen Habiba, haƙiƙa masu abu na da shi amman babu ruwansu da mu, ko ɗan abincin nan a zuba a abawa maƙota basa yi. Tashi ta yi zaune tana kallona, cikin kuka ta soma magana. “Nawwara sai da na je gidan Hajiya Murja na faɗa mata halin da muke ciki, har ƙarya na yi mata Inna na ce tace a ara mata kuɗi, ta ce min bata da kuɗi amman dai za ta yi ma mijinta magana. Da na fito sai na haɗu da ɗanta Mustapha a harabar gidan, shi ya kirani ya tambayeni miya kawo ni gidan, na faɗa masa sai ya ce zai bani kuɗin amman na masa alƙawarin duk abunda ya ce zan masa, na ce na yi, muka fita daga gidan gaba ɗaya, ya fiddo kuɗi da yawa a aljihunsa ya ƙirga dubu ashirin, har zai ba ni sai kuma ya fasa, ya ce sai idan na aminta na na bashi abunda ya ke so yanzu, na ce mi yake so, ya ce kawai taɓa jikina zai yi sai ya bani kuɗi shi ba iskanci zai yi da ni ba, har da min ratsuwa” Ta yi shiru. Can kuma sai ta cigaba. “Na ƙi yarda na nufo haɓyar gida, har na kawo sai kuma na ga ba mu da wata mafita sai wannan, dole tasa na koma, ko da na koma ya fita, sai nasa mai gadinsa ya kirashi a waya yace ina nemansa, sai yace na same shi gidansu killers, haka na je gidan na same shi shi kaɗai a gidan, sai... Sai... Sai. Ya ya.. Riƙani Wallahi Nawwara cewa kawai yayi zai taɓa jikina ya ba ni kuɗi, amman shi ne ya kira har da abokinsa suka.. Suka.. Suka yi.. Yi iskaci da ni...” Ba shiri na buɗe baki ina kallonta hawaye na bin fuskata. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 9⃣ “Miyasa ba ki masa ihu ba?” “Mi zai sa na yi masa bayan ni na kaina? Idan na masa ihu ba zai ba ni kuɗin ba kuma zai iya dukana ma” Kwantar da ita na yi jikina, ina kuka kamar yadda ita na take. Har dare ya bara muna zaune ni da ita a gurin muna aikin kuka. Wannan abu shi ya zame min jiki, a duka lokacin da na keɓe ni kaɗai na kan yi kukana sosai, saboda tausayin rayuwar Inna da Sakina da Jamila, sai kuma Habiba da kullum na ke zullumin idan ciki be shige ta ba. Yau ce ranar da Baba ya cika sati ɗayda rasuwa, har kuma tsawon lokacin ba mu sake jin wani abu daga gurin ƴan sandan ba, da yamma Baba Sulaiman ya samu Inna a gida yana faɗa mata gobe zasu je su ji

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});