Chapter 92
Chapter 92
ko da na duba sai na ga number Rabi na yi mamakin kiranta a wannan lokacin sai dai hakan be hanani dauka ba. “Assalamu alaikum” “Wa'alaikissalam Nawwara kina gida?” “Ina gida lafiya dai?” “Lafiya kalau akan maganar nan ne, bana son na yi shigowar rana wani ya gan ne, alhalin kuma ba Oga Jibril ba ne ya aiko ni” “Yanzu zaki zo kenan” “Idan zan samu dama ba” “Allah ya kawo ki lafiya” Daga haka na kashe wayar sai ga kiran Jibril ya shigo wayata, da gangan na ki dauka saboda ina tunanin wata maganar zai min ta daban, har sai da ya yi min kira fiye da uku sai kuma ya aiko min da sako karta kwana wato sms cewar Noor ne yake son magana da ni, da ya sake kira sai na dauka cikin rashin walwalah saboda tsanarsa da na ke ji cikin raina. “Hello” “Babe-Naj ga Noor zai yi magana ina fatar kina lafiya” “Zan bashi but ki amsa min mana ko sanyi na ji” “Zan kashe wayar idan baka ba shi ba” “Allah ya huci zuciyarki, ya dorani akan ki Naj” Yana fadar haka ya mikawa Noor wayar. “Hello Momy ina wuni? Momy i miss you” “I miss you too miyasa ka bi Daddynka ba ka zo nan ba?” “Daddy ne ya zo da ni, kuma ya ce ke ma za ki zo gobe, Momy ki zo yanzu mu kwana nan dan Allah” “Ba zan zo ba Noor, gobe ma ba zan zo ba har abada ba zan zo ba, idan kana son zama da ni ka ce ya dawo da kai gidanmu” “Saboda me ba za ki zo ba?” “Saboda nan ne gidanmu ni ba zan zauna ko ina ba sai gidanmu” “Momy gidan yana da kyau fa, har ya fi na su Sadiq kyau dan Allah ki zo” “Ba zan zo ba Noor, idan kana son zama tare da mu ka ce ya dawo da kai gida gurin mu” “Momy zan yi kuka” Ya fada cikin muryarsa mai nuna yana shirin yin kuka da gaske. Sai na ji muryar Jibril yana fadin “No no don't cry Noor tana maka wasa ne kawai zata zo” Ni kuma na katse wayar na kalli Inna. “Inna rabi zata zo yanzu, akwai maganar da zamuyi da ita” “Wace magana ce?” “Wallahi nima ban sani ba, amman dai ta ce tana da muhimmanci sosai” “Da wa kike waya yanzu” “Noor ne” “Amman shine kike fada masa wannan maganar kamar wani babba? Kina son ki saka danki a damuwa ko? Ki raba masa hankali gida biyu” “Amman Inna ai kara na fada masa gaskiya saboda yasan ba zan taba zama da mahaifinsa ba tun yanzu” “Amman be kamata ki masa magana ta wannan hanyar ba, ki daina sauke masa haushin mahaifinsa akansa” “Inshallah Inna ba zan kara ba” “Allah ya kyauta gaba” Sai da na amsa da Amin sannan na tashi na soma duba dakin inda be kintsu ba kimtsa saboda kar Rabi ta zo ta tarar da dakin ba a natse ba. Tara saura kwata ta Rabi ta shigo gidanmu da lullubinta na katon gyale kai baka ma ce ita ba ce, duka muka hada baki gurin amsa mata sai na fita na shigo da ita cikin dakin ta gaisa da Inna sannan Inna da su Sakina da Jamila suka fita waje suka bar mu mu kadai. “Ina tunanin babu wani gurin da ya kamata mu yi maganar nan sama da gidanku shiyasa na zabi na tarar da ke a gida, kuma idan da dare ba kowa zai gan ni ba balle har a tsammaci wani abu” “Me kike so mu tattauna mai muhimmanci har haka?” “Na fada miki akan ki da kuma dan ki da kuma Noor” “Me muka yi?” “Ba ku yi komai ba sai dai wanda ake shirin yi muku” “Ban fahimta ba” Ta sauke ajiyar zuciya. “Nawwara ke kadai ce mace da zata iya tsamo Jibril daga tarkon Siraj a yanzu, ke kadaice zaki iya raba alakar da ke tsakaninsa da Siraj a yanzu” “Miye nawa a ciki da har zan shiga na raba alakarsu? Babu komai fa tsanina da Jibril” “Na san babu komai a tsakaninku a yanzu, amman ai akwai yaro tsakaninku, iya abunda na fahimta Oga Jibril yana son ki sosai, ke ce kadai zaki iya anrar da shi daga ramen da yake kokarin fadawa” “Ni fa ban gane wannan bayanin na ke ba” “Nawwara Siraj ba abokin kwarai ba ne, kokarin zamewa Oga jibril kafafu yake ya dilmiyar da shi, kokarin kwace duk wani abu da Jibril ya mallaka yake kokarin ganin ya zama na sa. Sunana Rabi'at Abdulrazak, ni ba bahaushiya ba ce ni ibira ce asalina ni yar jihar kogi ce, ina zaman gurin Antyna ne a Abuja bayan na gama karatu na, daga baya na samu aiki a kamfanin One on One limitless company da ke Abuja, da sannu na fara aikina kwarewata da kuma jajircewa ta a akan aiki yasa mahaifin Jibril wato Alhaji Baahir yake yaba min sosai kuma ya dauki yarda ya bani, lokacin da zai turo Jibril aiki a nan sokoto sai ya sa muka zo tare akan na rika kula da duk wani abu da Jibril yake yi saboda yana ganin kamar Jibril ba zai iya kula da kamfanin yadda ya kamata ba, da muka dawo nan sai Jibril yasa aka yi ma Siraj transfer daga Abuja zuwa nan, ban san cewa Siraj abokin Jibril ba ne sai a wannan lokacin, ba zan iya fada miki dalilin alakarsu ba domin ni ma ban sani ba, amman da aka dawo da shi nan sai Jibril ya dauki yarda da amana ya mika masa, idan be samu zuwa meeting ba Siraj yake turawa, komai za ayi sai ya ce a a nemi Siraj” Ta gyara zamanta kana ta yi dariya. “Ba ina kishin Siraj ba ne Nawwara, sai dai akwai abubuwan da na lura da su akan Siraj, ina tunanin kamar shi ya koya masa shan cocaine saboda ua haukarta shi ko kuma ya juyar da hankalinsa zuwa wani gurin ba dan damuwar Jibril kawai ba, idan har dan damuwa ce shi Siraj baya da ita? Miyasa baya sha sai Jibril yake bawa? Abu na biyu ni yake sa na kira mahaifinsa na fada masa dukan abunda yake gudana a kamfanin marar kyau, Siraj ne yayi kokarin kashe Noor saboda yana tunanin idan har Jibril ya san yana da da zai sashi ya daina abunda yake kuma ya natsu, wanda ba haka Siraj ke so ba kuma yana ganin kamar idan Noor yana raye dole wata alakar zata sake kulluwa tsakaninki da Jibril wanda baya son haka shi be ki ma Jibril ya mutu ya mamaye dukiyarsa ba, da hadarin ya faru sai ya dorawa Bilal laifin ta hanyar sanar da Jibril cewar wani ya fada masa cewar Bilal ne ya yi kokarin kashe Noor saboda yana bakinciki Jibril, wannan yasa Jibril ya koreshi daga aiki har ma yayi kokarin kai kararsa kotu amman sai Siraj ya hana a cewar su wai basu da hujja su jira har sai an samu wani abun na daban wanda zasu rike su yi hujja da shi, ke kanki rayuwarki tana cikin hadari domin Siraj zai iya sawa a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119