Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 73

Chapter 73

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zai san abunda ke ciki, kuma ina addu'a inshallah babu abunda zai sameni” “Tau Allah ya tsare ya kai lafiya, ni jiya ma duk a tsoro na kwana saboda gidan nan da yan kudi da aka bamu, yau zanje na kai gidan Ya Umma na fada mata komai duk shawarar da aka yanke idan kin dawo sai kiji” Ta karasa tana miko min dari biyar na hau Napep. “Tau Na gode sai na dawo” “A dawo lafiya Allah ya tsare, ga wayarki da kika bari jiya” Nasa hannu na karba, miss call talatin da bakwai Siraj ya yi min, sai kuma kiran Jibril guda daya, da kuma wata bakuwar number ni dai ban wani maida hankali kan wayar ba nasa kai na fice ina ta tuno abunda ya faru jiya sai na ji raina ya sosu. Yau na ji da wuri sai dai duk da hakan ya rigani zuwa, a gabansa na gyara office din na jera komai yadda ya dace sannan na hada masa tea, files din da aka kawo dake kofar office din farko na dauka ina duba wanda zai saka hannu na kai masa wanda kuma ni zan yi aikin na maida hankalina ina ta yi, misalin sha biyu na shiga na fada nasa meeting din da muke da su da kuma mutane da yake da appointment da su, be samu kansa ba sai biyu daidai saboda ganawa da yake da mutane, abun mamaki sai gashi ya fito da alwalarsa ya sauka saka ya yi sallah, ni dai already na yi sallah duk da kasancewar ina jin marata tana murda min tun Shekaran jiya alamar menstruation dina na daf da zuwa, sai dai na san kamin ta zo na kan yi kurajen fuska ko da kwara daya ne ko biyu, rashin ganin kurajen yasa ban maida hankali akan tararta ba. Bayan ya dawo ya shiga meeting, yana fitowa yasa na hada masa tea, na shiga office din ya fi a kirga ina kai masa files da documents, sannan na koma na cigaba da saka kwashe abubuwan da suke cikin computer ina sakawa a laptop, muma haka danjar nan tayi kara alamar da mutun a bakin kofar office din, a computer na ga Rabi sai na bude mata ta shigo fuskarta da murmurshi kamar kullum, wata bakar leda ta aje min saman table ta ce “Oga ya ce a baki wannan” Tana ajewa ya juya ya fita, ni kuma naja ledar na soma budewa, abaya ce mai dankwali green color sai dozing din pant da pad da kuma turare. Gabana ya fadi mi yake nufi ne, sauri mikewa na yi tsaye na duba baya ashe rigata ta bace, gashi abaya ce ba Hijab balle ya kare min, arzikina ma bakar abaya ce, amman ya aka yi ya zubo min ban ji ba? Wata irin kunya ce ta rufe ni tunanin daya fado min a rai shine. A haka naje meeting din ko dai bayan mun dawo cikin office haka ya faru? Kaddara dai ta riga fata, bathroom na shiga na tsabtace kaina sannan na wanke rigar da karamin saket dina da ya bace da pant dina, na saka abunda ya bani, sannan na kulle wadancan kayan a ledar na fito na saka a jakata. Ina zaune da kunyata sai gashi ya fito daga office dinsa yana fadin “Ba zamu samu damar cin abinci a kamfanin nan ba, saboda akwai wanda zan mu magana da shi a waje, saboda haka tare zamu fita sai na shiga meeting din ke kuma ki ci abinci” Ni dai ban ce komai ba kuma na ki na kalleshi, sai dai kijina na bani so yake na kalleshi din, na dauki jakata na rayata sannan na rika jakar dake hannunsa a dayan hannuna kuma laptop ce. Tare muka shiga motar ina jin kamar na natse saboda kunya, har muka isa ban kalli inda yake ba, shi kuma yana ta motsi yana son na kalleshi din. Kamfanin da muka je kamfanin Chinese ne yan nigerian da suke aiki ciki basa da yawa, komai a tsare gwanin sha'awa. Wani bahaushe ne mai far'a da son mutane ya tare mu kuma ya yi mana iso har inda za'ayi meeting din. Da zai shiga ya juyo yan karbi jakarsa da laptop din dake hannuna ya kalleni ya ce “Duk kika sake kika yi fira da wani sai na yanka miki baki” Be tsaya jiran amsar da zan bashi ba ya shigewarsa tare da mutumen, ni kuma na zauna a gurin ina kallon mutunen dake ta kai da kawo, bayan kamar minti biyar sai ga mutumen ya kawo min abinci na karba ina masa godiya ba dan ina iya ci ba, saboda mutane kowa kallona yake ba zan iya bude baki a irin wannan gurin na ci abinci ba wannan ba mutunci ba ne. Fira ya soma yi da ni sama sama yana danna laptop dinsa, ana nan yake labarta min cewar shi dan Zaria ne, muna haka wayata ta soma ringing, bakuwar number ce har na yi kamar karna dauka sai kuma na daga, muryar Sakina na ji tana kuka. “Anty ki yi sauri ki zo Noor ya samu accident gashi nan za a kai shi asibiti” “Wace asibiti?” Na tambaya hankalina a tashe. “Specialist Hospital” “Gani nan zuwa” Na kashe wayar a lokacin har na fara kuka, “Lafiya?” “Ɗa na ya yi haɗari” “Bari a fada masa mana” “A a” Ina fadin haka na fita da gudu hankalina a tashe har bana iya gani da kyau. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣2⃣ Sun samu kusan mintuna arba'in suna meeting din sannan daga karshe suka cimma matsaya daya akan kwangilar da kamfanin zai bawa kamfaninsu Jibril. Hannu ya mikawa Jibril suka gaisa sannan ya fito, daman hankalinta yana can gurin Nawwara zuciyarsa na raya masa tana can tana fira da wannan mutumen na dazu. Da ya fito sai ya samu Mutumen shi kadai yana ta aikinsa sai wasu mutun biyu da suka zauna a kujerar da ya bar Nawwara dazu, kamar ba zai tambaya a zatonsa tana can wani gurin ne ko kuma ta koma cikin mota. “Mai gida matar da kuke tare ta fita wai dan ta ya yi hatsari” Sai Jibril ya tsaya cak kana ya juyo ya kalleshi. “Dan ta?” Ya fada. “Ee tun dazu ta tafi na ce bari a fada maka sai ta ce a a” “Kasan matar da muke tare kuwa?” “Ee wacce kuka shigo tare, ai ni na tarboku na santa wata fara doguwa ba sosai ba mai dan fadin fuska tana sanye da abaya green” “Amman dan ta ka ji ta ce ko kanenta?” “Dan ta dai ta ce indai ba rudewa ta yi ba, saboda waya aka kira aka fada mata” “Kaji wani abu bayan wannan?” “A a gaskiya hankalinta a tashe yake bata ce komai ba” Da sauri Jibril ya fita daga harabar gurin direbansa na hangosa ya san a uzurce yake kuma ya san babu abunda ya tsana irin jira, tun kamin ya karaso ya janyo mota kuma ya bude masa. Har Jibril zai shiga sai kuma ya mika masa jakarsa da laptop dake hannunsa. “Nawwara ta tafi” “Ee naga ta fice da gudu tana kuka har wani na tambayarta a abunda ya faru bata dai kula shi

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});