Chapter 24
Chapter 24
ma nice ba ita ba, hawaye suka zubo min sai na yi saurin tashi tsaye ina faɗin. “Bari naje na siyo mata maganin zazzaɓi” Inna ta amsa min da tau cikin yanayin damuwa, ɗaki na nufa na ɗauko Hijabina ina kallon Habiba take kwance malala kamar lakka. Kamar na fasa kuka haka na fito ɗaga ɗakinmu bayan na ɗauko ƴan canjina na fita zuwa siyo mata magani, har na isa tunanin maganar Inna nake, ta yadda zan yi na hanata kawai na ke nema. Bayan mum gaisa da mai shagon maganin sai na miƙa masa ɗari biyu na ce ya haɗa min maganin zazzafi kala-kala. Ya haɗa min kusa kala takwas cikin har da na malaria da na ciwon kai da na zafin jiki, ya ɗora min a saman gilashin da suke ɗora magani ni kuma na karbi leda na saka ina jiran canji. Sai kawai na ga Mustapha cikin shagon kamar an jefoshi, matsawa yayi kusa da ni sosai yana min magana ta yadda babu wanda zai ji “Ki yi haƙuri da abunda ya faru ranar nan, Wallahi ba da ke nake ba da mai Napep ɗin daya ɗauko ki na ke” Ji na yi kamar ace akwai wuƙa kusa da ni na daɓa masa a ƙirji, wani ɗogon tsaki naja wanda ya jawo hankalin duk wanda ke shagon zuwa garemu, na ɗauki canjina na fice zuciyata na bugawa kamar zata fito saboda ɓacin rai. NOT EDITED ⚠️ SHARE, COMMENT, VOTE. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣7⃣ ‘Ba a banza ya baki haƙuri ba, taya zai baki haƙuri mutumen da ba ya ganin kowa da mutuncin, ba dake yake ba kika mareshi sai kuma yanzu ya zo ya baki haƙuri, lallai akwai abunda yake nufi da ke’ Shine abunda na ke ta saƙawa a zuciyata, a zahiri kuma sai nan nemin tsarin Allah akansa. “Allah ka min tsari da sherinsa” Har na iso gida ina ta saƙe-saƙen abubuwa biyu a raina, maganar zubar da cikin Habiba da kuma haƙurin da Mustapha ya ba ni. Na samu kaina da faɗuwar gaba sakamakon hango Bilal da na yi a tsaye ƙofar gidanmu, cikin rashin kuzari na ƙarasa daman can babu kuzarin a tare da ni. Lokacin da na ƙarasa kusa da ƙofar gidanmu sai na tsaya dai-dai inda yake tsaye ina masa sallama. “Assalamu alaikum” A maimakon ya amsa min sai kawai ya ɗaga idonsa dake ƙasa ya kalleni. “Miya hana ki zuwa aiki yau?” Ajiyar zuciya na fara saukewa sannan na haɗe yawun da ke bakina na fara magana a daƙishe. “Bana jindaɗi ne” “Miyasa baki kira kin sanar min ba?” Yanzu kan bansan mi zan ƙara ce masa ba, shirun da na yi ne ya bashi damar fassara ni da abunda yake hasashe. “Saboda kin yi zaton na ganki ko? Wallahi Nawancy ban ganki babu Hijab ba, lokacin sa kike aikinki ina can ina nawa aikin, ba zan miki alƙawari ba amman zan yi ƙoƙari na kawar da idona daga kallonki idan kina aiki” “Wallahi ba saboda haka ba ne Bilal, kawai akwai abunda ya ke damuna” “Ko zan iya sanin minene?” “Sanin ba shi da amfani, barin wannan sirrin a cikina zai fi min amfani” Magana nake kamar zan fara kuka saboda damuwar da ke raina. Shi kansa ya fahimci haka saboda be saba ganina cikin irin wannan yanayin ba. “Allah ya yaye miki damuwarki Nawancy, Allah ya zama gatanki, ƴa shiga dukan lamarinki ya tsareki daga dukan sheri, ya jiɓɓanci lamarinki, kada Allah ya barki da kanki” “Amin” Na amsa hawaye na bin fuskata. Ya lumshe ido ya buɗe. “Ki shiga ciki, ni zan wuce, daman na rubuta wasiƙa a gurin aiki amadadakin cewar baki da lafiya” “Zan shigo gobe” Na faɗa ina share hawayen idona. “Karki dakurawa kan ki, and if you need someone to talk to i'm here” “Thank you Bilal you have encouraged me every time, Without you I don't think I could ever be fine” Na faɗa kuka na cin ƙarfina sosai. Har ga Allah ina jindaɗin zama da Bilal yana ƙarfafan min guiwa, yana damuwa da damuwata ko kaɗan baya son ganin ɓacin raina. “Get some rest” Na gyaɗa masa kai sannan na shiga cikin gida ina jin kamar na rafke na faɗi. Ɗakinmu na nufa jiki babu ƙwari, sai na samu Habiba a zaune tare da Inna kwanon ruwa na gaban Habiba jiƙe da magani. Na zauna nima ina buɗe ledar maganin. “Gashi ya ce wannan uku zaki sha, wannan kuma biyu biyu sai wannan shi ma uku” Na faɗa mata yadda ya rubuta a jikin kwalin maganin, sauran kuma duka na ɗiba ne, wasu biyu wasu huɗu. “Tau ki bari har a jima ki sha, yanzu na jiƙa mata tagargade da gishiri ta sha” Cewar Inna ni kuma na kalleta cike da mamaki. “Tagargade da gishiri kuma Inna?” “Ee yana yanke mara, wai ko za a samu cikin ya zube” Wani dogon numfashi naja na sauke, na san ko na yi magana ba lallai ne Inna ta fahimta ba, idan har kuma nasa ta bar cikin a can gaba wani abun ƴa faru zata ɗora laifin a kaina. “Bani maganin na sha ko zan samu sauƙin zazzaɓin nan” Habiba ta faɗa tana miƙo min hannu. Tashi na yi na ɗebo mata ruwa na miƙa mata maganin ta sha, sannan na je na yi alwala har na yi sallah tunani ne a raina. A tare da ita muka kwana a ɗakin, duk bayan minti biyu zuwa uku Inna sai ya miƙa mata tagargaden ta sha, haka ta kwana wulle-wulle sai abun ya zame mata biyu ga zazzaɓi ga ciwon ciki. Ita ke ciwon amman ni na kwana kuka ina jin zafin ciwon kamar a jikina ya ke, can kusan asuba Allah ya bata sauƙi har ta samu bachi. Ni kuma na tashi da ciwon kai na yi alwala na yi sallah, ina zaune saman carpet ɗin ina karatun ƙur'ane har rana ta soma huduwa. Tashi na yi cikin ƙanƙanen lokaci na shirya na aika Sakina ta siyo kunu suka sha domin ni ko ruwa bana iya kaiwa a bakina. Haka na kama hanya zuwa gurin aiki ba tare da na saka komai a cikina ba, duk kuwa da kasancewar ana cewa fita ba a karya ba bashi da kyau. Har na isa gurin aikin jina nake kamar ba ni ba, sai nake jin kamar ba ni nake motsa jikina ba, wata ƙila saboda nauyin da na tashi yana min yau ne. As usual sai da nayi duk abunda ya dace tun daga kan rubuta suna da time na yi komai sannan na shiga cikin kamfanin na soma aikina. Ina daf da ƙarewa a ɗaki na ƙarshe, Amina ta shigo tana min magana kaɗan-kaɗan. “Ƙawata ana kiranki, wai kin yi mopping da ruwa da yawa, matar nan sai masifa take” “Wacece?” “Wata mai'aiki a nan ce amman ita babba ce dan har office tana da shi” Ba musu na bita muka tafi inda ta ce ana kirana ɗin wato a ɗakin dana fara mopping, abun mamaki sai na samu Zinatu tsaye a ɗakin tana sanye da suit da baƙin gilashi hannunta riƙe da wani ƙaramin akwati. “Nawwara ke kika yi mopping ɗin gurin nan?” Na ɗaga mata kai alamar Ee. “Amman fisabilillahi haka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119