Chapter 63
Chapter 63
game, yana shigowa hankalinta ya dawo kansa. “Mom taje zata yi magana da Nawwara abunda ka daɗe kana jira amman kuma sai naga kamar baka farinciki” Ya kalleta irin kallon nan na sai yanzu ya lura da maganar da take. “Ofcourse am happy i was just thinking of something else” “Like?” Sai yayi murmushin da ya bayyana haƙoransa ya miƙe ya shiga kitchen yana faɗin “Manta kawai ba wani abu bane mai muhimmaci” Freezer ya buɗe ya ɗauko gorar ruwa ya kai a bakinsa ya sha sai kuma ya nufi gurin window yana ta tunani. “Impossible” Ya sake cika bakinsa da ruwa, sai kuma ya yi murmushi yana sauke ajiyar zuciya. “I love you so much” Ya daɗe a kitchen ɗin sai da yaji motsin shigowar Mom sannan ya juyo ya fito riƙe da gorar ruwan ya nufo falo. “Mom ya kuka yi?” Ya tambaya tun kamin ta cire mayafin da ke kanta, sai dai bata bashi amsa ba sai da ta zauna saman kujera fuskarta da murmushi. “Sun ce ba zasu yafe ba” “You must be joking Mom” “Ka ci gidanku, ni zan maka wasa” Ya zauna kusa da ita yana kallon murmushin da ke fuskarta. “Na yi magana da su kuma sun ce sun yafe maka, baka ga yadda mahaifiyarta ta tarbeni ba kamar daman can babu komai” “Da gaske? Amman Nawwara fa?” Ta ɗanyi shiru sannan ta ce “Ita ma ta yafe maka har ma tace a gaisheka” “Mom da gaske” “Sai kaje ka tambaya idan baka yarda ba” Wani irin tsalle ya yi ya dare kamar mahaukaci. “Mom i love you so much” Mom ma tana farinciki ganin farincikin ɗanta, cikin zumuɗi ya fice daga falon ya nufi part ɗinsa. A ranar kasa bachi ya yi saboda farinciki, sai ya kwana yana istigifari da hamdala ga Ubangijinsa, a zatonsa da gaske Nawwara ta yafe masa har ma ta miƙo gaisuwar gunsa. Around eight o'clock in the morning Mustapha ya fito part ɗinsa zuwa part ɗin Mom, sai dai hango motar abokinsa da ya yi yasa shi tsayawa baƙin ƙofar yana jiran ya ƙaraso. NAWWARA POV. Cikin rashin daɗin rai na shiga gida, Inna ma ta lura da haka sai dai bata cemin komai a zatonta tsakanina da Bilal ne wani abu ya faru. Misalin takwas da rabi na dare muka ji sallama a ƙofar gida, Inna ce ta amsa ni kuna idona na kan Noor take ta faman game baya gajiya. Sarai muryar Hajiya mahaifiyar Mustapha a ɗaki kunnena a sallamarsa ta biyu, gabana ya faɗi ba dan tsoro ba sai dan tunanin abunda yake tafe da ita. Inna ce ta unƙura ta fita sai kuma ta dawo ta ɗauki tabarma ta sake fita, sama sama nake jiyo firar da suke da dukan alamu yafiya take nemawa ɗanta abun mamaki har da su wa'azi da nuna ƙaddara, zuwa can kuma dai na ji Inna ta kirani daga inda na ke na amsa mata sannan ya miƙe na fita. Hajiyar ce zaune saman tabarma yayinda Inna take zaune saman kujerar mata ta tsakar gida. “Nawwara ce” Hajiyar ta faɗa tare da kunna fitilar wayarta ta haska fuskata. “Ina wuni?” “Lafiya ƙalau, ayi ta haƙuri kinji haka abubuwan duniya suke zuwa” “Allah ya bamu haƙuri” Daga haka ban ƙara cewa komai ba na miƙe tsaye na dawo ɗaki. Bata ɗauki tsawon lokaci ba tayi ma Inna sallama ta fice. Inna kamar jira take tana shigowa cikin ɗaki ta hau ni da masifa. “Wannan halin ba na ki ba ne Nawwara ba irin wannan tarbiyar muka baki ba, yafiya da afuwa ga wanda ya yi maka ba daidai shu aka fi ga musulmi, duk yadda zaki so Habiba ko ki nuna baƙincikinki akan mutuwarta be kai ni uwarta, tun da har na yafe kema ya cancancanta ki yafe, Ƙaddarace ni da ke duk ba mu wuce faɗawa a cikinta ba, yanzu da ace ɗan uwanki ne ya faɗa a wannan halin ko kuma ɗan ki Noor yaje yana neman yafiyar wata ba ta yafe masa ba zaki jidaɗi? Komai zaka yi ka riƙa kwatantawa da kanka” Tun da take maganar na ke hawaye, Inna ta min fahimta baibai, ta kasa gane irin zafin da ɓakincikin rashin yar'uwata da nake, ko da Habiba tana raye dole na ƙyamaci Mustapha saboda ya yaga mata rigar mutunci, tana ɗora min laifi akan Jibril saboda tana ganin kamar na zufafa da yawa, ni kou na san irin zafin da na ke ji idan na tuna wulaƙancin da ya yi min ya yi min ƙazafin zina a gaban iyayensa da iyayana yasa mutane unguwa suka kira ɗa na da shege ni kuma aka kira da karuwa, irin waɗannan mutanen ne take ganin na zufafa ƙiyayyata a garesu? “Ki yi haƙuri Inna, zan yi iya abunda zan iya na danne zuciya daga abunda take ji, dan Allah ki yi haƙuri kuma ki roƙa min Allah ya sassauta min abunda nake ji” Na faɗa ina ta kuka kamar zan haɗiye zuciya na mutu, sai Inna ta zauna kusa da ni ta dafani tana lallashina. Sama sama na samu bachi a daren ranar saboda kuka da na kwana ina yi ga kuma tunani ƴar uwata da ya dawo min sabo. Washe gari da wuri na farko bayan na gama raka'atayal fajir sai na jira aka tayar da sallah na masallaccin da ke kusa da mu bayan na gama na karanta azkar na safe, da ayatul kursiyu na fara A 'oothu billaahi minash-Shaytaanir-rajeem. Allaahu laa 'ilaaha 'illaa Huwal-Hayyul-Qayyoom, laa ta'khuthuhu sinatun wa laa nawm, lahu maa fis-samaawaati wa maa fil-'ardh, man thai-lathee yashfa'u 'indahu 'illaa bi'ithnih, ya'lamu maa bayna 'aydeehim wa maa khalfahum, wa laa yuheetoona bishay'im-min 'ilmihi 'illaa bimaa shaa'a, wasi'a kursiyyuhus samaawaati wal'ardh, wa laa ya'ooduhu hifdhuhumaa, wa Huwal- 'Aliyyul- 'Adheem. sannan ɗora da ƙula'uzai Allahu ahad, Allahu assamad, Lam yalid walam yoolad, Walam yakun lahu kufuwan ahad. Qul a'aoothu birabbi alfalaq, Min sharri ma khalaq, Wamin sharri ghasiqin ithawaqab, Wamin sharri annaffathatifee al'uqad, Wamin sharri hasidin itha hasad. Qul a'aoothu birabbi annas, Maliki annas, Min sharri alwaswasi alkhannas, Allathee yuwaswisu fee sudoori annas, Mina aljinnati wannas. Sai kuma na karanta hasbiya ƙara bakwai Hasbiyallaahu laa 'ilaaha 'illaa Huwa 'alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-'Arshil-'Adheem Sai kuma na karanta Bismillaahil-lathee laa yadhurru ma'as-mihi shay'un fil-'ardhi wa laa fis-samaa'i wa Huwas-Samee 'ul- 'Aleem. Ƙafa uku. A'oothu bikalimaatil-laahit-taammaati min sharri maa khalaqa Sau uku Waɗannan addu'o'i ne na neman tsari matuƙar ka karantasu babu abunda zai same ka daga iska har tsafi har ma da wasu ƙwari masu cutarwa, bayan na gama na ɗora da azkar ɗin godiya ga Allah waɗanda ake son musulmi ya karanta safe da yamma. Sannan na rufe da shugabar istigifari wato Allaahumma 'Anta Rabbee laa 'ilaaha 'illaa 'Anta, khalaqtanee wa 'anaa 'abduka, wa 'anaa 'alaa 'ahdika wa wa'dika mas-tata'tu, 'a'oothu bika min sharri maa sana'tu, 'aboo'u laka bini'matika 'alayya, wa 'aboo'u bithanbee faghfir lee fa'innahu laa yaghfiruth-thunooba 'illaa 'Anta. Yana na gama na yi salatin annabi ɗari istigari ba ɗari, sannan na yi hasbiyalahu sau ɗari huɗu da hansi, wacce ake karantawa a duk lokacin da mutane yake cikin matsala na halin rayuwa ko neman mafita, kamar neman aure warwarewa al'amura duk ka lamuncin karantawa zaka samu mafita cikin gaggawa. Ko da na fito
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119