Chapter 19
Chapter 19
komai kawai mun yi magana kan Baba ne” “Nawwara ki yi haƙuri idan ma a duniya ba a yi komai ba, lahira za'ayi domin Allah baya zalumci kuma zai ƙwatar mana haƙƙinmu” “Haka ne, Inna kina da kuɗi a siyowa Habiba maganin Malaria?” “Duba a cikin jakata ba za'a rasa ba, tace kanta ke ciwo” Ban iya tsayawa amsa mata ba, na nufi ɗakin na ɗauko kuɗin na aiki Sakina ta je siyo mata, bata daɗe ba ta dawo da kuɗin wai sunje masallaci. Kayan jikana na tuɓe na koma gaban murhu ina hura wuta domin ɗora girkin rana, har na yi girkin na gama kuka nake a boye saboda bana son Inna ta gano ina kuka hakan zai raunana mata zuciya kuma dole zata tambayeni dalilin kukan wanda ba zan iya faɗa mata ba. Bayan na gama na shiga banɗaki na yi wanka tare da kuka a can, domin a nan babu wanda zai san da damuwata, bayan na fito na raba abincin na sake aikin Sakina ta je ta siyo mata maganin. Da kaina na ɓalla na bata ta sha na zuba mana abinci sai ita ta kasa ci saboda zazzaɓin ya rufeta sosai, jikinta ya yi zafi sosai. Ni kaina kasa cin abincin na yi, sai mutuwar Baba ta dawo min sabuwa, da ace ƴan sanda nan ba su masa duka ba, da be mutu ba da Habiba da ni da Inna duk ba mu shiga wannan halin ba. Bana son kowa yasan kukana hakan yasa na ɗauki buta na shiga banɗakina na ci kukana sao da na ƙoshi sannan wanke fuskata na fito, a lokacin ana kiran sallah la'asar. Ba laifi Habiba ta samu sauƙi bayan shan maganin da ta yi, da muƙa gama sallah magariba ba har waje ta fito muna ɗan taɓa fira da ita, har ma ta ci ciwon masarar da na yi, hakan ba ƙaramin faranta min rai ya yi ba, gar na samu sakewa na labartawa Inna zancen Bilal, babu irin ruwan albakar da Inna bata sa mishi ba, Habiba ma sai yabonsa take. Inna ce ta cilasta ni kiransa a waya na sanar masa tana son ganinsa. Bayan Sallah isha'i ya zo Inna tasa na shigo da shi har cikin gida ta yi masa godiya, bayan mun fito ni nake masa godiya duk da nasan cewar ba da sanin mahaifiyarsa ya yi mana wannan abun ba, da ba zata bari ba domin ta ƙi jinin ta ganmu tare ma balle kuma har kyauta ta shiga tsakaninmu, mun daɗe muna fira shi sannan muka yi sallama. Bayan na dawo nake labartawa Inna yadda gurin aikin yake da kuma irin ƙa'idojinsa sai kuma zancen yadda kace min Shugaban ya ke, ta yi murna sosai ita da Habiba sun ƙarfafa min gwuiwa kuma suka min addu'ar samun nasara. Washe gari naje na sanar da Jidda zancen samun aikina, ita ta yi murna sosai kusan sai na ce ta fini farinciki, haƙiƙa Jidda ta wuce ƙawa a gurina mun zama ƴan'uwan juna ni da ita, mun sha fira sosai yadda na ke labarta mata gurin aikinmu ita abun ma burgeta ya yi, wai ban sanar mata da wuri ba da ta kai takardunta na diploma sun ɗauke ta aiki a guri. Sai yamma na baro gidansu bayan na haɗu ni da kwanon shinkafa da miya, abincin da na ke marmari. *** *** *** MONDAY MORNING... Hankalina ya kwanta sosai a kwanan biyu da Habiba ta yi bata sake ko da ciwon kai ba, hakan ya gamsar da ni lallai malaria ce take damunta. Dukan mu shiri muke bayan mun gama karyawa, ni ina shirin zuwa gurin aiki su kuma suna shirin zuwa makaranta, ban shafa hoda ba bayan na shafa mai, domin kawaliya bata dame ni ba, balle ni da zan fita tun 6:30am. Uniform ɗin na ɗauko na cire daga cikin leda, dogon wando ne ash color da farar riga, sai kuma wata ƴar ƙaramar riga marar hannu da za a ɗora saman wacan farar rigar ita ma ash, sai da na gama kallo ni da Habiba sannan na saka. Cas na fito kamar wata ma'aikaciyar banki musamman da na saka baƙaƙen takalmin nan masu kama da cover shoes. “Wow Nawwara kin wanku” Cewar Habiba tana kallona, ni kuma na yi dariya ina mai jindaɗi a raina. Ba Habiba kaɗai ba har Noor da Inna sai da suka yaba ni, ni kaona na san shigar ta yi min kamar wata ma'aikaciya, idan ba wanda ya sani ba babu wanda zai ce aikin Mopping zan yi. Wata ƴar ƙaramar baƙar hula na ɗauka na saka a kitson da ke kaina, sannan na ɗora ƙaton Hijabi yaɗi huɗu da rabi na saka, a gaggauci na fito daga gida gudun kar na yi lattti gashi yau ne farkon zuwana, duk yadda Habiba ta so na tsaya mu fito tare ƙiyawa na yi gudun kar na ɓata lokaci. Sai da na kawo bakin titi sannan na tuna da hoton da aka ce na kawo, da gudu na koma gida na ɗauko na sake fitowa ina ɗan jin kunya saboda mutane da ke kai da kawo a unguwat sun ɗan fara fitowa, duk da yake ba za'aga uniform a jikina ba amman sai na samu kaina da jin kunya saboda ban saba saka wando na fita da shi ba. Ko da na isa kamfanin bakwai sauran minti biyar, yau kan sun tare a bakin ganin suna ɗan bincikata, sai na faɗa musu komai har ma na nuna musu uniform ɗin da ke jikina da kuma katin sheidata, sannan suka bar ni na wuce. Kamar yadda Bilal ya nuna min sai da na fara isa na saka sunana da lokacin da na shigo da kuma rana sannan suka nuna min gurin da zan aje Hijabi da wasu kaya idan na zo da su, na nufi gurin na na cire Hijabina na aje a lokar da suka ba makullinta, na samu kaina da jin kunya sosai ganin babu komai a jikina sai uniform ɗin da kuma ƴar ƙaramar hular da ke kaina, sai da na ɗan jima tsaye a gurin sannan na juyo na fara takowa, sai ɗaya ɗaga mutanen da ke reception ya ɗaga hannushi yana nuna min hular da ke kaina, a dole na juya na je na cire na aje, na juyo ina wani taku kamar wacce bata son saka ƙasa babu komai a tattare da ni sai kunya, shi kanshi ya lura da yanayina, hakan yasa ya sakar min murmushi, nima na sakar masa kaɗan idona a ware, ina kalle-kalle ala-ala na ke kar naga wanda na yasan ni har na nufi Lifted na danna ta buɗe na shiga sai na danna number 3 ta rufe ta soma tafiya da ni, zuciyata sai bugawa take da ƙarfi irin bugarwa nan na ɗoki da kuma tsoro a lokaci ɗaya. Muna isa number 3 ta buɗe na fito sai na samu masu irin uniform ɗina suna ta aikin gyara gurin, ganin duk mata ne yasa ni na ɗan saki jikina na nufi gurin da aka nuna min da zan ɗauki kayan aikina. A ciki na tarar da wata yarinya mai far'a da son mutane domin ita kaɗai ce ta amsa min sallamar da na yi har ta yi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119