Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 82

Chapter 82

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ke jin abunda na ke ji babu mai ji min zafi? Ni kadai na san irin wulakancin da na fuskanta a gidan Jibril amman yau Inna har ta tana marina saboda shi? Zama da mutane da kalubale shi yake canjawa mutum rayuwa Inna ta kasa fahimtar hakan. Har na isa gida kuka nake, mai Napep din har tambaya ya yi wai ko an yi min mutuwa ne nidai ban amsa shi ba, da hawayen fuskata na shiga gida Sakina da Jamila suna zaune waje suna shan iskar hadari da ke kadawa, yanayin shogowata yasa Sakina ta taso ta sauri ta tari ne sai ta haska fuskata. “Lafiya Anti Nawwara? Ko Noor ya mutu ne?” Na girgiza mata kai alamar a'a, ina kallon yanayinta da ya yi min kama da na Habiba, banbancinsu da Habiba ce rumgumeni zata yi ta fashe da kuka ko da kuwa bata san abunda na ke wa kuka ba. “Anti Nawwara miya faru?” Ta tambaya tana jijjigani zuciyarta cike da fargabar abunda ya saka ni kuka. “Na rasa komai Sakina, na rasa karatuna wanda shine gimshiken rayuwata saboda Jibril, na rasa mahaifina mai fahimtar kukana, na rasa yar'uwar da ke goyon bayana, yanzu kuma zan rasa Noor Inna kuma tana goyon bayan Jibril, ni kan miya ragemin a duniyar nan? Kowa baya fahimtata, babu mai jin yarena, ni kadai na ke kukana, damuwata ni kadai ta dama, ni kadai na ke jin zafina, duniya ta juya min baya ta kona min komai na farinciki, duk abunda na taba zafi yake min, mai amfanin kuma ta mayarda shi toka da na taba sai dai ya bi iska, na kasa gane bayana balle na fuskancin gaba, babu ranar tsayuwar hawayena” Ta rika hannuna tana kuka kamar yadda Habiba take min. “Allah yana tare da ke Anti Nawwara shi zai miki maganin komai” Na gyada kaina alamar gamsu har na saukarda nauyayyen ajiyar zuciya. Sannan na share hawayena na nufi dakinmu. “Habiba” Ina shiga na ambaci sunanta kamar tana jina, sai kuma na kwanta saman katifa ina hawaye, wayar da ke hannuna ta yi kara alamar sako, ina dubawa na ga number Jibril. _I'm so Sorry Nawwara i'm sorry_ Haka ya rubuta a sakon, wai na yi wurgi da wayar na kara fashewa da kuka. A ranar kwana na yi ina kaiwa Allah kukana saboda bachi ya yi kaura daga idona. Na mikawa Allah lamurana, sannan na bar masa zabi akan dukan abunda zai fi zama alheri a rayuwata, a ranar na roka idan ma mutuwa ce ta fi alheri a gareni Allah ya matso min da ita, idan kuma ba iyakar wahalata kenan ba, Allah ya bani zuciyar da zan iya dauka, saboda shi ya tsara min komai. Washe gari Inna bata dawo ba sai tara da rabi, ban ga annuri a fuskarta ba wanda hakan ke nuna har yanxu bata huce ba kenan, ban kuma ji ta ce na shirya na je ba, daman ni na ke kwana da shi sannan ita kuma da rana taje ni sai na dawo na yi wanka na shirya sannan na koma. A daki na sameta na durkusa kasa na rike kafafunta ina kukan da ni kadai nasan zafin fitar hawayena “Inna ki dubi girma Allah ki yafe min, Wallahi duk kika yi fushi da ni Allah ma fushi zai yi da ni, ke kadai kika rage min a duniyar nan, ba ni da wani gata sai na Ubangiji da yayi min ta hanyarki, zan iya jure komai amman ban da fushinki da rashinki babu dan da zaiyi albarka matukar uwarshi tana fushi da shi, mai yawan neman yafiyar mahaifiyarsa da mahaliccinsa kuma dan gata ne har a gurin Allah, kuma ba zai taba tabewa ba, yarda Allah tana tare da yardar iyaye, idan suka yarda da kai to Allah ma ya yarda da kai, ki taimaki rayuwa kada na zama daya daga cikin masu tabewa, kar soyyayyar wami yasa ki yi fushi da yarki” Zaunawa ta yi bakin gadon tana kallona fuskarta dauke da damuwa. “Ba zan taba fushi da ke ba, domin na san illar fushin uwa ga yayanta, na mareki ne kuma na daure miki fuska ne saboda ki gane abunda kika aikata babba ne, na san zuciyarki zata zargeni da cewar ina son Jibril fiye da ke, ba saboda kudin Jibril yasa na yi miki haka ba, da kudinsa na ke kwadayi da na cilasta miki komawa gidansa ko kuma kulla wata alaka da shi, ba wannan na ke dubi ba Nawwara, rayuwar dan ki ta nan gaba nake hangowa da kuma taki rayuwar, wata rana zaki gane gaskiya nake fada miki wata kila a lokacin bana raye, amman za ki gasgatani, ba zan taba cilasta miki gurin auren Jibril daman tun farko bamu cilasta miki ba, amman na san ko da mahaifinki yana raye kwatankwacin abunda na aikata shi zai aikata a gareki, ba zan taba fushi da ke ba” Na kwantar da kaina saman cinyoyinta wata kalar rahama ta uwa tana shiga cikina. “Na gode Inna, na miki alkawari ba zan sake yin abunda zai sa ki fushi ba, ko da kuwa abun nan baya min dadi” “Allah ya sauwake miki wannan rayuwa ya baki wanda zuciyarki take muradi wanda zai share miki kukanki kuma wanda za ki more hakurin da kika yi ta hanyarsa” “Amin” Sakina ta shigo tana tambayar jikin Noor, sai Inna ta amsa mata da “Ya ji sauki, yanzu wanka zan yi na koma” “Bari na shirya na je” Na fada ina kokarin tashi tsaye, sai Inna ta rike min hannu. “Aa ba sai kin je ba, ki hutar da kanki daga yau zuwa gobe” “Saboda mai?” “Saboda ki samu sukuni a zuciyarki, kuma ki shirya amsa tambayoyin da Noor zai miki, domin yana ta min na ce masa ban sani ba ke kadai kika sani, dan haka yana nan yana jiranki, kuma Jibril yasa an canja mana wata asibitin tun jiya da dare an kaimu wata” “Tau Inna” Na amsa ba dan raina ya so ba, tabbas Jibril na daf da rabani da dan na ni kadai na sha zafin daukar cikinsa na raineshi kuma na haifi abuna saboda kawai shi yana da dukiya. JIBRIL POV. Shiru ya yi ya rasa abunda zai cewa Abbah, zuwa can ya sauke ajiyar zuciya ya ce “Abbah sam na manta da ranar ma sai yanzu” “This is rubbish kasan hasarar kwangila irin wannan tana janyo a fara raina mana kamfani? Kowa ya sa rai mu za a bawa kwangilar nan amman saboda sakacinka komai ya lalace” “Abbah kasan ba guri daya hankalina yake a yanzu ba” “Fine ka mikawa Siraj ragamar kamfanin nan, a duk lokacin da ka dawo cikin hayyacinka sai ka kamfanin ya dawo hannunka, amman ba zai yiyu muyi ta hasara hakan nan kawai ba” “Okay Abbah nima hakan zai fi min an gaskiya bana cikin kwanciyar hankali a yanzu” “Ai kai ka jawa kanka komai saboda baka jin magana, da gaskiyar Hajiya (step mother dinsa) da take cewa na rika kyaleka duk da gangan kake komai” Ajiyar zuciya Jibril ya sauke be sake cewa komai ba, yana ta sauraren fadan da Abbah ke masa, kamin daga bisani ya kashe wayar. “Oh Allahna kai kadaine gatana” Ya furta yana shafa

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});