Chapter 71
Chapter 71
yana kokarin zama, abun ya fi tsaya masa a rai Zinatu da gaske tana son shi ko kuma ta yi ne kawai as a friend ita kuma Nawwara kishi ya rufeta. “Wow” Ya furta yana dora kafarsa daya saman daya yana lilo da kujerar. “Allah ya kara raba kanku” Bayan kamar thirty minutes Nawwara ta shigo Office din idonta a kasa. “Kana bukatar wani abun ne?” Kallonta yake, ya ji dadin abunda ya faru amman wannan halin da take ciki baya son shi ga hawayen da ta kasa dainawa har yanzu, yasan tana jin kwatankwacin irin zafin da yake ji a duk lokacin da ta kula wani ba shi ba. Mika hannu ya yi zai riko hannunta sai ta yanje ta yi cikinsa da masifa. “Miyasa kake son taba hannuna ne? Miyasa kuka dauki rumgumar mace da taba hannunta a matsayin wayewa? Baka san zunubin da ke akwai a taba hannun mace da ba muharramarka ba? Baka da rayuwa mai kyau Jibril” Uffan be ce mata ba har ta juya ta fita, sai dai maganganunta suna masa zafi, baya jindadin yadda duk maganar da ta zo mata a baki take fada masa, ciwon da ke damunsa ne ya taso masa har yana neman numfashinsa sai da ya dinga sauke ajiyar zuciya yana dafe zuciyar sannan ya samu sassauci har ya nufi freezer ya sha ruwa, sai kuma ya bude durowarsa ya dauko cocaine ya zo ya zauna gaban teburinsa ya soma shaka. Sai ga Nawwara ta shigo da wasu takardu a hannunta tsayawa ya yi kallonta kamar yadda ita ma take kallonsa. “Kana da meeting da pearls global company misalin sha biyu da rabi, wannan kuma daga Dr Ishak Hacker ne zaka saka hannune a maida masa” Ta fada tana dora masa takardun saman table dinsa, kamar be damu da ganin da tayi masa yana shan cocaine ba ya dauki pen ya saka hannu, ita kuma ta juya ta fice ba tare da ce masa komai ba. Wayarsa ya dauka ya kira Siraj. “Ka bincika?” “Eh amman ance bata da wani da kuma binciken ya nuna bata ma taba yin ciki ba” Ya busar da iskar bakinsa dan ba abunda yake son ji kenan ba. “Ka tabbata?” “Yes, walimar da kasa a shirya yau za'ayi” “Thank you Siraj ayi abunda ya dace” Ya katse kiran yana ta tunani, sam zuciyarsa bata yarda babu da tsakaninsa da Nawwara ba, ji yake kamar dai Siraj be yi binciken daidai ba, ko kuma Nawwara tasa a boye masa ne. Rabi ya kira dan jin yadda aka yi daman tun da ta kai kayan ta kirashi be dauka ba sai ta aiko masa da sako amman be bude ba. “Good morning Sir” “Ina jinki!” “Na kira wayarka baka daga ba kuma na aiko maka da sako, anyi komai yadda ya dace Sir sai dai ita kadai na yi ma siyayyar” Ta fada da zimmar ta ji abunda zai ce tace ba tayi ma yaronta ba dan ita a zatonta Jibril ya san da shi. “Eh daman ita kadai zaki yi ma” Yana fadar hakan ya kashe wayar yana jin kansa kamar marar lafiya. Sha biyu saura kwata Nawwara ta sake dawowa office din. “Akwai wani abun da ya kamata muje da shi gurin meeting din ne?” “Ee takardun kamfanin nan, suna cikin can” Ya nuna mata wani katon box dake lake da ginin gurin, karasawa ta yi tana kokarin budewa amman ta kasa. “Sai kin sa password” “Miye password din?” “N¹¹A²³W²¹W³¹A³³R¹³A” Sunanta ne zere sai mixing da aka yi da numbers, tana saka. Password din sai ya bude, farkon box din cocaine ce mai yawa, na biyu kuma zinari ne irin wanda aka ciro cikin kasa ba a sarrafashi ba, sai dollars dake binsu daga karshe ne takardun suke. “Duka zan dauko?” “Ki duba files din wanda aka rubutawa 001 zaki dauko” Daki-daki ta bisu har ta wanda yake magana akai ta dauko, sannan ya maida marfin box din ta rufe ta taso ta nufo table dinsa. “Miyasa kake son shan cocaine ne?” Yaja ragowar dake hancinsa sannan ya dauke idonsa daga barin kallonta. “Saboda na rage damuwa da bacin rai” “Waya fada maka tana cire damuwa?” Ya mike tsaye ya nufi gurin window ya tsaya tare da sanya hannayensa aljihu. “A lokacin da na haukace akan tunaninki na rabu da kowa, na watsar da dukan abokaina sai Allah ya hadani da Siraj, shi ne kadai mutumen da ya taimaki rayuwata na fara dawowa mutum da wannan cocaine din, a duk lokacin na shakata ina samun sassauci akan tunaninki, musamman a lokacin da take buguna ba kamar yanzu da bata min aiki ba” “Amman miyasa kake sha?” “Saboda ta zame min jiki” “Idan har kana son ka kore damuwa ka rika daukar kur'ane kana karatu, ina tunanin ka san illar wannan cocaine din” Ya juyo ya kalleta. “Ba ni da wani zabi ne saboda tunaninki na fara shanta” NAWWARA POV. Ban sake ce masa komai ba na juyo ya baro office din, zuciya cike da rashin jindadin halin rayuwar da jibril yake yi. Yanzu akaf a familynsa a rasa wanda zai tsaya ya fada masa gaskiya akan rayuwa? Babu mai iya bata lokacinsa ya zauna da Jibril ko dana dan lokaci ne? Abun bakiciki ne namiji kamarsa ace be san abunda ya dace ba, shikenan saboda be da mahaifiya a raye mahaifinsa ba zai iya zauna da shi ya fahimci rayuwar dansa ba? Ni kadai ce zan iya canja rayuwar Jibril a yanzu, saboda ni kawai yake saurare ni ce kadai zan matsa tsawa be maida min ba, dole na taimaki rayuwarsa ko dan dana ba ni da wani zabi a yanzu da ya wuce wannan ko na ki ko na so uban Noor ne kuma dole wata rana Noor zai yi rayuwa da Ubansa, idan bashi a tafarki mai kyau taya Noor zai kalleshi? Tunani kenan sai kuma wata zuciyar ta jefo min tambaya. ‘Yanzu mutumen da ya wulakanta ya nuna baki da muhimmanci a rayuwarsa mutumen da ya kiraki da annoba? Yasa aka kiraki karuwa? Ya ce dan da kike takama da shi ba nasa ba ne? Ya wulakanta mahaifanki ya tozarta ki a idon duniya ya ce ganin bakin maciji ya fi masa ganinki, shi zaki taimaka? Irin wannan mutumen zaki tausayawa? Wanda ya kasa baki taimako daga lokacin da kike bukatarsa ya fifita karuwa akanki?’ “No no ba zan iya ba” Na furta a fili idanuwana cike da tsanarsa. “Yaje ya yi ta yin rayuwar da yake ganin zata fidda shi ni babu ruwana a ciki” Ina rufe bakina yana fitowa daga office, ni kuma na mike tsaye na dauki takardun. “Naj ina ɗa na?” Wani wawan kallo na watsa masa. “Da kuma? Ko cocaine din ta fara bugunka?” “Ina cikin hayyacina na san abunda na ke ina dana ko yata?” “Mtssss kana hauka Jibril baka ma san abunda kake fada ba” Ina yin gaba na ji an fisgoni na fado kirjinsa sai ya rumgume kamkam ya lumshe ido, ina jin yadda zuciyarsa ke mugun bugawa numfashinsa kuma na fita da sauri. Iya karfin da Allah ya bani da kuma dabara ya saka wajen ganin na kwace kaina amman na kasa ko kwakkwaran motsi, saboda karfinsa ya ninka nawa sau
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119