Chapter 49
Chapter 49
abunda zan yi sai dai su kalleshi a a matsayin butulci. Duk da maganar da Daddy ya ce yi ya sai da aka kwashe wata ɗaya har da kwanaki rana ɗaya Momy ta kirani wai na je na shirya yau Jibril zai zo ganina, gabana ya faɗi sosai har na ji ina ma ba zai zo ba har abada domin na san zuwan nasa ba alheri ba ne. Wanka na sake na saka wasu tufafin kwaliya kan ban yi ba, mai ma dan ya zamin ne jikine yasa na shafa, daman ta saka mai aikinmu ta shirya masa abinci da lemu haɗin gida. Haka na zauna tun sha biyu na rana har magariba be zo ba kuma be kira ba, misalin goma sha na dare Momy ta shigo ɗakina wai na taso gashi can ya zo, Ba musu na tashi na cire kayan bachi dake jikina na ɗauki atamfa na saka da mayafi na saka takalmi na fito jikina a sanyaye na nufi part ɗin baƙi. Tun a bakin ƙofar falon ƙamshin turarensa ya daki hancina hakan yasa gabana faɗuwa, da sallama na shiga falon amman be amsa min ba sai dai idonsa na kaina har na zauna a kujera na soma miƙo masa gaisuwa a kufile, nan ma be amsa ba, sai wani shan ƙamshin yake ya tsare fuskata da kallo kamar mai neman munina. “Saboda ke Daddyna yasa na dawo garin nan, saboda ke ya cilasta min dawo wa da aiki a nigeria gaba daya, ke dan Allah ba ki jin kunyar yadda ake ta turaki gurin namiji kamar ni?” Ɗagowa na yi na kalleshi kallon mamaki da takaici ina ma zai san abunda ke zuciyata da ya taimakamin ya rabu da ni, akwai tsantsan tsoro da fargaba a tare da ni a wacan lokacin shine abunda yake ta cutar da ni sai kuma zurfin ciki da ya zame min hali. “Zuwanka da rashin zuwanka duka ɗaya ne a gurina, ni dai ina neman izininka zan koma makaranta” Be ci komai daga abunda Momy tasa aka kawo masa ba, sai ya tashi tsaye ya nufo inda nake ya zauna kusa da ni har jikinsa na shafar nawa ya matso da fuskarsa kusa da tawa ta yadda ni kaɗai zan iya jin abunda zai fito bakinsa sannan ya kalleni ya na ƙara haɗe fuska ya ce. “Ba aure kika zaɓa ba? Tam zaman aure zaki yi babu ke babu karatu har a bada, ai baki san waye Jibril ba kina da butaƙar sanin wanene tuƙunan” Yana kaiwa nan ya tashi tsaye na saka hannunsa aljihu ya ciro kuɗi ya watsa min. “Ga tsiyarki nan” Ni kuma na miƙe tsaye ina kallonsa na ce “Tsiyarka dai, tsiyar da ta saka baka ganin kowa da mutunci, na ji ni ƴar talaka ce kuma ni talaka ce amman haka ba zai baka damar ka yi min duk kalar wulaƙancin da ka ga dama ba, kuɗi kawai kake da shi Jibril ni kuma na ɗara ka da tarbiya da biyayya” Murmushin gefen fuska ya yi ya taɓe baki. “Fine, zamu gani” Daga haka ya fice, ni kuma na koma cikin gida ko inda kuɗin suke ban kalla ba, zuciyata cike da ƙuna. Tun daga wannan lokacin be kuma sake zuwaba sai da aka sake yin wata ɗaya sannan ya kira Momy a waya yana tambayar lafiyata shi ma kuma na san cilasta masa aka yi, bayan ya tambayi Momy aka kawo min wayar sai ya kashe ba tare da ya ce da ni komai ba, a ranar n samu Momy na yi mata bayani akan bana son Jibril kuma bana son zaman aure da shi sai ta muna min na yi haƙuri komai zai wuce da zarar na tare a gidansa, ganin bata goya min bayan rabuwa da shi ba yasa na samu Daddyda kaina na kuka masa halin Jibril da abunda na ke hangowa a zamantakewar auren da zamu yi, amman sai ya bani haƙuri saboda a tunaninsa saboda na daɗe a gidana ne yasa nake wannan tunanin shi ma sai ya kasa fahimta ta, wannan ƙorafin da na kaima yasa ya kira mahaifin Jibril ya yi masa magana akan tarewar mu. A cikin watan nan aka yi kawo lefena kayan masu kyau da tsada, bayan sati ɗaya aka yi walimarta Daddy ya aika da ƙaramar mota aka ɗauko Mama da wasu daga ƴan'uwanta da kuma ƴan'uwan Baba. Ranar da akayi walimar aka kaini gidansa bayan anyi min huɗuba sosai ciki har da Mama da take ta kukan rabuwa da ni, ni kaina ba zan iya misalta irin kuka da na yi a wannan ranar ba. Tun tara na dare aka kaini gidansa amman abokansa basu shigo da shi ba sai ƙarfe goma sha biyu, su kansu kamar sun sam baya son auren suka mana addu'a suka fice tare da wasu ƙawayena. Misalin ƙarfe ɗaya na dare ya bar gidan, ban saka shi a ido ba har garin Allah ya waye, haka na kwana na wuni be shigo gidan ba har sai da aka kwana huɗu tsoro duk ya kamani saboda ƙaton gida ne gashi ni kaɗai ke ciki sai ƴan aiki da safe ne kawai ake aiko mana da abinci daga gidan Momy, yau ma da yake rana da huɗu ne ba a kawo ba ni na girka da kaina. Sai a ranar na biyar ya shigo shi ma kuma tare da budurwa Aisha, a gidan suka wuni suka kwana idan yana buƙatar wani abun ko kuma tana buƙata sai ya aiko min da saƙo a waya na tashi na yi musu, ni dai na yi ma kaina alƙwarin ba zan taɓa nuna masa ina jin zafin abunda yake ba, ba kuma zan taɓa saɓa umarnin iyayena na cewar na yi duk abunda ya saka ni. Ranar da na gaji da zama gida na fita maƙota, gidan wata matar na shiga wacce gidanta ke kusa da nawa sosai, ba laifi matar tana da son mutane da far'a Cikin ƙanƙanen lokaci muka sabu har ta kai gidan naje gidanta sai dare zan dawo shi ma kuma idan mijinta ya dawo, ita da kanta ta fara fahimtar irin zaman da nake da miji har ta tambaye ni na labarta mata kaɗan sai ta bani shawarwari akan na daina biye masa kuma na nuna wayeta sosai saboda shi yana shiga ƙasashen turawa ne dole idonsa zai buɗe da yawa. Gaskiya Ummi Faisak na da kirki na koyi abubuwa da dama a gunta ciki har da girki da kuma iya kwalliya, sai dai ban taɓa gwada ko ɗaya ba saboda na san irin mijin da na ke aure. Wata rana ina gidanta har dare sai gashi ya kira ni na ce masa ina maƙota yanzu zan so, ko da na fito sai na same shi bakin titi yana jiran ƙarasowata shi da wani abokinsa, ina isowa ya wanke min fuska da mari da har sai da na ga wasu ƙananan taurari, har abokinsa ya yi ƙoƙarin riƙeni saboda tangal-tangal da na yi zan faɗi, abun mamaki sai ya fara faɗa da abokinsa kamar zai cinye sa wai taya zai yi ƙoƙarin riƙa masa mata ai ko baya so na yasan zafina na matarsa kar an ya sake masa haka. A ranar na wuni da zugin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119