Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 35

Chapter 35

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tambayeta inda ta samo wannan kayan domin ita kanta tasan na san wannan kayan yafi ƙarfinta, bata ɓoye min komai ba ta faɗa min daman can Jidda bata ɓoye min komai. “Wallahi Mustapha ne ya kawo ya ce idan zanje na riƙa miki wannan, wai kar nake hannu sake, daman ina ta tunanin abunda zan riƙo miki dan bani da kuɗi kuma bana son zuwa haka nan” “Daman kuna waya da shi?” “A'a ɗazu dai ne ya zo yake tambayata jikinki kuma ya bani number wayarsa wai idan zanje dubiyarki na faɗa masa, shine fa ya kwaso min wannan kayan” Bana son Jidda ta zargi wani abu, hakan yasa ban ƙara masa wata tambayar ba, sai kawai muka ɗauko wata firar. Sai da aka kira sallah magariba sannan na rakata ƙofar gida ta wuce tana mintar rashin adalci na mai kamfanin da nake aiki, domin na labarta masa cewar ya koreni. Tun daga wannan ranar kullum sai Mustapha ya aiko da saƙon a gidanmu da sunan ganin lafiyar jikina, wasiƙar gurin aiki kam kullum sai tazo gidanmu bayan ta waya da ake aiko min, tun Inna na lallaɓa na koma aikin har ta gaji ta zuba min ido domin ta fahimci ba zan koma ɗin ba, na kan faɗa mata ni bana son aiki a kamfanin ne saboda dokokin kamfanin. Bilal ma ya yi mamaki matuƙa ji da ganin yadda kamfanin yake neman na koma aikin bayan ance an koreni, shi da kansa yake faɗa min ko da harkar kasuwanci kanfanin zai ƙulla da kai da zai ci riba matuƙar suka koreka ba zasu nemeka ba balle kuma ma'aikaci, babu irin tambayar da bai min ba akan ko nasan wanine a kanfanin amman na nuna masa ni bansan kowa ba har ma na yi masa iƙirarin cewar ai na fada cewar ban yafe Haƙƙina ba wata ƙila shiyasa suke son na dawo aikin. Sam ban taɓa ɗaukar lamarin Mustapha azimun ba ne sai yau da mahaifiyarsa ta zo dubani, ita kanta Inna mamaki ya cikata kuma ta ɗan tsorata da lamarin kamar yadda nima nake ta almarar abun tare da tunanin abunda yake ƙoƙarin aikatawa. Kana ganinta kasan zuwan cilas ne domin ƙyamar gidanmu take sosai, zama na sai ya gagareta sai wani kallon gidan take a hankaɗe a tsaye ta yi min ya jiki ni kuma na bawa banza ajiyarta har sai da Inna ta amsa ta tana ta ƙoƙarin kareni, saboda ta tsarku da yadda na share Hajiyar a tsaye ko gefenta ban kalla ba balle har na iya gaisheta. “Iska ne da ita abubuwan ne sai a hankali” Ta taɓe baki tana gyara tsayuwar gilashin idonta. “Daman Son ne ya faɗa min akwai yarinyar da kai asibiti yana son na zo na dubata, ni zan wuce” Ko sakon biyar bata ƙara a gidanmu ba ta fice tana wani irin taku na ƙasaita Inna ta bita tana masa godiya, ni kuma na bita da harara, daman ba zan lissafata a cikin mutane mn da suka mana gaisuwar Habiba ko Baba ba duk da bana iya tantance kowa da kowa amman da tazo da dole wasu zasu ganta ko da ba ni ba, gashi tsanar ɗanta ya dasa nin tsanarta musamman yanzu dana fahimcin bana sha'awar mutane irinmu. Inna na dawowa daga rakiyarta ta cire takalmin ta buga min a kai, kana ta nuna ni da shi tana faɗin “Allah ya canja miki wannan baƙin halin da ya taso miki, ai ba ita kika kunyata ba ni kika kunyata” Tana faɗar haka ta nufi ɗaki ranta a ɓace, rabon da Inna ta ɗauki wani abu ta dakeni tun ina junior high school lokacin da na zo wani hutu, amman yau gashi ranta ya ɓace har ta buga min takalme a kai saboda ɓacin rai. Tashi na yi na bita ɗaki na bata haƙuri tare da shaida mata ba zan sake sannan muka shirya da ita har ma tayi min bitar zaman da mutane da kuma taka tsantsan na ka samu ka rabu da kowa lafiya. Haka muka zauna muna ta fira har su Noor suka dawo daga makarantar allo na tura masa karantunsa ya wanke allon yana ta murna wai malaminsu ya ce ya iya idan yaje gida ya wanke allo gobe yi masa wani rubutun. Bayan sallah magariba Bilal ya sallamomin kamar yadda ya saba sai dai yau sallamar tasa ta musammance domin firar kansa yake min wai mutane nata maganar ya kamata ya yi aure har da ƴan gidansu, ni dai murmushi kawai nake inda kuma ya kamata na yi dariya sai nayi dariya, har muka rabu beji wata kalma da yake zato daga bakina ba, hasalima ban barshi ya daɗe kamar yadda ya saba ba ganin inda akalar labarinsa ya dosa a yau. Misalin tara da rabi muka kulle gidanmu bayan mun gama fira da Bilal, na bawa Sakina ta kai min wayata maƙota saboda na samu caji, sai na alwalar na shigo ɗakin Inna na yi sallah isha'i, sannan na shiga na gyarawa su Sakina gurin kwanansu, ni kuma na dawo ɗakin Inna domin a yanzu na daina barinta tana kwana ita kaɗai. Saman gado muka haye ni da Inna Noor na bayana daman duk inda nake kwana a nan yake kwanan, na yi matashin kai da fillon Habiba kamar yadda na saba sannan na yi Noor addu'ah bayan wacce ya karanta ta shiga bachi, ni ma na yi muka kwanta cike da aminci da salama. Can cikin bachi naji Inna na tashina a hankali, ina buɗe ido hankalina ya tashi sosai, sakamakon jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar gidanmu da muka ji ana yi, ashe nice bachi ya lula da ni sosai ban ji ba har sai da aka tasheni su Sakina da Jamila kan tuni suka ji har sunyo ɗakinku sun ta ɓoya bayan Inna suna kuka, Noor ma yana ƙanƙame da Inna jikinsa sai rawa yake. “Ku shige ƙarƙashin gado” Inna ta faɗa kaɗan-kaɗan, ni kan araina na ce wane irin ƙarƙashin gado kuma ƙarƙashin gadon da itace ne muka saka a ƙasa ni da Habiba, saboda a samu yabuɗaɗɗiyar katifar ta tsaya. Kamin mu yi wani unƙuri sai dirowar mutane muka ji cikin ɗakinmu, daman ƙofar ɗakin ta cire ta can farkon shigowa gidace kawai ta rage muke rufe gidan da ita. Fitila mai haske sosai ɗayansu ya dallo min ba shiri na rumtse ido jikina na rawa na rumgume Inna ina saki fitsari abunka da mai mugun tsoro... TO SU WAYE KUMA WAƊANNAN😨😱 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣4⃣ Sakina da Jamila ne suka saka da Noor ne suka ihu ganin bindiga nikan dabam idanuwana a rufe suke addu'a kawai nake karantowa. “Ku yi mana shiru..” Ɗaya daga cikinsu ya faɗa a tsawace cikin wata murya mai kamar doro, sai duk suka yi tsif kamar babu su a gurin. “Dan Allah dan Annabi karku cutar min da yara ku yi haƙuri” Shine abunda Inna take ta roƙo muryarta na rawa alamar tsoro yana tare da ita. “Ki kwantar da hankalinki ba zamu miki komai ba ba zamu taɓa kowa na ki ba, kuɗi muke so ko abun kuɗi” Jin wannan yasa na sassauta riƙon da nayi wa Inna na buɗe ido tare da ɗagowa na kalli fuskokin waɗannan mutane da suka zo

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});