Chapter 68
Chapter 68
zai cinyeta. “Lokacin cin abinci ya yi, a nan zaki ci ko restaurant zamu je?” “Ka ce min idan uku ta yi zan iya zuwa gida idan har babu aiki da yawa, kuma na ga yanzu uku sauran kwata” Ta fada ba tare da ta kalleshi ba dan gaba daya ta tattara hankalinta ya maida kan computer. “Ee amman a ka'ida karfe biyu da rabi zuwa uku ma'aikata suke zuwa cin abincin rana, taso muje restaurant” Mike ta yi tsaye yana gaba tana biye har suka sauko kasa gaba daya, tare suke daga kafa kuma su aje tare har suka isa restaurant din dake cikin kamfanin, wani abun da ya bawa Nawwara mamaki suna shiga sai duk wanda ke gurin ya tashi ya fita, aka barsu su kadai daga ita sai shi. Karasa ya yi can guri wani teble wanda shi kadai yake zama akansa ya zauna ita ma ta zauna a kujerar dake fuskantar tasa. Waiter ne ya zo da sauri yana tambayar abunda za a kawo musu. “Fried rice and chicken soup” “And drink?” “Fanta” Ya juyo gurin Jibril. “And you Sir” A hankali ya juyo ya kalleshi ba dan yasan a abunda yake tambaya ba sai a lokacin ya kula da shi domin gaba daya hankalinsa yana gurin Nawwara. “And you Sir” Ya sake maimatawa ganin kamar be ji abunda ya ce ba. “Just water” Nawwara ta masa wani kallo “Ni ladai zan ci abincin kenan?” “No” Ya yi saurin amsa mata sannan ya sake kallon mutumen ya ce “White rice and pepper soup” “Drink?” “Lemun juice” “Okay” Ya juya da sauri ya koma inda ya fito. Cikin yan seconds sai ga abincin an kawo musu, Nawwara ce ta fara dan ta nuna masa ita fa cin abincin kawai ya kawota ba komai ba, shi kan kasa taba abincin ya yi ya tsura mata ido kamar mai kirga lomomin da take, zuwa can ta dago ta kalleshi, sai ya yi saurin daukar spoon ya soma wasa da abinci dan har ga Allah baya jin cin abincin, kawai saboda ita ta samu ta ci ne yasa shi zuwa ko ba komai hakan zai kara masa kusanci da ita, yadda take cin abinci mugun burgeshi take ya tattara hankalinsa gaba daya ya mika mata, har ta gama cin abinci be yi ko da loma daya ba. Wani abun da ya ba waiters din mamaki biya bill din abunda be taba yi ba, idan ba ya ci abinci a guri sai dai pa dinsa ya biya ko da kuwa shi da wani suka ci, amman yau shi ya biya da kansa sannan suka fita. A lifter ma kallota yake ta yi zuciyarsa na mugun fisgarshi kamar zata fasa kirjinsa ta fito. “Can i hug you?” Ta juyo da sauri ta kalleshi kamar yadda yake kallonta, idanuwansa sun yi fari kal har wani ruwa ya kwanta a ciki. “Baka da hankali Jibril, ka rumgume ni muharramarka ce? Ko dai ka dauka kamar Aisha na ke ne? Gaskiya kana bukatar komawa makaranta ka fahimci addini sosai” “Am sorry” Ya furta yana dauke idonsa daga kallonta so zai samu sauki zuciya, tare da danke hannunsa ya matse sosai. Suna shiga Office ya wuce Office dinsa ya zauna saman kujera ya dora hannunsa saman goshinsa ya rufe ido yana sauraren bugun zuciyarsa. Bayan an mintuna Nawwara ta shigo Office din rike da jakarta. “Ni zan wuce” Bude ido ya yi ya kalleta sai ya dauki wayarsa ya kira direbansa, yana yin picking. “Get ready” Yana fadar haka ya kashe wayar, da kansa ya dauki akwatinsa ya saka laptop dinsa da tardunsa sannan ya mika mata jikar. “Aje saman teble” Sai da ya aje sannan ta dauka suka. “Ni fa gida zanje fa naga garin hadari ma ya hadu” “Na sani a ka'idar kamfanin nan as you are my pa dole ni zan saukeki gida ko kuma direban kamfanin nan” Ya yi tunanin zata musa masa ne, sai dai shi ba ya yi ba ne dan kawai ya kara kusanci da ita, haka dokar kamfanin take. Tare suka fito duk mai son kallonsu sai idan sun bada baya sannan ake daga ido a kallesu domin sun san abunda Jibril ya fi tsana shine kallo. Ko da suka fito daga cikin kamfanin har an fara yayyafi motar da Jibril zai shiga kuma tana fake daidai bakin kamfanin, direban na ganinsa ya bude masa gidan baya da sauri yana kara masa umbrella, shi kuma sai ya zagaya ta wacan bangaren ya budewa Nawwara dan baya son ta shiga gaba, abunda ya bawa direban mamaki, ba tare da tunani komai ba ta shiga ta zauna, sai ya maida kofar ya rufe sannan ya zagayo ya shiga direban ya rufe masa, sai ta dora akwatin a tsakiyarsu ta maida hankalinta gurin gilashin motar tana kallon yadda ruwan sama ya soma sauka da karfi. “Guiwa locos” Ya fada yana kallonta, sai direban ya fisgi motar kamar ba ruwa sama ake ba, har aka shiga cikin unguwarsu bata juyo ta kalli inda Jibril yake ba, shi kuma idonsa na kanta, a hankali ya kai hannu zai taba hamnunta sai a ya yi dai dai da juyowarta tana fadawa direban inda zai aje ta. Hakan yasa shi saurin janye hannunsa ya danke ya maida kallonsa gurin gidajen da suke unguwar da yadda mutanen suka fake saboda ruwa. “Ya isa” Direban na tsayawa ta bude motar zata fita sai ya yi karaf ya ce “Akwai ruwa sosai ki dan jira a rage” “A'a” “Tahir kara mata lema” “A'a” Haka ta bude motar ta saka kafafunta cikin cabon da ke gurin tana tafiya ruwa na dukanta, sai da ya daina hangota sannan ya bude motar ya fita ya zagayo gefen da ta fito yasa hannunsa ya kwashi kasar da ta taka wacce ta fitar da sawon kafarta ya danke a hannunsa sannan ya koma cikin motar. “Gida” Kai tsaye direban ya nufi Sama road da shi, a hanyar ta tafiya ce ya fiddo wayarsa ya jira Rabi. “Zan aiko miki da kudi duk abunda ya kamata ki siye, sai ki ka a addiren da zan turo miki yanzu amman sai kin tambaya saboda ban ga ainahin gidan ba” Daga haka ya kashe wayar, har suka isa kasar na jinke a hannunsa ji yake kamar Nawwara ce ya rike, suna isa ya fita motar direban na tara masa lemar ya daga masa hannu alamar ya bari. Falonsa ya shiga da hannu daya ya cire kayan jikinsa faffadan kirjinsa ya bayyana muscle din jikinsa duk suka fito real namiji, sai ga karensa ya zo da gudu yana kada masa bindi, shi kuma be kula shi ba ya nufi wata kofar ya bude ya shiga harabar gidan dake can ciki, kwantawa ya yi saman tile din ya shafa kasar a kirjinsa ya ware hannayensa ya lumshe ido ruwan saman na dukansa. NAWWARA POV. Sai da na tabbatar ba zasu hango ni sannan na hada da gudu ina ta tunanin subul da bakan da na yi, da yanzu ya gane ya zanyi kenan? Gaskiya ina da yauta sosai ni mi ya kaini wannan maganar ma. Kamin na isa gida komai nawa ya jike saboda ruwan da ake sosai. Inna ma ta yi mamaki ganina cikin ruwa, a bakin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119