Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

neman kuɗi a gidanmu, ina ɗagowa ɗayan ya dalla min fitila a ido gashi ba shiri na sake rumtse ido. Ɗan abunda Inna ta san tana da shi na canji taje ta ɗauko ta kawo musu jikinta sai rawa yake tana faɗin “Shikenan na ke dashi a gidan nan Wallahi ba muda komai mu talakawa ne” “Kina da ɗan kunnen zinari ko azurfa?” “Wallahi bamu da shi” Ta bashi amsa ciki kuka mai cike da tsoro. Ban sake jin sun ce komai ba sai kawai na jin nayi suna da bincikar kayan da ke ɗakin wasu kuma suka nufi ɗakinmu wacan dake waje suna bincika, hakan ya bani damar buɗe idona a karo na biyu na kalli mutun huɗu da suke ɗakin suna mana bincike, daga ganinsu manyan ɓarayi ne domin ɗauke suƙe da manyan bindigogi fuskarsu sanye da fuska irin ta manyan ƴan fashin nan dukansu danye suke da baƙar riga da jean banƙi. Mun ga ikon Allah a wannan ranar domin komai sai da suka bincike, sam basu yarda bamu da komai ba, har tufafinmu sai da suka bincika suka tsince masu kyau, ragowar shinkafar da ta rage mana mana dafawa har da ita suka haɗa, wani abun ɗaure kai har da tukunyar da muke dafa abincin sannan suka ce duk mu rufe idonmu kuma mu kwanta, sannan suka fice suna cewa duk wanda ya ɗago sai sun halbeshi. Ni dai ba buɗe ido ba ko motsi ban sake yi ba har na kusan minti talati saboda kawai tsoro. A daren babu wanda ya sake runtsawa daga ni har Inna da Sakina, Jamila da Noor ne kawai suka yi bachi, Noor ma sai da na rumgumeshi. Abu ɗaya ne ya tsaya min a rai har garin Allah ya waye, miyasa basu shiga gidan manyan masu kuɗi ba sai gidanmu? Beside waɗanne irin ɓarayi ne ma da zasu ɗauki tsofin sutura da ragowar shinkafa da ƴan canjin da basu kai dubu biyu ba da sunan sata da alama mu fa manyan ɓarayi ne ba ƙananan ba. ‘Turosu aka yi’ Shine abunda zuciyata take ta yawan nanata min, sai dai kuma waya turo su? Washe gari mutane suka yi ta shigowa suna mana jaje tare da fatar allah ya tsare gaba ciki har da ƴan babban gida, sai dai wannan besa ɗayansu ya yi tunanin cewa mu koma can ba, duk kuwa da kasancewar rayuwarmu tana cikin hatsari saboda suna ganin idan muka koma zama tare da su lalurar mu ce zata hau kansu, kai tirrr da wasu ƴan'uwa! Da yamma Jidda ta zo ita da mamanta suna jajanta mana take labarta min abunda ake faɗi a unguwa, wai gurin dai suka zo har wasu na cewa ba zasu rasa min fyaɗe ba sai dai ba zan faɗa ba, maganar ta ɓata min rai daman nasan dole mutane su zargi haka ganin bamu da Komai kuma ace sun zo gidanmu. Baba Sulaiman ne ya kira mai gyara ya gyara mana tsohon ganbun na ƙofar gida da mutane suƙa ɓalle suka shigo. Tun da yamma muka bar gidan saboda ƴan'uwan Inna da suka sha kai akan sai dai mu dawo can da zama, ranar a tudun wada muka kwana gangaren tallatu sayin salamatu mai tuwo. Sun nuna mana mana kulawa sosai aka wuni ana firar ta nan na fahimcin Inna ma ta gano turosu aka yi, sai dai ita ta allaƙa abun ne ga Mustapha har take min faɗan wai na lallaɓa mu rabu lafiya da shi. Bayan sallah isha'i Bilal ya kirani na kwatanta masa inda nake, ko minti arba'in ba a ƙara ba sai gashi ya iso tudun wada, na fito titi na shigo da shi cikin lungun na mu. Gaisawace first abunda muka fara yi sai yasa na kira masa Inna ya gaisheta tare da yi mata jaje sannan ya ce an gidansu suna gaisheta. Bayan Inna ta shige ya dawo kaina sai bugun cikina yake yana ta son ya ji idan sun min wani na san wannan ba zai rasa nasaba da maganganun mutane da yake ji ba. “Kaima ka yarda da abunda mutane duke faɗa kenan” Ajiyar zuciya ya sauke ya gyara tsayuwarsa ya ce. “Yarda ta da rashin yardata duka suna gurinki, Wallahi komai kika faɗa min zan yarda da shi Nawancy” “Idan har ka yarda da ni toh ka yarda da duk abunda zan faɗa maka, Wallahi basu min komai ba ko hannuna basu riƙa ba, babu wanda suka taɓa a gidanmu” Sanyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke tare da jinginawa jikin iccen tarbejiya dake ƙofar gidan yana hamdala. “Allah na gode maka, Wallahi Nawancy da sun taɓa ki ban san yadda zan yi ba ban san iya halin da zan shigaba” “Da ba zaka iya aurena ba ko?” Hakan yasa shi ɗagowa daga jinginen da yake da sauri yana kallona fuskarsa da ɗauke da murmushi. “Nawancyta da gaske kike maganar nan da kika yi?” Ya tambaya yana matsowa kusa da ni kamar zai haɗa numfashinsa da nawa, hanzarin matsawa baya nake sai ya yi caraf ya cafke min hannun yana cigaba da matsosa kusa da ni. “Kin san waye ni babu abunda zan miki, kawai ina son na tabbatar ne, Wallahi Nawancy i'm ever ready to marry you dan Allah ki taimaka min” “Mutane fa zasu gani” Na faɗa a tsawalle ina kawar da fuskata, sai na yi sa'a ya sake ni, ina ganin hakan na juya da gudu na shige gida. Babu irin kiran da be min ba ta waya amman na ƙi ɗagawa har ya gaji ya tafiyarsa. Kwanan mu biyu a can muka dawo gida saboda tsallawa da muka yi saboda gidan gidan taro ne babu sakewa sosai, ga yaran gidan basa da ragowa a gaban idona suke buge Noor ba damar nayi magana ace na yi rashin ta ido su kuma ba zasu iya yi ma yaransu magana ba. Ranar da muka dawo ma mutane sun ta zuwa yi mana jaje mutanen da basu samu zuwa mana washe garin da abun ya faru ba, saƙon kamfani kan kamar ƙa'ida ko da muka dawo mun tarar da wasiƙa biyu wacce aka kawo yau ita ce ta uku ban da ta waya da nake ta karɓa ko wace safiya da kuma yammaci. Bayan na gama gyare-gyaren gida na shinfida tabarma na zauna tsakar gida ina ta nazarin abubuwan rayuwa ciki har da wannan abun da ya same mu, da kuma maganar ƴan sanda da suka yi mana izgilanci amman shiru har yau babu dpo babu labarinsa, ga kuma Jibril da ya sakoni a gaba yanzu. Wai shi Jibril me yake nufi ne ya yi nadama ko kuma so yake na koma aiki ƙarƙashinsa ta yadda zai sake gallazamin ya ɗauka kamar da ne? “Kut” A fili na yi ƙwafa, kana na ɗaga kaina dake ƙasa na kalli Inna wacce ta fito daga ɗaki tana maganar aikina. “Ni fa wannan lamarin har tsoro yake bani Nawwara, ban taɓa ganin wanda aka matsawa ya koma aiki kamar ki ba, anya babu wani abu?” Na yi dariyar da ni ƙaɗai nasan abunda yake nan. “Babu komai Wallahi kawai dai kin san abu idan aka ce maka da turawa ne, shiyasa” “Amman ke miyasa kika tsaya kai da fata akan ba zaki koma ba, nifa ina

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});