Chapter 107
Chapter 107
yan'uwanka Wallahi ina son ka, Bilal sauran fa sati biyu da kwana uku ayi auren nan dan Allah karka janye, kuma ko da ka fasa aurena ba zan taba auren Jibril ba, igiyar aure ba zata sake shiga tsakani na da Jibril ba” “Idan har baki auri Jibril ba Nawwara to son da kike min na karya ne...!” Ya fada a tsawace sannan ya share hawayensa ya yi tafiyarsa abunsa ya bar nan ina aikin kuka. Da kuka na shigo gida ina labartawa Inna abunda Bilal ya yi min sai tasa salati tana mamaki karfi hali irin nasa. Misalin tara da rabi Jibril ya kirani a waya wai gashi nan kofar gida ya siyowa Noor abu, a lokacin idanuwa sun kumbura kaina kuma yana mugun ciwo saboda kukan da nayi, nasan ba dan ni ya zo ba, amman ina da bukatar magana da shi saboda abunda ya faru tsakanina da Bilal hakan yasa na fito a lokacin yana tsaye shi da Noor yana bare masa ayaba. “Noor shiga gida” Na fada cikin muryata dake nuna na yi kuka har na gaji, ba musu Noor ya taka a hankali ya shigo cikin gida, ni kuma na kalli Jibril na ce “Rokon Bilal ka yi ka ce karya aureni ko?” “Miya kawo wannan maganar kuma?” “Ban sani ba, duk abunda ka yi be isheka ba sai ka saka Bilal a gaba ka rokeshi” “Wallahi ban rokeshi ba Nawwara, ni dai na masa magana ne akan ya rike min Noor da amana a matsayinsa na wanda zai aureki kuma na nemi yafiyarsa akan abunda ya faru daga karshe kuma na ce zan maidashi aikinsa ya ce min baya so yayi applying wani gurin sai dai idan wani abun ya fada miki daban wanda ba wannan ba” Na dafe kaina ina kuka. “Ki yi Hakuri Nawwara ban san haka zai bata miki rai ba da ban yi ba, nasan komai nayi a gurinki bana gwaninta” Ya fada da muryarsa mai nuna tsantsan nadamarsa. Kasa ce masa komai na yi sai ya juyo na dawo cikin gida cike da zazzafan zazzabi. MUSTAPHA POV. Har yau har gobe son Nawwara na nan cikin zuciyarsa, sai dai ba kamar da ba, yana son ya auri Jidda ne kawai saboda Iayayen sun ki yarda da Nawwara kuma yana jin Jidda zata maye masa gurbin Nawwara ko ba komai hakan zai kara wanke shi a idon Nawwara ta yarda zata yarda ya canja har abada, kuma yasan hakan zai kara kusancinsa gareta, a tunaninsa idan ya auri Jidda hakan zai yi ma Nawwara zafi kasancewar aminiyarta ce, kuma yana yawan ayyanawa a ransa cewar ko Nawwara tana kasa giɗa sai ya aureta amana dai ko da ta tsufa ne dan shi har gobe be cire rai daga aurenta ba. Momynsa ta yaba da Jidda ganin ita budurwa ce kuma ba a mata irin shaidar da ake yi ma Nawwara cewar ta haifi shege, mahaifinsa ma ya yaba da ita duk kuwa da kasancesar ba ita ya so ya aura ba, amman ganin ita ce zabinsa a dole ya amince da ita. Ba zai ce baya son Jidda ba iya abunda ya sani yafi son Nawwara da Jidda sau dubu ma ba dari ba, irin soyayyar da Jidda ke nuna masa ne ma yasa yanzu ya maida hankali sosai a gurinta har manyan suka shigo cikin, duk da kasancewar ba a saka ranar auren ba iyayensa sunje sunga iyayen Jidda kuma an tsaida magana akan cewar satin sama za a yi musu engaged. Duk irin shakuwa da so da kauna da ya shiga tsakaminsu har yau Jidda bata taba labarta Nawwara komai ba, ba dan kuma tana son boye mata din ba, sai dan tana nuna kamar ba zata kalli abun ta fuskar daya dace ba, tana ganin kamar Nawwara zata zargeta cin amanarta duk kuwa da kasancesar ta san cewar Nawwara bata son Mustapha amman bata san ta wace fuskar zata kalli alakarsu ba. [11/17, 12:17 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣7⃣ JIBRIL POV. Cike da bacin rai ya isa gida, abunda ya kasa ganewa miyasa Nawwara ta kasa sakewa da shi ne miyasa abu kadan zata rika ganin laifinsa, sai yaushe zata fahimci irin son da yake mata? Yaushe zata gane duk wani kalami marar dadi daga gareta yana taba masa zuciya, har sai yaushe Nawwara zata fara sanin ciwonsa? “O.... Ya Allah” Ya jefar da keys dinsa ya fadi zaune saman kujera yana sauke ajiyar zuciya. Can Bilal ya fado masa a rai sai ya maida laifin a kansa daman baya son ganin laifin Nawwara, yana da bukatar jin ta bakinsa da haka dole ne ya kirashi, wayarsa dake aljihu ya ciro ya nemo number Bilal ya aika masa da kira, ta dade tana ringing kamin ya dauka. “Hello” “Bilal a Maganganun da muka yi a akwai wata magana dana fada maka wacce bata kamata ba ne?” “Babu” “Dan me zaka je ka samu Nawwara ka fada mata mun yi magana? Ba dan kowa ya sani yasa na kiraka ba sai dan ganin da na yi hakan ya dace” “Nima dacewar na gani shiyasa na aikata abunda na aikata, na fada na fasa aurenta ne kuma gobe zan tura a karbo min kayan aurena da na kai gidansu shine kawai abunda ya tada mata hankali take ganin laifin” Jibril yay saurin mikewa tsaye, maganar ta zo masa a baibai ya fasa aurenta as how shi ba ko dazun da Nawwara take ta kuka tana masa bala'i be tsaya ya tantance takamaimain dalilin da yasa ta haka ba, kawai abunda ya fi ji maganar sa da Bilal da yayi kuma ta ji. “Ban fahimce ka ba?” “Na fasa aurenta na ce, hakan yasa tayi tunanin ko kaine ka yi min wani abu sai na fada mata haduwarmu” “Am amman miyasa ka fassa aurenta?” “Saboda mahaifiyata bata son auren” Yana fadar hakan ya kashe wayar be jira ya kara jin abunda Jibril zai ce ba. Farinciki ne da bakinciki suka zo masa a lokaci daya. Ya fasa aurenta yasa shi farinciki but what if shine dalilin fasa auren? Hakan zai sa Nawwara ta kara tsanarshi, bayan haka yasan Bilal yana son Nawwara idan shine yake kokarin aurenta kuma sai wani ya kwace masa ita ya zai ji? “Amman kuma ai mahaifiyarsa yace da Bilal yana da niyar fasa auren Nawwara saboda da da tuni yayi, ina tunanin abunda ya faru ne yasa mahaifiyarsa ta hana ya aureta” Ya furta a fili sai ya fadi zaune saman sofa ya lumshe ido. “Wow da ace zan ganki matar nan da na miki kyauta mai tsoka” Can kuma ya bude ido. “I hope you're not fooling me, no he's not ai da Nawwara ba zata yi kuka ba har tana zargina” Shi kadai yake ta maganarsa ransa fari fal ba zaka ce shine ya dawo gidan da bacin rai ba. Mikewa ya yi tsaye yana ji a ransa cewar addu'arsu ce Allah ya amsa kuma gana ganin he deserved happiness again tun da rayuwarsa ba mai tsawo ba ce. Wayarsa ce dake kan sofa ta yi ringing sai ya juyo da sauri. “Nawwara” Ya furta gabansa har bugawa yake da karfi, yana daukar wayar ya ga number Abbah lumshe ido
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119