Chapter 95
Chapter 95
ba. Mustapha ya kamata ka yi tunani, ni da kai ba daya ba ne, ballanta wani abun ya shiga tsakanin ni da kai, yar uwata ka yi ma fyade taya kuma ni zan aureka? Zuciyarka ta daina yaudararka abunda ba zai taba tabbatuwa a gareka ba, ka daina hangen abunda ba naka ba, Ina tunanin mutuwar Habiba ta canja mana rayuwa dukanmu, ta zamo silar shiriyarka, shin miyasa ba zaka tsayardar tunaninka guri daya ba ka yi abunda zai fiddaka? Duk yadda zaka so ni aikin banza ne, saboda komai ya riga ya lalace, a zan boye maka Mustapha soyayyarka ba zata taba samun gurbi a zuciyata ba ko da kadan ne, ka daina wahalar da rayuwarka akaina, ka yarda kaddara ce a haka sai kaga Allah ya kawo maka mafi alherinta” “Thank you Nawwara na gode da kika fada min gaskiya, har gobe ina alfari kuma zan kasance a cikin alfari da son ki har abada, domin son ki ya canja min rayuwa, ya sa na zama kalar da ban taba tsammanin zama ba” Ya fada idanuwansa na cika da kwalla. “Ina maka fata ta gari Mustapha, domin ni Bilal zan aura kai ma ina maka fatar samun matar da zata so ka sosai kuma iyayenka su so ta tadda zaka ji dadin zama da ita” “Thank you but ina son ki taya ni da addu'a domin abun ba sauki” Ya fada yana murmushin karfin hali tare da share hawayen da suka zubo masa. “Zan taya ka, ina maka fatar alheri” Ya dade a tsaye yana kallonta yadda zai yi rayuwa babu ita yake hange, ya san gaskiya ta fada masa shi kanshi yana jin kamar ba zata aureshi ba, sai dai a ganinsa idan har bata aureshi ba ba zai taba gamsuwa cewar ta yafe masa ba, but kalaman da tayi masa a yanzu yasa shi canja tunaninsa kuma ya samu gansuwa a ransa cewar Nawwara ta yafe masa har zuciyarta, ya riga yasan matukar yana son ya shirya da iyayensa dole ya rabu da ita, duk da yana jin a yanzu ta zama wani bangare na jikinsa. Kamar marar lafiya haka ya dawo gida nan da nan sai zazzabi ya rufe sai dai be bari mahaifiyarsa ta sani ba. [11/8, 9:40 PM] CANDY_♥️🖤: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣2⃣ SIX MONTHS LATER... Rayuwar da ban taba tsammanin zan iya yinta ba ita na ke a yanzu, ni kaina ina canjin da na yi a jikina da kuma ruhina, na zama RAI BIYU a gurin mutum biyu Noor da Jibril, na yi fadi tashin rayuwa kamin na kawo yanzu, na yaki zuciyata kuma na yi nasara akan kudirina. Komai ya canja a yanzu wa zai yarda da ni idan na ce ina rayuwa da Jibril a matsayin kanwa kuma abokiya, ni kaina na kan yi dariyar kaina kamin mamaki ya biyo baya, na zauna a matakin da ban taba tsammanin zan zauna ba, na shiga na fita na gyara rayuwar da na fi tsana a duniya abunda ko a mafarki ban taba tsammanin afkuwarsa ba, a yanzu Jibril ba shi wani madubi ko kuma tsarin rayuwa sai nawa, dukan wani abu daya shafi kamfaninsa da rayuwarsa ko kuma ta Noor da ni yake shawara kamin ya aiwatar da shi, hakan yasa kara tsanar da Siraj ya ke min har bayan son ganin sai dole, gashi case din da muke a kotu ashe yayarsa ce da ke aure nan domin a asalinsu su yan kaduna ne, shi kansa be taba sani ba sai da muka yi zaman kotu na hudu aka je da shi muka hadu, akwai nasara sosai a shariyar ta mu kasancewar Dpo ya tsaya kai da fata wajen ganin an yi mana adalci kuma an bi maka hakkin mahaifinmu, gaskiya na yaba da irin kokarin da dpo yake mana hakan ya kara tabbatar min mana cewar ba duka yan sanda marasa na na gari ba, domin a cikin bata garin ana samun na gari a cikin na garin kuma ake samun bata gari, Inna ma ta yaba da kokarin shi duk da ita tafi maida hankalin akan cewar wai so na ke, ni kan ina ganin kamar dai yana yi dan Allah kawai domin ni ai yasan an samin rana, duk da wani lokacin haka kawai xai kirani a waya ya ce fira yake son muyi ko ya ce yana son jin muryata, sai dai duk wannan firar da muke a waya Bilal be sani ba da sai ya kusa hadiye zuciya saboda mugun kishina da yake ko da yake na lura kamar ya fi kishina akan abunda ya shafi bangaren Jibril, kamar yadda shi ma Jibril yake nuna min kinshinsa na banza a duk lokacin da na ambaci Bilal a gabansa ko kuma na yi waya da shi, ni kuma na kanyi hakan ne saboda ya daina wahalar da kansa yana kusa kansa gareni domin na dade da zama matar wani. Na yi nasarar shiga na kanannade duk wata hanya da zata sa Siraj ya samu wani abun a karkashin Jibril, idan zuwa wani aikin ne ko taro ni kaina na ke cilasta Jibril zuwa, kuma na sa ya karbe komai nasa da yake hannun Siraj duk da be so haka ba, har ta kai ta kawo idan ban ga dama ba Siraj ba zai iya ganin Jibril ba indai a office ne, da fari Jibril da shi kansa Siraj din sun zarge ni da shiga tsakaninsu na neman rabasu, sai dai nasarorin da Jibril ya yi a cikin watan nan shida ba tare da Siraj ba yasa na fahimci shi kadai ma zai iya ba sai tare da wani, ko da wasa ban taba fadawa Jibril cewar Siraj yana masa Zagon kasa ba, sai dai na kan yi kokarin nuna masa haka ta hanyar wasu abubuwan da Siraj yake yi, tare da Rabi muke komai ita take sanar da ni duk wani kudiri na Siraj ni kuma sai na yi kokarin Jibril aikatawa, Jibril bw taba yarda da ni sosai ba kamar lokacin da na daukeshi muka je bypass da kansa ya ga kamfanin da Siraj yake ginawa wanda be taba fada masa ba, hakan yasa shi ma na ya fara ja baya da shi har suka soma samun sabani saboda rashin fahimta da ta shiga tsakaninsu Jibril yana ganin be kamata ace Siraj ya boye masa abu mai muhimmanci kamar haka ba, shi kuma Siraj yana ganin Jibril ya dauki amana ya bani har ina shiga tsakaninsu. Jibril ya sake shiga rayuwata a karo na biyu, na sake jiki da shi irin sakewar da ban taba tsammanin zan iya yinta ba, ya canjawa Noor da Jamila makaranta daga makarantar gwanati zuwa Imam international school, da school bus ake kawo su kuma a dauke su da safe, shakuwar data shiga tsakanin Noor da Jibril a yanzu har mamaki take bani lallai na yarda da aka ce yara sun fi sabawa da iyayensu maza. Sakina kuma ya maida Khalifa International School wace ke can kusa da Polytechnic bypass, dukan wani abu da za'a ci a gidan daga aljihun Jibril yake zuwa, idan na yi magana yace dansa yake yi ma, ni kuma na kan bashi damar hakan ne saboda nima na samu damar shiga cikin tasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119