Chapter 43
Chapter 43
ina ganin ta shigo rayuwata ne a lokacin da be kamata ta shigo ba. Dan haka karka sake faɗin wata mummunar kalma akan Nawwara, na zan iya tukararta kai tsaye ta yafe min ba, amman idan muna zama a guri ɗaya ita da kanta zata fahimci halin da nake ciki ta yafe min, i need to work with her, i need to be close to her” Yana kaiwa nan ya share hawayensa ya nufi Bedroom ɗinsa, ya bar Siraj a tsaye yana jinjina lamarin. *** *** *** Kukana ya yanke tun kan na iso gida, sai dai hakan be hana mahaifiyata fahimtar ina cikin damuwa ba, ga shi na dawo da wuri ban daɗe ba. “Lafiya kika dawo yanzu?” “Lafiya ƙalau kawai faɗa muka yi da wani na mareshi sai suka ce na dawo gida” “Faɗa kuma? Da namiji miya haɗa ku” “Na goge gurin ne sai yazo yana min masifa har da riƙa hannuna na ni kuma na mareshi” “Tau kin kyauta kin yi abun a yaba miki kowa ya yi miki ba dai dai ki riƙa hannu kina marensa kinji Allah ya miki albarka” Na san baƙar magana ta yi min wacce ke nuna bata jidaɗin abunda na yi ba. “Amman Inna ni ce nai gaskiyafa” “Idan kina da gaskiya sai ki ɗaga hannu ki mareshi wata ƙila ma ya girmeki, duk wani hali da ba naki ba Nawwara yanzu kin ɗauka kin ratawa kanki, wannan zabin zuciyar na Habiba ke aka saukewa shi? Ita tafi sai masifar ta dawo kanki, wannan ba halinki ba ne Nawwara, kuma ba tarbiyar gidan nan ba ce” “Yi haƙuri Inna na miki alƙwari ba zan sake ba” Na faɗa idona cike da ƙwalla, domin ni kaɗai na san halin da nake ciki, ita kanta da tasan wanda na mara da bata min wannan masifar ba. Ɗakinmu na wuce na ci kuka sai da na gode Allah sannan na fito. Bayan sallah magariba, Bilal ya kirani a waya ya sanar min yana waje, na ɓata lokaci kamin na fita saboda na san maganar da zai min ba zata wuce ta abunda ya faru yau ba, sallama na yi masa amman be amsa min ba sai ya jefo min tambaya. “Ance min kin kirashi da azzalumi, shi kuma ya baki haƙuri har ya yi iƙirarin kiranki da matarsa, shine Baban Noor ko Nawancy” Na gyaɗa masa kai “Shine” “Daman kin san nan kamfaninsa ne kike aiki?” “Ban sani ba sai yau” Wani dogon numfashi yaja ya sauke. “Na yi farinciki da ya gane kirkurensa, ko ba komai Noor zai san mahaifinsa na gaskiya” Na yi saurin girgiza masa kai idanuwa cike da ƙwalla. “Ba zai sani ba Bilal ba zan iya bashi Noor ba, be san zafin ɗana ba, be san yadda na yi na haifi ɗana ba, be san wahalar da na sha kamin da bayan na haifi ɗana ba, ko sau ɗaya ƴan'uwansa ba su taɓa biyo sawunna su duba lafiyar ɗana ba, Noor be cancanci Uba irin Jibril ba, Dan Allah dan girman Allah karka faɗa masa ina da ɗa zai iya raba ni da ɗana Bilal” “Ba zan faɗa masa ba, amman dole wata rana zai gano, lokaci yana zuwa Nawancy zaki koma ke da shi kamar ba ayi ba” Ya faɗa muryarsa na nuna tsantsar damuwar dake cikin ransa. “Ba zamu koma ba Bilal, babu wanda zuciyata take so take ganin ƙimarsa kamar kai, kai kaɗai ne mutun da zan tuna na yi murmushi, Wallahi kai kaɗai zuciyata take ƙaunara Bilal” “Ina jin tsoron faruwar wani abu Nawancy” “Babu wani abun da zai faru, sai idan ba son aurena kake ba, ba son ƙwarai kake min ba, daman can zaka biye abunda mutane suke cewa ka gujeni” “Ba zan taɓa gudunki ba Nawancy, ina ƙaunarki sosai” Ya faɗa yana ƙoƙarin kai hannu ya share min hawayena sai na yi saurin saka nawa hannun na share, sai kawai ya saka min dariya. “Na jidaɗin wannan abun ko ba komai kin nuna min yadda kika so na” Ni kuma sai na cire talakmena na gwaɗa masa a hannu har sai da ya yi ƙara. “Ka daina taɓa ni da wannan hannun” “Nima ba son raina yake taɓa ki ba, kawai dai shi ɗin ne ya damu sai ya taɓa ki, amman ranar da zai taɓa halalinsa zan ga bakin da ya isa ya hana shi” Na zaro ido ina mamakin kalaminsa, sai ya kannemin ido ɗaya yana murmushi. Mum yi firar da ta ɗebe min kewa fira irin ta masoya firar da ta gusar min da duk wani tunani da damuwa har sai da na dawo cikin gida. Bayan na yi sallah isha'i na ci abincin dare kaɗan saboda kar Inna ta gano abunda yake damuna. Dakimmu na dawo da zimmar bachi amman sai na kasa rayuwar da na yi a abaya ta dawo min... FLASH BACK....... _______________________________________ I can't wait na ji tarihin Nawwara zamanta da Jibril.. 💃 #RB #TEAM MUSTAPHA #TEAM JIBRIL #TEAM BILAL *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣8⃣ Khadija shine sunan da mahaifina ya saka min, sai ya yi min alkunya da Nawwara, duk da kasancewar ba ni ce ta farko ba, ƴaƴƴuna hudu maza duk basu tsayaba sai ni da nazo a ta biyar kuma mace. Bayan ni sai da mahaifiyata ta shekara biyar sannan ta haifi Habiba, a lokacin Mahaifina yana ta faɗi tashin rayuwa na nema mana abunda zamu ci. Ba zan kira kaina da kyakkaywa ba, sai nasan ni ba mummuna ba ce, abunda kawai zan iya shaidar kaina da shi shine na ɗauko fari da kuma dogon hancin mahaifiyata kasancewarta fulani, gashin kan ba a magana na girata ma askewa nake balle kuma na gadon bayana dake ƙayatarda mai kallo. Siye da siyarwar na fatoci, Sana'ar iyaye da kakkanina ce sana'ar wacce mahaifina ya buɗe ido ya samu kansa a cikinta har muma muka zo muka tarar anayi, kowa ya tashi a gidan ana buɗa masa shago ko kuma a haɗashi da wanda zai riƙa masa ja gaba kan sana'ar har ya kafa tashi. Kusan zan iya cewa sana'ar bata karɓi mahaifinmu ba, tun lokacin da ya fara ba riba ba kuɗi, wani lokacin har kuɗin wani sai sun shiga ciki su ƙi fita, duk lokacin da mahaifinmu ya siyo fata da zimmar saidawa sai karaya ta sameshi wacce zata zama silar da ba zai iya maida kuɗin ba, yayyunsa da Yakumbo da kuma Hajiya Lamtana Allah ya jiƙanta sai suka ɗauki karan tsana suka ɗora ma Ramatu wato mahaifita, a ganinsu ita ce bata da ƙashin arziki, sukan ce wai can kamin ya aureta a lokacin da yake saurayinsa yana sa'arsa lafiya sai da ya aureta sannan komai yaso ya lalace. A lokacin ina ƙarama amman abun yana min zafi sosai saboda yana damun mahaifiya sosai, har na riƙa kallonsu a matsayin maƙiyanmu wanda har yau shine a zuciyata, domin a lokacin a gaban idonmu suna faɗa wai uwarmu mai farar ƙafa ce wanda hakan suke tunanin ba komai bane ko kuma mu bamu kula ba alhalin yana mana zafi sai dai bamu isa mu nuna ba kasancewar gidan taro ne, ko tari kayi sai anji, Babban gida irin gidan nan ne da kakanni suke siye sai iyaye da jikoki su
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119