Chapter 79
Chapter 79
son ta bayan shi, abu daya yake ce masa tuwo a kwarya a yanzu ba komai bane face rashin iya karatun kur'anen, haka zai dauko kur'anen ya rike but he can't read it ko baki be iya hadawa balle har ya tada ya karanta aya, and now he need to know his religion more than everything, yana son yasan abunda Allah ya ce da kuma wanda ya hana, zuciyarsa na raya masa idan har ya shiryu ya zama na kwarai Nawwara zata so shi, a duk lokacin da ya tuna da dansa yana asibiti sai ya ji kamar zai mutu saboda yana son naje ganinsa sai dai yasan Nawwara ba zata bari ba. Haka ya jera kwana uku be sake saka Noor a ido ba a duk lokacin da tunaninsa ya taso masa sai ya dauki cocaine din ya sha sannan ya samu sassauci. Misalin karfe biyu dare yana zaune saman carpet yana istigifari sai ga Abbah ya kirashi, da fari ya ji tsoro dan yasan Abbah be saba kiranshi a irin wannan lokacin ba, sai kuma daga baya wani tunanin ya zo masa na cewar wata kila Abbah zai masa fada ne akan rashin zuwa aiki da ya yi kwana biyu. “Hello” “Jibril kana lafiya?” “Lafiya kalau Abbah” “Ka tabbata?” “Lafiya ta kalau” “Allah ya tsare ka, kawai na yi wani mafarki ne marar kyau ina fatar babu komai ko? ” “Babu komai Abbah sai damuwa, Nawwara ta ki fahimta ta Abbah kuma akwai da a tsakaninmu” “Ni ma na samu wannan labarin lokacin da na je zan bawa iyalanta da kuma ita kanta hakuri akan abunda ka yi musu, sai dai ba samu ganin yaron ba” “Abbah da gaske? Yaushe ka zo?” “An kwana biyu, kawai dan ban fada maka ba ne” Abbah ya labarta masa komai daga zuwansa da kuma abubuwan da suka faru, Jibril ya ji dadi hakan ya tabbatar masa da mahaifinsa yana sonsa kuma yana tare da shi. “Abbah ka taimaka ka min izinin zuwa gidansu Nawwara Dan Allah” “Ka yi alkawarin ba zaka yi wani abu marar kyau ba?” “Taya mai neman hanyar gyara zai yi wani abu marar kyau? Wallahi Abbah ina son Nawwara sosai kamar zan hauka ce” “Amman da muka zaba maka ita ai cewa ka yi baka son ta” Ya yi shiru be ce komai ba, sai Abbah ya kara da “Kuma kasan sai dai ka yi hauka dan babu aure a tsakaninku ko? Kasan saki uku ka yi mata fa” Idanuwansa sun cika da kwalla. “Yanzu Abbah babu wani gyara da za a iya yi? Ba wata mafita?” “Babu zan kwanta sai da safe” Abbah ya kashe wayarsa, sai Jibril ya fara surutai “Dole akwai mafita Wallahi, dole a samu mafita No no no” Wannan tunanin ne ya hana shi bachi har garin Allah ya waye, tun da asuba ya shirya ya fita, kai tsaye asibitin ya nufa. Ya taki sa'a yau Nawwara ce kwana asibitin, ko da ya tura kofar dakin ya shiga zuciyarsa na bugawa dan ya yi tunanin zai samu Inna a ciki ne ko kuma ya tararda Nawwara a farke, sai ya tarar tana kwance bayan Noor saman gadon asibitin suna ta bachinsu a tare, karasawa ya yi kusa da su fuskarsa dauke da murmushi yana kallon iyalinsa. Wayarsa yasa ya dauke su hoto sannan ya cire jacket dinsa ya lulluba musu ya zauna saman kujerar da ke facing dinsu yana ta kallonsu cike da shauki. “Na bata komai, da yanzu muna nan a iyali daya” Kadan kadan yake maganar amman hakan be hana Noor farkawa daga guntun bachinsa ba, sosai da sosai yake kallon Jibril ganin wani babban mutum mai kama da shi, sai kuma ya unkura ya tashi zaune zai yi magana Jibril ya dora hannunsa saman bakinsa ya yi masa alama da ya yi shiru. “Shiiiiiiiiiiii” Sai ya mika masa hannu alamar ya zo, ba musu Noor ya mika masa nashi hannayen sai ya dauke shi ya zaunar saman jikinsa ya rumgume ya lumshe ido. Hawayen farinciki da bakinciki suka cika masa ido lokaci daya. “Waye kai kai likita ne?” Noor ya tambaya da muryarsa yar karama. Sai Jibril ya girgiza masa kai alamar a a ba tare da ya bude idon ba. Shi kuma sai ya sake tambaya cike da mamaki yana ta kallon fuskarsa. “Kai ne wanda Inna ta ce min zaka zo ka ganki? Kai ne Uncle din?” Ya gyada masa kai still be bude idon ba dan baya son Noor ya ga hawayensa, Nawwara kam bachi kawai take abinta bama san ana yi ba. NAWWARA POV. karar bude kofar da aka yi ne ya tasheni daga dogon bachin da na ke, sai turaren da na fi tsana a duniya ya yi marhaban sannan na kula da jacket din da aka lulluba min saman jiki. Inna na gani zaune tana jan karbi ba Noor a kusa da ni kamar yadda muka kwanta, saurin zabura na yi. “Ina Noor?” “Yana gurin Babansa” “Dauke sa ya yi? Miyasa kika bari ya shigo?” “Ke ya kamata na tambaya dan nan na shigo na sameshi” Na sauka saman gadon hankalina a tashe sai Inna ta rike hannuna. “Ba gudu zai yi da shi ba, sun fita waje ne su sha iska, ina tunanin ya canja Nawwara a nan ya durkusa yana ta ba ni hakuri, wannan abincin karyawar da kika gani daga kamfani yasa aka kawo” “Wallahi zai iya gudun min da da mugu ne” Na fita daga dakin hankalina a tashe, ina fitowa harabar asibitin sai na hango Noor saman motarsa zaune shi kuma na jikina jikin motar ya rumgume Noor. Karasa na yi ina masa fada. “Waya baka izinin fitar min da da?” Sai ya dago ya kalleni sai ya sauko da Noor da ko riga babu a jikinsa. “Ki yi hakuri na fita da shi ne ya sha iska” Daukar Noor na yi na koma da shi ciki, shi ko sai zuba min tambaya yake akan wannan Uncle din nasa da Inna take fada masa zai zo ya duba shi. A ranar duk wanda ya kawo mana ziyarar dubiya ya tararda Jibril a asibitin saboda nan ya wuni, duk wani tafiyar numfashin Noor yana kula shi hannun kuma maikaraya yana kula da shi sosai, na yi mamakin da Zinatu ta zo ganin Noor ko da yake ba abun mamaki ba ne duba da Jibril yana cikin asibitin, yau kan Bilal dake zuwa kullum duba Noor ya tarar da Jibril wanda hakan yasa shi kin sakewa sosai daman kwana biyu nan na rasa gane kansa, hakan be min dadi ba dan ban jidadin ganin da Bilal ya yi ma Jibril a asibitin ba, ni kuma na raka shi har gurin gate din asibitin sannan na dawo. A lokacin Jibril ne kawai cikin dakin Jibril ne kawai sai Noor suna rike da hannun juna, daman Inna waje ta koma da zama bata iya zama a cikin dakin matukar Jibril na ciki. Kamar jira yake na shigo sai ya mike tsaye ya nuna ni da yatsa fuskarasa a kumbure saboda bacin rai ya ce. “Kar Bilal ya sake zuwa duba min yaro wannan ya zama na farko kuma na karshe...” Kallonsa na ke sai ma na rasa abunda zan ce masa, daman
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119