Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 4⃣ Inna ta doso inda na ke a yayinda da juyo cikin gida hawaye na bin fuskata. “Nawwara lafiya?” Ban san ta ya zan faɗa mata ba, sai dai babu wata damar ɓoye mata dole na faɗa mata gaskiya. “Wai Baba aka kama, yana station ɗin ƴan sanda” “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” Ta faɗa tana dafe kanta fuskarta na bayyana tashin hankalin da ke zuciyarta. “Mi yayi musu?” “Nima ban sani ba, na tambaya ya ce idan na je can zan sani” “Mun shiga uku muna cikin wannan halin kuma wani za mu shiga” “Ina ganin sharar fage ne ga wata sabuwar rayuwa” Na faɗa ina hawaye. Bata kula zance ba ta shiga ɗaki ta ɗauko tsohon Hijabinta ta saka tana ce min. “Zan je na faɗawa Dahiru muje tare, ke kije ki faɗa a babban gida” Bata ko tsaya jiran abunda zan faɗa ba ta fita hankalinta a tashe. A take nima na saɓi mayafina, na ja ƙofar gidan na nufi babban gida wato gidan kakaninmu. Babban gida ne mai ginin ƙasa da laka irin gidan nan da ake a zamanin baya wanda a yanzu ake kira da family house, ba kasafai na ke son zuwa gidan ba saboda mutanen da ke ganin mutunci na da na ubana basa a raye a yanzu, wato kakanin na kenan waɗanda suka haifi ubana, sai dai ƙanen da ƴaƴansu da suke ganin kamar Baba yayi mana gata dan ya ware mu daban, duk laifin duniya da ganin kamar mu munfi kowa sai suka ɗauka suka ɗora mana har wasu na cewa wai dan Tsoho ba shi da rai ne tasa Baba yin haka. Alhalin ba haka ne kawai Baba baya son rigima ne da ƙaƙanan maganganu da yawan anyi an'ce kamar ya kashesu. Sashensu Yakumbo na fara shiga wato gwaggo Babana, tana ganin hawaye a fuskata tasan ba lafiya. “Tsohuwa Lafiya?” “Baba aka kama” “Kama kamar ya? Kamu na ƴan sanda ko mi?” A take ya zayyana mata komai ina hawaye. Miƙewa ta yi tsaye ta fita tsakar gida duk da jikin nata babu wani dogon ƙwari saboda tsufa. Kan ka ce kwabo har ƙofarta ta cika da ƴan cikin gida kowa na tambayar ba'asi, abunda na faɗa mata shi na faɗa musu, sai tasa aka kira ƙannen Babana wanɗanda basa nan a waya ta sanar musu. Ban baro gidan ba sai da aka kira sallah azahar kuma har lokacin Inna bata dawo ba. Sakina da Jamila kan suna tsakar gida zaune, Noor ne kawai yake sha'aninsa, ina shiga suka yo kaina da tambaya. “Anty ina kika je?” “Baban gida na je” “Me kika je yi, ina Inna?” Yara ne ƙanana a tunani be kamata na sanar su wannan maganar yanzu ba. “Na riga Inna fita ban san inda taje ba, ni na je gaishe su ne kawai” Noor ya zo ya riƙe min hannu. “Momy yunwa na ke ji, kunon da na sha ya ƙare” Hannu da ke cikin nasa na sunce na nufi ɗaki dan bana son yaga ƙwalla da suka cika min ido. Ɗan kuka na yi kaɗan a ɗakin domin idan na yi da yawa zai tona asirin abunda na ke ɓoyewa Sakina da Jamila ne, fito na yi waje na yi alwala na koma ɗakin na shinfiɗa ɗankwalina na yi sallah azahar, babu irin addu'ar da ban yi am Baba ba duk ya ke ban san halin da yake ciki ba ko kuma dalilin kama ɗin shi ɗin ba, na roƙar masa mafita da sauƙi ga Allah, tun a cikin sujudar ƙarshe har a cikin zaman tahiya zuwa addu'ar da ake bayan sallamewa. Ƙarfe biyu da kwata Habiba ta dawo gida cikin uniform ɗinta na makaranta. Tun da ta yi sallama na kasa amsa mata ta fahimci akwai matsala. Hijabi ne kawai ya zame mata dole ta cire ta nufo inda na ke zaune ta dafa ni. “Nawwara mi ya faru” Idan na ce zan ɓoye mata hawayena to zan yaudareta ne kawai, domin ta riga ta ga yadda hawayen ya ke sauƙowa daga idona, bakina kuma a gumɗe ina gintse kuka da ke son fito. “Ki faɗa min mana ina Inna?” Ta sake tambaya idonta na cika da ƙwalla. “Habiba ƴan sanda sun kama Baba, tun safe Inna ta je har yanzu bata dawo ba” Ta ɗora hannu saman kai. “Mun shiga uku? Mi yayi musu?” “Wallahi ni ma ban sani ba” A gurin ta zauna ta fara kuka kamar an yi mana mutuwa, daman Habiba bata da taurin zuciya irina, zan iya ɓoye kukana ko kuma bayyanawa a duk lokacin da nake buƙatar hakan amman Habiba bata iya wannan, a duk lokacin da abun kukan ya sameta a take zaka gane. Sakina da Jamila har da Noor suka shigo ɗakin a guje suna kallonta, nima kallonsu na ke hawaye na bin fuskata. Sallamar Inna da muka ji ne yasa muka ɗunguma gaba ɗaya muka fita waje, tana kallonmu sai ta fashe da kuka ta faɗi zaune. Daga ni har Habiba kasa tambaya mukayi kowa da abunda yake saƙawa a zuciyarsa, musamman ni da nake zargin ko sun kashe she ni. Jamila da Sakina ne suka ƙarasa inda take suna tambayarta. “Sata ake zargin mahaifinku yayi ta kimanin dubu ɗari biyu da saba'in” Tana faɗar haka ta ƙara fashewa da kuka, Habiba ta faɗi zaune irin jikinta ya mutu sosai, ni kuma na lumshe ido wasu zafafan hawaye suka zubo min. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 5⃣ Haƙiƙa mahaifina talaka ne, amman bana tunanin wannan talaucin zai saka Baba sata, sai idan wani tsautsayin ne ko ma zai sata ba zai saci kuɗi har naira dubu dari biyu da saba'in ba, tau ina zai kaisu? “Miya ɗauka har na dubu ɗari biyu saba'in?” Habiba ta yi tambayar da na ke da niyar yi ma Inna. “Dako ya je yi kasuwa, wacce yaje yi ma dakon wayoyinta da ɗankunenta na zinari ya ɓata, ta ce wayoyinta na dubu ɗari da ashirin ne, ɗankunen zinarinta kuma dubu ɗari da hansi” Sulalewa na yi ƙasa hawaye na min zuba, babu zancen da nake tunawa kamar maganar mu ta ɗazu da safe, yadda na ke nanata masa kar yaje dakon nan kamar na san abunda zai faru. “Babu irin roƙon da ba'ayi mata ba ta ce ita ba zata haƙura sai an biyata” Inna ta faɗa cikin kuka. Sai duk muka saka kuka har su Sakina da Jamila, daman Habiba bakinta a buɗe yake tana aikin kukan. “Ku daina mana kuka tun da ba mutuwa aka yi ba” Cewar Inna tana share hawayenta. Bayan Inna ta bar gurin na miƙe tsaye na koma cikin ɗakin na zauna ina aikin kuka. Haka muna yi sallah isha'i cikin zullumi da tunanin makomar Baba har ma da tamu gaba ɗaya, bayan an yi sallah isha'i ne maƙota suƙa riƙa shigowa suna mana jaje. Ban taɓa yarda tashin hankali na hana bachi ba sai a wannan karon ina ji ina gani bachi ya ƙaurace daga idona. Alwala na fara gabatarwa kamin sallar nafila, har aka kira sallah asuba ina zaune saman ɗankwalina ina tasbihi, bayan na gama na yi ma Baba addu'a sannan na gabatar da sallah asuba. Tun da dungu-dungun safiya muka ji an buga mana ƙofa, Habiba ce ya je

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});