Chapter 11
Chapter 11
halin da ake ciki, ita kan uffan bata iya ce musu ba, Bilal ya sallama a ƙofar gidan mu yana nemana. Cikin rashin kuzari na miƙe tsaye kasancewar Hijabin da na yi sallah da shi yana jikina ne. Jikine da ƙofa na same shi yana rumgume da hannayensa, fuskarsa ba yabo ba fallasa. Sallama na fara masa kamin na miƙa masa gaisuwa. “Lafiya Ƙalau Nawancy ya haƙuri?” Ya tambaya ba tare da ya kalleni ba, har lokacin idonsa na kallon wasu gidajen da ke fuskarta na mu. “Mun gode Allah” “Nawancy kawai ina son na ɗan miki wasu tunatarwa ne akan abunda ya faru-” Na tsaleshi tun kamin ma ya fara. “Dan Allah Bilal ka karka so ma idan ba kuka na kake son ya dawo sabo ba” Ya juyo ya kalleni ido cikin ido. “Na daina Nawancy” Yaja wani dogon numfashi ya sauke yayinda ni kuma na ke tare ƙwalla da suka cika min ido. “Am sorry ban zo nan dan saka ki kuka ba, daman na zo ne na faɗa miki aiki da nace miki za a ɗauka a gurin aikinmu an fara” “Yaushe?” “Tun lokacin da abubuwan nan suka soma faruwa, kawai ban miki magana ba ne saboda ina ganin kamar be dace ba, gobe ma za a rufe, daman kwana goma ya bada” “Da gaske? Amman suna ɗauka masu ssce?” “Yeah sai dai aikinsu goge-goge da kuma mopping sai aikin kai documents ko ɗaukowa, maza kuma shara da buɗe ƙofa” “Indai zasu ɗauke ni zan iya Bilal, ina ake applying?” “A can gurin mu zakije ki bada takardun idan sun duba sun ga ka cancanta zasu nemaka ta waya” “Ƙarfe nawa ake zuwa?” “Goma” “Allah ya kaimu zan zo” Ya ɗaga min, sai ya miƙa min nokia hannunsa. “Wannan ki saka layinki saboda kira suke ba zuwa ba, ara miki na yi ba kyauta ba” Na san ya ce haka ne dan kawai na karɓa, duk da nima bana da wata mafitar da da wuce na karɓa ɗin, kasancewar babu waya a hannuna ga shi kuma number Jidda da nake badawa wani lokacin yanzu ta siyar. “Aro” Na faɗa yayinda na ke miƙa hannuna na karɓa. Murmushi ya yi “Yes aro, da kin fara aiki ki siya min sabuwa,ko da yake albashinku mai yawa ba ne” “Nawa ne?” “12k” “Ba laifi Bilal indai zasu biya ƙarshen wata” “On 25 suke biya, baki da matsala da wannan” “Allah dai yasa na samu” “Zaki samu inshallah” “Na gode” Na faɗa cike da ƙosawa da kuma son ya tafi, ba kasafai nake son ana ganin ina tsayuwa da shi ba, saboda ƴan sa idon unguwa. Shi kansa ya lura da hakan sai yayi min sallama ya tafi ni kuma na dawo cikin gida. Bayan Sallah isha'i nake labarwatawa Inna maganar aikin har ma na nuna mata wayar da Bilal ya bani. “Allah ya bada sa'a” Kawai tace min ta jingina da gini tana jan carbi, wanda hakan san be min daɗi ba, Habiba ce kawai ta zo ta zauna kusa da ni tana tambayar yadda aikin yake. A cikin dare na ɗauko tsohon layina na saka a wayar da Bilal ya ba ni. Washe gari ta kama ranar alhamis, ranar na tashi da azumi, daman duk litanin da alhasmis na kan yi azumi wani lokaci, musamman yanzu da ya zama ba komai na ke ci ba idana ban yi azuminba zan wuni da yunwa ne kawai. Misalin bakwai na safe na ɗumama su Jamila tuwon shinkafar da na yi musu jiya miyar kuka, Inna kuma na dama mata kunu ita da Habiba saboda shi kaɗai suke iya sha ko da rana da dare kuma ruwan tea. Bayaɓ na gama na je yani wanka na shirya ciki wata farar atamfa na saka baƙin Hijabi sai kuma tsofi takalmi waɗanda suka kasance baƙaƙe sannan na sake dawowa ɗakin Inna na same ta har lokacin tana shan kunu. Jaƙar da muke ajiye kayan karatu na buɗe na ɗauki takarduna na makaranta na buɗe ina duba tare da tunatar da Habiba maganar zuwa makaranta. “Ya kamata ace kin je makaranta gobe ko kuma monday nan mai zuwa, yau kusan kwana nawa baki je ba, kuma jarabawa kuke fa, gashi rashin zuwanki ya haddasa har su Sakina sun daina zuwa” Ta turo baki. “Ni ba zan sake zuwa ba, karanta mo zai tsinana min, ko na yi karatu ba zan wuce babbar makaranta ba, kema da kike da ssce min kika amfana da shi” Murmushi na yi, nasan tana tunanin babu wanda zai iya ɗaukar ɗawainiyarta ne da har zata yi babbar makarantar gaba da secondry, tun da karatun ya zama sai da kuɗi. “Na miki alƙawari zan ɗauki nauyin karatun ki, ke dai ki dage ki cigaba da wannan ki kammala sai kije babbar makaranta” “Ta yaya?” Ta tambaya tana hararata irin bata yarda ɗin nan ba. “Wannan aikin idan na samu zan riƙa aje wani abu daga albashina saboda ke Habiba” “To Hajiya bari har ki samu” Ta faɗa tana ɗaukar Noor ta ɗora saman ƙafafunta. Ni kuma na yi murmushi na kalli Inna na ce “Ni zan ta fi Inna” Fillo ta ɗaga ta ɗauko ɗari biyu ta miƙa min. “Ki hau Napep, karki manta da nasihar da mahaifinki yake miki akan mutuncinki Nawwara” “In'sha Allahu” Na tashi cikin jiki ba ƙwari na fita. Yau kan sai da na yi nisa sosai sannan na samu Napep, kai tsaye na kwatanta masa inda zai kaini wato koko road. Nesa da Company ya sauke ni na bashi kuɗinsa, sannan na aikawa Bilal please call me kasancewar babu ko na flashing a wayar, sai ga shi ya kirani cikin ƴan mituna, na sanar masa ina kusa da gurin. “Ki ƙaraso mana gani nan fitowa” Bayan na amsa masa da okay na doshi company gaba sai dukan uku-uku yake, wata ƙila ko dan ban taɓa zuwa babban kamfani kamar wannan ba oho.. *ONE-ON-ONE LIMITLESS* _One of the Largest Metal Companies in the world_ A hankali na karanta, ina ƙara faɗaɗa ido ga kallon ƙofar gate ɗin company ma da ta kasancewa ƙatuwa. ‘Anya za su ɗauke ni aiki kuwa’ Na tambayi kaina ina kallon securities da ke bakin gate ɗin sanye da uniform kamar na ƴan police sai dai na su farar rigace sai baƙin wando. A ƴar ƙaramar ƙofar da ke gefen gate ɗin na hango Bilal ya fito sai sauri yake ya doso inda na ke. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣0⃣ Na ɗan faɗaɗa fuskata da murmushi kaɗan na kuma gyara tsuwata. Shi ko haƙoransa a watse har ya ƙaraso kusa da ni. “Miyasa baki shiga ciki?” “Waɗannan jibgin securities ai ba za su bar ni na wuce ba” “Haka zuciyarki ta nuna miki, ai su aikinsu tsaro ba hana mutane shiga ba, kin tsorata ne?” “Sosai ma” Sai kawai yasa min dariya har da tintsirawa. “Haba sai ka ce wacce bata zauna ƙasashen turawa ba, ai zaki saba da su ne, amman fa zan yi fama da kishi dan suna sakewa da mata sosai” “Kishi?” Na tambaya cike da mamakin kalaminsa, haka wani lokacin ya ke sakar min magana kamar mai suɓul da baka. Sai kawai ya shafa fuskarsa be bani amsa ba ya zuma hannayensa aljihu ya kama hanya. “Mu je”
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119