Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cikin unguwar” Bana da wata dabara ta da wuce na hau ɗin, babu tantanma idan har na zaɓi zuwa a ƙafa zan wahala sosai. Abun ka da mai nema sai kawai na gyara zane na na haye mashin kamar na yayana ko kuma na ce na Ubana. Bilal ba baƙona ba ne hakan yasa na sake da shi sosai muna fira har muka isa bakin ƙofar gidansu Zinatu. Na sauka ina masa godiya. “Am Nawancy na manta ban labarta miki wani abu ba, mun samu sabon shugaba a kamfaninmu kuma ya buƙaci sauye-sauye saboda yana da zafi sosai, kuma duk ya zubar da ma'aikatan gurin ya ce sabbi za a ɗauka, sai dai be faɗi rana ba, so ina fatar idan za a ɗauki wasu zaki yi applying” “Kai ka ce kai ma kun tsallake rijiya da baya” “Wallahi mun tsallake kan, domin mutumen akwai zafi sosai, gashi baya ganin kowa da mutuncin, ko dan yana kamfanin Mahaifinsa ban sani ba” “Ai fa ka ji to mu da ba wani zurfin ilmi mukayi an ya zai ɗauke mu kuwa, Bilal kafa san SSCE ne kawai da ni” “Abun sa'a ne Nawancy zaki iya shiga kuma ki yi sa'ar samu, ai kisan mataki mataki ne” “Naga Babban kamfani ne Bilal” Yayi wani abu da fuska yana matse hancin, irin yadda yake min a duk lokacin da zai zolayeni. “Trust me girl zaki samu babu tantama” Na yi murmushin da ya fitar da dimple ɗina, ina ƙara jan gyalena dan rufe jikina. “Ni zan wuce aiki kar na yi latti ya kore, dan ya faɗa mana idan ka ƙara minti ɗaya zai koreka daga kamfanin” “Tau Allah ya kiyaye na gode” Hannunsa ya ɗaga min. “Ina gaida abokina Noor” Kai na ɗaga masa as respond na juya kamar zan shiga gidansu Zinatu, ina hango ya kama hanya, na juyo dan har ga Allah ba gidansu Zinatu zanje ba na san ma by this time bata gida, ko ma tana nan mi zanje na yi a gidansu yarinyar da bata ƙaunar zuwa gidanmu. Miƙe ti-tin gawon nama na yi har na ɓullo ta gurin gidan Alu, wato tsohon gonnan, na miƙe na tsallaka babban titi na doshi Candy Restaurant. Restaurant ne mai kyau da tsari ga tsafta, ba laifi ma'aikatan gurin suna na'am-na'am da mutane tun a farkon zuwana na lura da hakan. Kai tsaye na nufi gurin wanda na ke zaton babbansu mai sanye da riga orange an rubuta mata Candy Restaurant da fafaren harufa. “Assalamu Alaikum” “Wa'alaikissalam” “Sannu ko ka gane ni?” “Gaskiya ban gane ki ba, abun da yawa” “Ni ce wacce na zo kwanakin baya ka ce min Khadeeja Candy bata nan” “Ayya Allah sarki, sai kuma kika ƙara rashin sa'a yau ma bata nan” “Dan Allah ko kasan yadda za'ayi ma sameta?” “Gaskiya bata garin nan tana Gusau kusan yanzu a can take zama, ko tana garin ma da wahala ta shigo nan” “Dan Allah ko zaka taimaka min da numberta?” “Gaskiya ba zan iya baki numberta ta saboda matsala ta tsaro, amman ke zaki iya barin Number idan ta shigo gari sai na sanar da ke” A take na rubuta masa Number Jidda domin bana da waya, kuma Baba ko Inna babu mai waya a cikinsu. “Idan ka kira ka ce Nawwara kake nema” “Tau Inshallah” “Na gode” “Yauwa a sauka lafiya” Jiki ba ƙwari na juya na fito. Har ga Allah ban jidaɗin rashin ta tararda mai restaurant ɗin ba, ga kuma uwar hanyar da zan miƙe duk da yaƙe rana be yi sosai ba, sai dai ina jin kamar zan wahalar da kaina tafiya a ƙafa har zuwa unguwarmu. “Allah ƙa zame min gata” Na furta a fili ina busar da iskar bakina. Dabarar na je gidansu Zinatu ne ya faɗo min a rai duk da ban yi niyar hakan ba. Haka na kama hanya na miƙe na koma ta inda na fito har na isa ƙofar gidansu Zinatu. Har na kai hannu zan buga ƙofar gate ɗin sai mai gaɗinsu ya wangale gate ɗin gaba ɗaya daga can ciki. Zinatu hakince a motarta ta kunno kai da alama fita zata yi, har ta yi kamar zata wuce sai kuma ta tsaya ta sauke gilashin motarta tana kallona ta cikin baƙin gilashin da yake idonta. “Khadija Musa Kafinta” Ta kirani da sunan da nake amfani da shi a makaranta, nima kuma sai na kirata da nata. “Zinatu Alhasan Hamshaƙi” Ta yi wani shu'umin murmushi tana cire gilashin idonta. “Nawwara ashe ana ganinki ko dai hanya ce ta biyo da ke?” “A'a haka kawai yau na ce zan kawo miki ziyara” Ta yi ƙis a ƙasan maƙoshinta wato ƙwafa na ƙasan maƙoshi. “Aiko kin kyauta gashi kuma zan fita, ki shigo na saukeki gida kawai” Na ji wani sanyi a raina daman abunda nake nema kenan. “Okay” Na faɗa sannan na buɗe motar na shiga. Jefi-jefi muke firar makarantarmu wato Nana Girl's Secondary School, kamin na ɗauko mata zancen masters da naji ance ta fara yi. “Wallahi ina nan ina yi yanzu haka kuma na samu aiki a wani babban kamfani this monday zan fara” “Mashallah, Allah ya taimaka” “Amin ai ke kin ƙi karatu ko?” “Uhmm” Na yi murmushi kawai ina danne abunda ke raina, yawancin mutane sukan faɗa min haka musamman abokaina wai na ƙi karatu bayan kuma karatun ne ya ƙi ni tun da komau sai da kuɗi, hawan napep zuwa da dawowa ma ai sai da kuɗi. Har ta sauke ni ƙofar gidanmu bata kalma bata sake fita daga bakinta, nima kuma ban sake ce mata wani abun ba. “Na gaida Inna” Ta faɗa lokacin da ta ga na buɗe mota zan fita. “Inna zata ji na gode” “Okay” A bakin ƙofar gidanmu na tsaya ina kallonta cike da sha'awar rayuwarta, duk mutune da yayi karatu burgeni yake, balle ita da ta fara cin amfanin karatun a yanzu. Sai da na daina hangota kan kwanar gunguwarmu mai kwatannin sannan na shiga gida. Inna na samu a tsakar gida tana shara, gyale na kawai na yaye ya karɓi tsintsinyar dake hannunta na cigaba da shara. “Allah yasa dai an yi sa'a” “Wallahi ba'ayi ba Inna wacce na je nema bata nan, amman na bada number wayata aje mata” “Allah yasa mu da ce, amman dai daga yau karki saki zuwa wani gurin ki haƙura idan ” “Amin, inshallah nima zan haƙura indai da rabon na samu zan samu” “Allah ya miƙi albarka” “Amin” Ta shinfiɗa tabarma ta zauna ni kuma na cigaba da sharar ina labarta mata cewar Zinatu ce ta kawo ni gida. Bayan na gam sharar na tattara na kwashe, muka ji ana sallama a ƙofar gida. Inna ce ta amsa ni kuma na nufi ƙofar dan duba ko wanene. Ganin mutun sanye da kakin ƴan sanda yasa gabana faɗuwa sosai. “Nan ne gidan Musa Kafinta?” “Eh Nan ne” Na amsa murya na rawa. “Musa Kafinta yana police station na guiwa locos, ana son a sanar da iyalansa ne kuma baya da waya shiyasa na zo” “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, miya faru?” “Idan kika je can zaki ji” Ya juya yayi tafiyarsa, ni kuma na juyo cikin gida idona na zubar da ƙwalla. MAI KUKE TSAMANI A PAGE NA GABA? *RAI

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});