Chapter 17
Chapter 17
dace ba” ‘Musamman ga irina masu manyan mazaunai’ Na faɗa a raina. A fili kuma sai na ce. “Ai zan iya saka Hijabi ko abaya a sama” “Amman baya son haka, sai idan kin tashi aikin ko kuma idan zaki shigo, shi be yarda ma ko hula a saka a gurin aikin ba balle kuma Hijabi” Cike da mamaki na ce “Ba musulmi ba ne hala?” “Wallahi musulmi, amman mutumen sai a hankali, haka zaki ga tattoo a jikinsa, ina jin ya zauna waje ne” Na taɓe baki cike da ƙyamar halin mutunen duk da ban san shi ba “Allah ya kyauta amman abun baƙinciki ne ace musulmi ya rinjaya wani addini sama da nasa, ga shi ka ce ya cika tsanani” “Yana da tsanani sosai, amman tsananinsa yana burge ni wani lokacin, kin ga dole kowa ya riƙe aikinsa da muhimmanci, kuma kin ga wacan da aka canja baya damuwa da duk waɗannan abubuwan shiyasa duk ƙarshen wata sai an siyo kayan abincin da cups da aikatan gurin suke aiki da su, amman zuwan wannan ya saka dokar duk wanda ya fasa masa cups za a cire cikin albashinsa, dole kowa ya riƙa taka tsantsan da abubuwan gurin” “Amman daman ba a biyan kuɗin abincin ne?” “No ana biya restaurant ɗin da ke cikin kamfanin ai nasa ne, amman idan ba restaurant ba kin ga ma'aikici zai buƙaci shan ruwa ko wani abun ko kuma tea musamman ga masu zuwa tun safe, ko kuma idan aka yi baƙi, to duk da wannan cups ɗin ake amfani. Bayan ma wannan kamfani suna da Sabuwar Asibiti da aka buɗe nan by pass, One-On-One Special Hospital, amman ance ta masu kuɗi ce dan katin ganin likita ma ɗari takwas da hasin ne” Na jinjina kai ina faɗin. “Kamfanin ma akwai girma, ni Allah yasa ma har na yi aikin na gama ba zan ganshi ba” Sai kawai yasa min dariya. “Kina tsoro ne Nawancy?” “A'a ba tsoro ba ne, kawai ba zan iya jurar wulaƙanci ba ne, kaga ƙara ma ace bamu haɗu ba” Mun daɗe muna fira yana ta labarta min kamfanin da kuma wasu abubuwa na cikinsa da kuma yadda aikinsa yake, kamin hirar siyasar ƙasar nan ta shigo ciki, sai tara da rabi muka yi sallama ya tafi ni koma na cikin gida. Ko da na shiga su Habiba sun ci sun ciye an gutsura min ɗan tsiton cake da nama ƙwara ɗaya an aje min sai kuma ice cream a cibi. “Yanzu wannan abun kawai zaku bar min?” “Eh mana dan kin samu ma mun rage miki” Cewar Habiba, tana bani amsar tambayar da nayi, sai Noor yasa dariya yana cin namansa ya ce “Momy ƙyale Mama Habiba sai ta yi bachi zan ƙara miki karki kuka kinji?” Sakin baki Habiba ta yi. “Au ni zaka watsawa ƙasa a ido?” Ta kai masa dudu. Inna tasa dariya, yau kan ba laifi muna cikin farinciki farincikin da muka daɗe ba mu yi ba tun bayan rasuwar Baba, sam ba zaka gan mu a yanzu ka ɗauka akwai wata damuwa a ranmu ba. Daman can talauci baya hana mu walwala ko kuma farinciki, idan ka ganmu a damuwa to muna jin yunwa ne, da kuma mun samu mun ci sai mu gode Allah da wannan ni'imar, mu kuma roƙi na anjima. *** *** *** Kamar yadda muka kwana cikin farinciki haka muka tashi da shi, abun ka da sabon shiga su Noor na wucewa makaranta nima na shirya muka fita tare da Habiba ita ta wuce tata makarantar ni kuma na ɗauki hanyar gurin mu a Napep. Yau ma da na isa ban shiga ba sai da na ƙira Bilal na sanar masa ina bakin gate, shi ya fito ya shiga da ni, sai mita yake wai ya kamata ace na shigo ciki da kaina tun da Monday zan fara aiki, ni kuma ina taka tsantsan ne gudun ƙar na yi wani abun da ba daidai ba, shugaban ya ce zai hukunta tun ban fara aikin ba. Ciki ya shiga da ni har muka isa cikin wani ƙaton haɗi inda na faɗa musu sunana suka duba sannan suka ɗauko uniform ɗin dake cikin leda suka ba ni, sai kuma wasu takalmi masu kama ta da malaman lafiya na asibiti, suka miƙa min wasu takardun na saka hannu sai suka buƙaci idan zan dawo na zo da ƙaramin hoto na guda biyu, wai zasu saka a file ɗayan kuma a kuma na saka a catin zan rayata a wuya na shedar aikina. Ɗaya daga cikinsu ne ya yi min ja gaba har gurin da zan yi aikin nawa, kitchen zan riƙa gogewa da kuma da ake aje files kusan ɗaki biyar, sai dai ba ni zan yi sharar ba aikina Mopping ne kawai, kuma idan zamu yi mopping ɗin sai mun saka safar hannu idan mun gama mu jefar, sai kuma goge kofuna da jerasu a muhallinsu, shi ma sai mun saka safa, tsarin kamfanin kamar na turawa, lallai sai a yanzu na tabbatar da zancen Bilal na cewa Kamfanin yana takara da kamfanonin duniya. Mai nuna min aikina ya jaddada min kamin na jera kofunan sai na ƙirga ko guda nawane na rubuta a file ɗin gurin da kuma time da na fara da time ɗin da na gama, da kuma ko kofi nawa na tarar, daga ƙarshe Bilal ya kai ni reception ya nuna min gurin da zan saka sunana da kuma lokacin da na shigo, idan kuma na gama sai na saka sunana da kuma lokacin da na fita, ƙarfe bakwai zan fara aikin na ƙare tara, hakan na nufin bakwai ta yi min a can kenan. Irin yadda tsari da dokokin kamfanin suke sai duk na ji aikin ya fara fita raina kamar ba zan iya ba, sai dai babu yadda na iya tun da nema na ke yi kuma ba anan zan dauwamaba. Har bakin titi Bilal ya rakoni, muna tsaye da shi na hango motar Zinatu ta shiga kamfanin, na tabbatar da ita ɗin ce saboda hangota da na yi ta gilashin motar da ke sauke. Bilal ya tara min Napep na hau sannan ya koma ni kuma na kama hanyar gida ciki da mamakin tsare-tsaren wannan kamfani, gaskiya ba dan ina son aikin ba da na haƙura da yinsa, a gurin da na saba sauka na ce mai Napep ɗin ya aje, sai na karɓi ragowar canjin kuɗin da Bilal ya bashi na nufi cikin unguwarmu. A hanya na haɗu da mai gidan da muke haya, wata irin kunyace ta mamaye mu nasan yayi mana karamcin tun da be mana magana tun baya rasuwar Baba ga shi har Inna zata gama wanka takaɓan ta cikin wannan satin. Sun-sun-sun na gaisheshi ya amsa min yana murmushi tare da tambayar ya haƙuri. “Mun gode Allah dan Allah ka yi haƙuri akan maganar kuɗin nan, inshallah za a kawo” “Kuɗin me? Ai Bilal ya biya be faɗa muku ba ne? Tun Margayi be yi sati da rasuwa ba ya kawo kuɗin dubu arba'in cif” Na saki baki ina mamakin ikon Allah. “Wallahi ba mu sani ba” “Wallahi ya biya sai dai ayi masa godiya” Sallama na masa na wuce zuciyata cike da hauƙin Bilal, bakina kuma har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119