Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 94

Chapter 94

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da alheri” “Amin amin sai dai littafan da za a siyo” “tau kamar nawa za a kashe?” “Zamu siyo ahalari sai kuma husnul muslim da kuma dan goma mai hade da bakaken harufan arabi ta yadda zai maka sauki ganewa” “Kana da account ne?” “Eh akwai” “Okay ina zuwa” Wayarsa ya bude ya yi masa transfer 10k na siyen littafan, har Malamin na cewa kudin ya yi yawa sai ya ce ya dauki sauran abunda ya rage. Cikin dadin rai ya dawo parlour saboda yana jin ya fara taka wani mataki na gyara rayuwarsa, abunda yake ta kokarin yi shine ya zama uba na gari gurin Noor wanda zai yi alfahari da shi ko bayan ransa. Da kansa ya yi feeding Noor sannan ya shiga wanka ko da ya fito Rabi tana parlour zaune ta kawo masa kayan Noor da ya bukaci taje ta siyo, ita yasa ta shirya Noor, shi kuma ya shiga ciki ya shirya kansa sannan suka fito tare harabar gidan ita ta wuce shi kuma ya kama hanyar gidansu Nawwara tare da Noor dake gaban Mota. Jibril ne ya fara fitowa cikin motar sannan ya zagaya ya budewa Noor ya dauko ya dorashi kofar gidan. “Shiga ciki ka ce da Mamanka ina waje” Da gudu Noor ya shiga cikin gidan, bayan few seconds ya dawo ya ce “Wai ta ce ka shigo” Wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya dora kafarsa a kofar gidan ya shiga bakinsa kumshe da sallama. “Wa'alaikaissalam” Inna da amsa masa, sai ya zube a gurin yana kwasar gaisuwa kai baka ce ma shi ba ne, kansa a kasa yana mai jin kunyar Inna sosai kamar yau ya fara haduwa da ita. “Tashi Jibril shigo ciki, ashe an sallami Noor” “Eh an sallame shi jiya shine naje da shi gida” “Allah ya kara lafiya” “Amin ya rabb” Daga haka ya mike tsaye. “Bari na wuce daman wani gurin zanje na ce bari na fara kawoshi” “To an gode” Tashi ya yi ya juyo ba dan kuma yana da gurin zuwan ba, yace hakan ne kawai saboda ya kare kansa, yana son ya tambaya ina Nawwara kuma yana jin kunyar haka ga alheri yana son ya yi ma Inna kuma be san yadda zata kalleshi ba. Bayan na fito ya nufi motarsa sai yaji Muryar Nawwara ta kirashi. “Jibril” Ya juyo da sauri ya dawo zuwa inda take. “Nawwara kina lafiya” “Lafiya kalau” “Am sorry about yesterday” Ya fada yana kallon yanayinta sai kawai ya ga murmushi a fuskarta abunda ya bashi tsoro da kuma mamaki a lokaci daya, dan ya yi zaton wata bakar maganar zata fada sai kawai ya ji ta ce “Never mind, ni har na manta da wannan ma, amman Jibril ka ce min zaka canja ko?” Ya kara matsowa kusa da ita. “Na canja Nawwara ba wai zan canja ba, Wallahi na canja” “Idan har ka canja zaka zama uba na gari Jibril, kuma da na gari gurin Mahaifinka” “Abunda na ke kokarin yi kenan ganin na zama uba na gari wa Noor” “Miyasa zaka mikawa Siraj ragamar kamfanin mahaifinka?” “Saboda na yarda da shi kuma mahaifina ya yarda da shi, kuma ba zan iya jan raganar kamfanin ba a yanzu” “Saboda mai?” “Saboda ke Nawwara tunanina da damuwata duka akanki suke” Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce “Ya kamata ka yarda da kaddara Jibril, ka yarda abunda ya sameka da wanda zai sameka nan gaba duka daga Allah ne, ka daina saka tunani a cikin ranka saboda ni matar wani ce, idan har ka yarda da kaddara ina son ka cireni a cikin rayuwarka, Jibril ina son ka nuna min irin son gaskiyar da kake min ta hanyar maida hankalinka akan rayuwarka da kuma ta danka, ina son ka min alkawari Jibril cewar ba zaka sake shan cocaine ba, kuma zaka maida ragamar kamfanin mahaifinka a hannunka, ina son ka zama jarumi Jibril” Kallonta yake yi ido cikin ido yake karantar gaskiyar kalaman dake zuciyarta, duka abunda ta rokeshi yayi zai iya yi matukar hakan zai faranta ranta. “Na miki alkawari Nawwara zan yi duka abunda kika fada” “And lastly ina son ka cireni cikin ranka Jibril, ka yi focusing akan rayuwarka ta nan gaba da kuma ta danka, ka sa a ranka ko babu Nawwara zaka iya rayuwa, domin can baya babu ni a duniyarka, a yanzu ma idan babu ni zaka iya, na tabbatar min da canjin da kake cewa ka yi Jibril ka zama namijin gaske” Ya gyada mata kai yana murmushin da yafi kuka ciwo. “I promise you Nawwara zan yi dukan abunda kike bukata” “Zan maka addu'ah, kuma ina son na koma aikina tare da kai” “Zamu koma yaushe kike so?” “Allah ya kaimu, but Nawwara ina fatar ba za ki hanani kusanci da dana ba, kuma ba za ki hanani kyautatawa family ki ba” “Na fi kowa son ka yi kusanci da Noor Jibril saboda na san ko nayi aure ba zaka bar ni naje da shi, so tun yanzu ina son Noor ya saba da kai sosai da sosai, matukar wannan canjin da na gani a yanzu a tare da kai ya tabbata zan fi kowa farinciki Jibril I'm ever ready to help you ko dan saboda Noor” Matsowa ya yi kusa da ita kamar zai taba ta sai dai yasan babu wannan damar domin bata son ya tabata kuma shi ma kansa yana son sabawa kansa da wannan. “Thank you so much Nawwara, Wallahi Ina son ki sosai ina son ki yarda da wannan” “Na yarda Jibril” “Ina jin kamar mafarki na ke Nawwara, you actually changed” Ta yi murmushi tare da sanda kanta kasa abunda ya kara burge Jibril ya ji wani sonta na kara shigarsa, sai dai kalamanta na cewar ya fitar da ita daga ranshi be masa dadi ba, but shi kansa yasan yana bukarta cireta a ranshi ko dan ya samu sukuni a rayuwarsa. MUSTAPHA POV. Yau kwanansa biyu da dawowa daga asibiti, tun lokacin da Hajiyarsa ta yi ma Nawwara wannan furucin ransa ya sosu matuka yake jin rashin dacewa da kyautawa abunda Momynsa ta yi. Dan haka ya yanke shawarar yau sai ya kaiwa Nawwara ziyara saboda ya bata hakuri kan abunda ya faru, dan haka yana fita sallah magariba be dawo ba ya wuce gidansu Nawwara, ya taki sa'a yana aikawa kiranta sai gata ta fito cikin Hijabi sai kamshin turare take, sallama ta fara masa sannan gaisuwa ta biyo baya, daga nan kuma sai dukaninsu suka yi shiru ita tana jiran abunda zai fada mata shi kuma yana tunanin ta ina zai fara, da ta fara gajiya da shirun ne yasa ta ce “Ya jikinka? Sorry ban je na dubaka a asibiti ba” Yayi mamakin jin furuncinta domin sam be tsammaci ma zata fito ba balle har ta kula shi haka har da tambayar jikinsa. “Naji sauki sosai Nawwara, ina son na baki hakuri akan abunda Momy ta yi miki last time...” Ta daga masa hannu. “Mahaifiyarka tana da gaskiya Mustapha, na kaina uwa ce kuma uwa kadai tasan abunda wata uwar take ji game da danta, ni kaina ba zan yarda dana ya rasa rayuwarsa akan wacce bata san zafinsa ba, wacce na san ba zata taba aurensa

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});