Chapter 54
Chapter 54
Hijabina na ɗauki wayata na nufi Babban gida daman na kwana biyu ban leƙa ba. Ina cikin tafiya wayata ta yi ƙara alamar saƙo, da fari na yi zaton mtn ne ashe Bilal ne ya aiko min da saƙon barka da safiya. _Morning text does not only mean good morning. It also means, I think about you when I wake up, I love you._ Wani kalar farinciki ne da annashuwa suka nemi inda zuciyata take suka mamayeta, at that time phone ɗin ta nokia @360 ta yi ringing da number nan da aka saba kirana da idan wacce sai na ɗauka sai ayi shiru aƙi magana. Kamar ba zan ɗauka ba sai kuma na daure na ɗauka a tunani na Mustapha ne ashe Jibril. “Kai wai wane irin shashasha ne? Akan ne zaka riƙa kirana ne wahalalle” “Dan Allah ki yi haƙuri Wallahi na kira ne kawai na tambaya idan zaki zo aikin saboda na ga baki shigo ba yau” “So kai ne ko? Daman kai ne kake kirana ka ƙi magana ko?” “I just want to hear your voice” Ya faɗa muryarsa a ɗaƙile, ni kuma na ja tsaki na kashe wayar ma gaba ɗaya, saboda ya ɓata min rai. Ban wani daɗe Babban gida ba kasancewar ban tarar da Yakunbo ba domin a ɗakinta na ke shiga na kwanta saboda rashin hayani, mun ɗan yi fira da wasu cousins ɗina mata, sannan na taso na nufo hanyar gida. Ina shigowa gida na tarar da Inna ta rafka uban tagumi tana kallon ƙofar shigowa, da sauri ma ƙarasa kusa da ita. “Inna lafiya” “Mahaifiyar Mustapha ta zo gidan nan ta min cin mutunci, kuma ta gargaɗe ni matuƙar baki ƙyale ɗanta ba sai tasa an ci mana mutunci, har tana iƙirarin wai mun yi ma ɗanta magani mun zugashi yaje ya ci mata mutunci” Faɗuwa na yi zaune shi ƙenan mu dan muna talaka ba mu da gata kowa ya ɗauko shararsa sai ya juye akan mu wai mai muka yi mutanen nan ne...? JIBRIL POV. Lilo yake ta yi da kujerarsa hannunsa dafe a kai ya lumshe ido, sai shaƙar ragowar cocaine ɗin dake hancinsa ya ke. Siraj ne ya turo ƙofar office ɗin ya shigo riƙe da wasu takardu a hannunsa. “Kana ta takurawa kanka Jibril yarinyar ba zata zo ba, ɗazu fa nan ka kirata amman ta kashe maka waya, akwai mata da yawa fa a garin nan da ma wajen gari be kamata ace kana damun kanka akan ƴar talakawa ba...!” Da mugun ƙarfi Jibril ya daki teburin dake gabansa har wasu abubuwan suka zube ƙasa, ya kalli Siraj cikin wani irin ɓacin rai ya ce. “Oh s*** how many times do i have to tell you ka daina faɗin wani abu marar daɗi akan yarinyar nan ne, baka san wacece ita ba ka daina saka bakina a kan maganarta, you're just my friend so stay where are you” Yana kaiwa nan ya miƙe tsaye ya nufi window yana huci tare da busar da iskar bakinsa. Siraj ya tsorata sosai da yanayin Jibril duk zamansu tare be taɓa masa haka ba sai yau, cikin sanyin jiki ya ce. “Akwai wanda yake son ganinka” Ba tare daya juyo ba ya ce. “Yana da appointment da ni ne? Idan yana da ayi cancelling bana buƙatar ganin kowa a yanzu sai NJ, na faɗa maka idan ma wani abun ne akan aikin nan zaka iya wakiltata” “This one is important too, ya zo ne akan maganar gidan nan da ka siya na su Nawwara, ni ya kira na faɗa masa inda kake ya zo PA ya hana shi ganinka, so shiyasa ya ƙara kirana ya matsa yana son ganinka” Da sauri Jibril ya juyo yana kallonshi da idonsa da suka kaɗe sukayi ja. “Waye shi?” “Ban sani ba ya ce dai sunanshi Mustapha” “Bar shi ya shigo” “Ka faɗawa PA ɗinka ya barshi ya shigo domin yana reception yana jira” Daga haka Siraj ya juya ya fice, Jibril kuma ƴa nufi telephone ɗinsa. WHAT DO YOU EXPECT NEXT ....? *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee ❤* 3⃣4⃣ Tare da Siraj suka shigo a lokacin Jibril na zaune saman kujerarsa yana kallon ƙofar shigowa office ɗin. Tun da suka haɗa ido da Mustapha zuciyarsa take ta raya masa wani akansa, Siraj ne ya nuna masa gurin zama a cikin kujeru dake gaban teburin Jibril suna facing ɗinsa, domin Jibril in banda kallonsa babu abunda ya ke. Mustapha ya miƙa masa hannu. “Sunana Mustapha Faruk Turaki” Jibril ya daɗe yana kallon hannunsa sannan ya miƙa masa. “And...?” Mustapha ya yi mamakin ganin yadda yake amsa masa kamar baya maraba da mutane, sai dai be nuna masa komai ba ya ɗora akan abunda ya kawo shi. “Na zo ne akan wani gida da yake guiwa, wanda ka siya ta hannun Malam Haruna” “Me gidan ya yi maka?” “Be min komai ba, ance min ka siye gidan ne milion ɗaya ni kuma zan baka 1.5 million ka mallaka min gidan” Jibril ya yi murmushi tare da kwantawa saman kujerarsa yana lilo tare da wani shegen murmushi. “Waya faɗa maka ni na siya gidan?” “Malam Haruna ne ya faɗa min, naje gunsa ina son na siye gidan sai yace min wani ne ya siya sunansa Jibril, amman ya ce be san waye Jibril ɗin ba, yaro ne ko babban na buƙaci gani ka, yace bashi da number ka sai da ta wanda suka yi cinikin domin ya bar number akan idan mutunen gidan su tashi a faɗa masa, na buƙaci ya bani number wanda suka yi cinikin ne sai ya bani number wannan Siraj ɗin, ni kuma na kirashi sai ya yi min bayanin ba shi ya siye gidan ba kai ka siya kuma shi baya da wani abu da zai yi sai dai na yi magana da kai” Hannu Jibril ya kai yana wasa da wata ƙwallo da ake saman teburinsa mai ruwan zinari wance aka ɗora saman wani abu mai kama da turmi. “Amman miyasa zaka siya gidan har 1.5 million?” “Saboda kai da ka siye gidan ka bawa waɗanda suke cikin gidan kwanaki su tashi, that's why na ke son siye musu gidan” Siraj ya haɗa ido da Jibril sannan ya kalli Mustapha ya ce “Kana da alaƙa da ƴan gidan ne da har zaka siye gidan da kuɗi da yawa haka, gidan da be wuce dubu ɗari shida ba?” Mustapha ya watsa masa wani shegen kallo tare saboda yadda yaga sun maida shi ƙaramin yaro. “Mr gida na zo siye ba bincikar alaƙata da ƴan gidan na zo ku min ba” Jibril ya yi murmushi yana ciagaba da juyawa saman kujerar. “Come on tell me boy maybe i can help” Mustapha ya maida dubansa gurin Jibril jin irin isgilancin da yake masa, yanzu kan zuciyarsa ta fara raya masa akwai dalilin da ya sa Jibril ya siye gidan. “Ban girmi ka karani boy ba? Name what ever you want zan baka am not here to play a game” Jibril ya miƙe tsaye yana dariyar ƙeta ya nufi gurin window sa yana faɗin. “In banda kai daƙiƙi ne baka taɓa tsayawa ka yi tunani ba, baka taɓa tambayar kanka dalilin da yasa ka na siye wannan gidan ba?
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119