Chapter 79
Chapter 79
“All this while.. The killer’s right in front of me. Makashiyar tana nan a gabana.. Ina can inata neman makashin ba tareda sanin tana nan tare dani ba.. Claiming to be my wife.. wacce tafi kowa kusanci a gareni bayan mahaifiyata..” Ya d’ago idonsa wanda siririn hawaye ke gangarowa daga ciki yana duban Assad. Lokaci guda yaci gaba da furta “She killed my sister Assad, and then she acts innocent.. Like she was also grieving for Ikram’s death.. She made me look like a complete idiot. Ina can inata bincike kaman wani wawa.. Tanata toshe duk wani hanyar da zanbi na samu gaskiya.. Assad she insulted my profession, you know.!” Saurin dafasa Assad yai yana fad’in “Try to calm down first.. please Mu’azzam..” Mik’ewa Mu’azzam yai yana fad’in “You’re not the one who’s being fooled by the woman you call her wife..! You are not the one who lost a sister in the most painful way.. So don’t.. even.. ask me to Calm down..!” Yai maganar jijiyar goshinsa na kuma fitowa sosai gumi na kuma tsartsafo masa. Kafin Assad yace wani abu Mu’azzam ya nufi k’ofa. Assad yai saurin take masa baya yana ambaton sunansa amma inaa ko sauraronsa baiba. Karo suka kusan yi da Chief Jaja wanda ya nufo Office d’in. Mu’azzam ya tsaya Cak yana duban Chief da idanunsa da suka gama kad’uwa. Chief yana murmushi yake shafa hab’arsa lokaci guda yana duban Mu’azzam d’in “Inspector Gamji, I hope you learned your lesson.. You should know there’s no right way to do wrong things.. Next time sai a kiyaye..!” Ya k’arashe yana bubbuga kafad’an Mu’azzam d’in guda. Maleeka dake tsaye gefe itada Yusuf sai aika ma Chief mugun kallo take musamman da taga yanayin Mu’azzam d’in. Mu’azzam baice da Chief komai ba har ya gama maganganunsa sai dubansa da rinannun idanunsa da yake. Lokaci guda Chief ya gyara tsayuwarsa had’ida gyaran murya “Any update regarding your case, Inspector Gamji..?” Ya tambaya yana tsare Mu’azzam d’in da idanu wanda ko motsi mai kyau ya kasa Sai dad’a damk’e wayar Sagir dake cikin hannunsa yake. Chief ya gyara tsayuwarsa yana karantar Mu’azzam d’in.. Lokaci guda Maleeka da Yusuf suka k’araso yayinda Assad ma gaba d’aya za’a iya cewa ya shiga missed call. Yama rasa mai zai yi sai duban Chief yake yana kuma duban Mu’azzam. Chief ya dubi Assad ya kuma duban sauran team members d’in Wato Yusuf da Maleeka. Nan yaga gaba d’ayansu kaman an cire masu laka. “Detectives..!” Chief ya fad’i yana dubansu d’aya bayan d’aya kafin ya tsaida idanunsa kan Assad. “Shattima.!” Ya kira surname d’in Assad. Assad ya sara masa “Sir.!” Chief yaci gaba da fad’in “Any progress..?” Duban Mu’azzam Assad yai cikin rasa mai zai fad’i. Yanzu kam ran Chief ya soma kad’uwa wajen b’aci. Cikin tsananin zafin nama yake furta “Why are you all mute.?” Ya girgiza kai yana ci gaba da furta “It seems we assigned this case to bunch of incompetent Detectives.. Am I right.?” Ya k’arashe cikin daka tsawa. Yayinda suka duk’ar da kawunansu k’asa idan ka cire Mu’azzam wanda har lokacin duban Chief yake bai daina murza hannunsa ba. “Give me updates now. Detectives.!” Ya k’arashe cikin tsananin daka tsawa. Zuciyar Chief fari k’al ganin basu ce komai ba, yanzu ya tabbata dole a gaji ai closing case d’in kaman dai yanda suka tsara. Ya wani gyara tsayuwa yasha mur sosai kafin ya soma jinjina kai cikin tsananin b’acin rai yana duban Mu’azzam d’in “I am going to warn you for that last time Inspector Gamji..! Bring all your team together to collaborate more effectively on this case.. Unless kana so ai maka retire before your retirement period.!” Lokaci guda Mu’azzam ya d’ago wayar daketa faman dunk’ulewa cikin hannunsa yana nunawa saitin fuskar Chief. “Meye wannan..?” Chief ya tambaya. “It’s Sagir’s cell phone.. Sir.!” Mu’azzam ya basa amsa kai tsaye. Dukda cewa zuciyar Chief ya yanke, ya kuma razana da ganin wayar Sagir d’in amma Sai ya wayance yace “Good.. At last something good came out of your investigation.! Good Inspector Gamji.. You’re one of our best agents. Nasan bazaka bamu kunya ba.. Let’s see what you found inside..” Ya k’arashe yana mai kad’a kafin ya nufi office yana fad’in su biyosa.. Babu musu suka bi bayan Chief. Zuciyar Chief sai yankewa take. Ya kula Mu’azzam bazai tab’a dakatawa ba har Sai ya tono komai. Ya tsani Mu’azzam.. Sannan zai komai in his power ya tabbata Mu’azzam ya bar aikin D’ansanda for good. ** Su Safeenah suna komawa guda suka tadda Daddy zaune harabar gidan saman kujeru na shak’atawa. Sai kallon kallo suke ma juna ganin Daddy ras kaman ba shine Aunty Shemau ta kira ta sanar dasu Baida lafiya sosai ba. Dan har kaman kuka sukaji tanayi cikin wayar. Gaba d’aya suka fito suka nufi mahaifinsu wanda Mommy ke zaune gefensa ta cika tayi fam sai girgiza take. A guje Meema da Kiki suka k’arasa suka rungumesa “Daddy wai bakada lafiya..? Daddy munji tsoro sosai.?” Murmushi ya sakar masu ya shafi fuskokinsu kafin yace “I’m fine now.. Ku kwantar da hankalinku Kunji koh...” Kiki ta kuma rungumarsa tana fad’in “Daddy banso mu rasaka.. I can’t even bear the thought of it..” Ya shafi kanta kad’an yana murmushi kafin yace “Ku shige ciki zamuyi magana da Addarku..” Babu musu suka shige dan Mommy kam basu ma ga fuskar mata magana ba tsaban tafarfasa da take. Safeenah dake tsaye daga baya tana hawaye suna shigewa ta k’araso ta zube kanta saman cinyar Daddy dake zaune kan kujera. Kuka take sosai tana fad’in “Daddy it is true..! Daddy Mu’azzam mace yakai cikin gidana.. Daddy zan mutu.. Mutuwa zanyi Daddy.. I can’t take this anymore..!” Bai hanata kukan har saida tai mai isanta kafin ya dubi Mommy yace “Can I have a moment with my daughter, Please.” Mommy Ta dubesa da mamaki kafin Ta soma magana cikin huci “Wllhi wllhi kaji na rantse maka da Allah sai na maka Mu’azzam a kotu.. Ko ka shawo kan Safeenah ka danneta wllhi sai nayi k’aran Mu’azzam kan abinda yayima Safeenah. Har ofishin nasu zan tafi na kai masa sammaci wllhi.. Babu ruwana da cewa shi D’ansanda ne.. Idan shi bakin bindiga ne k’arewar tsaro wllhi Sai na maka k’ararsa ehe..!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye. Daddy ya d’ago yana dubanta “Kin gama.?” Bata basa amsa ba sai ci gaba da jijjiga da take. “Idan kin gama leave us alone with my Daughter.. Please..” Mugun kallo ta watsa masu daga shi har Safeenar kafin Ta wuce fuu kaman zata tashi sama. Aunty Shemau dake tsaye saman Balcony d’in Mommy akan idonta komai ya faru. Tana ganin Mommy ta nufo cikin gidan ta nufo k’asa itama. Daddy ya d’ago Safeenah ya zaunarta saman kujerar gefensa yanda Mommy ta tashi. Har lokacin Safeenah bata daina jan zuciya ba alamun taci kuka. Daddy yai gyaran murya a hankali kafin ya soma fad’in “I know you’re hurt.. And you’ve the right be angry.. Dole kiji zafi dan jin zafi.. Amma abinda nake so ki sani shine tashin hankali bai tab’a kawo solution wa matsala ba, saidai ma ya k’ara b’ata komai.” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Safeenah my Daughter, don’t allow your anger to consume you..
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243