Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Gidan Aro Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wacce malama ce kuma har matan aure tana koyarwa, wasu lokutan idan Kyallu Ta fice tsiddabarunta da bokancinta gidan Malama Hafsatu take zuwa domin ta taimaka mata da abinci.. Yau d’inma hakance ta kasance da Ajidde.. Malama Hafsah na aji tana ma matan aure karatu Ajidde ta shigo da k’yar da k’yar kaman zata kifa k’asa.. ‘Yan aji suna ganin Ajidde suka soma k’ok’arin mik’ewa kowacce tana neman hanyar gudu dan an canfa ance tanada Farin k’afa dik yanda taje Sai bala’i ya auku wajen.. Malama ta tsawatar masu da fad’in “Shin ba yanzu muka gama karatu kan yarda da canfi ba.. Canfi haramun ne a musulunci.” Wata mata Ta d’aga hannu tace “Malama inada tambaya” Malama Ta jinjina mata kai tace “Ina sauraronki..” “Amma malama ai akwai Kambun baka.. Shin shi ba canfi bane..?” Malama ta jinjina kai tace “K’warai Al’ainu haqqun. Akwai Kambun baka, harta a musulunci an yarda akwai Kambun baka, yazo kuma a sunna cewa akwai Kambun baka har an bamu addu’a da zamu dinga yi domin neman tsari daga sharrin Ido wanda ake cema kambun baka.. D’aura laya ko wani abu mai kama da haka da sunan neman kariya daga sharrin ido haramun ne a musulunci.. Yin hakan shirka ne inji Manzon Allah SAW, hadisin yana nan a cikin Musnad Ahmad 16969.” Malama ta d’an tsagaita kafin taci gaba da fad’in “Wacce dik take neman kariya daga sharrin ido ko Kambun baka ga abinda zatace ‘A’uthzu bi kalimatillahit taammaati min kulli shaid’anin wa haammaa wa min kulli ainin laammaa.’ Wannan addu’a ce ingantacciya datazo a sunna sannan zaki iya karanta ma yaranki ko wacce safiya da maraice domin nema masu kariya daga sharrin ido dama duk wani shed’ani ko abin sharri.. Babban darasin da nake so mu d’auka a nan shine wani baya tab’a sauk’ar maka da bala’i sai idan Allah yaso haka wani baya tab’a kawo maka nasara sai idan Allah yaso Kun fahimta..” Gaba d’aya suka amsa da “Na’am Malama mun gane..” Malama ta jinjina kai tace “Monita ki bud’e shafin da muka k’ara jiya ayi bitarsa kafin na dawo muyi k’ari.. Ku d’an ara min lokaci naji da Ajidde..” Gaba d’aya suka jinjina kai suna amsa mata.. Malama ta janyo Ajidde suka fice zuwa tsakar gidanta.. Dik karatun kore shirka da aikata tauhidi da malama tai tsaf Ajidde ta saurareta, gaba d’aya jikin Ajidde yayi sanyi domin kuwa abinda Inna Kyallu ta d’aurata Kai kenan.. Malama ta nufi kitchen ta d’auko ma Ajidde abinci Ta bata tace ta zauna taci.. Saidai yau gaba d’aya jikin Ajidden a sanyaye yake babu sokancin data saba yima Malama.. Tak’i zama taci abincin ta fice sai waige waige take tana kuma duban Malamar rungume da kwanon abincin. Sauri sauri ta fice dan kar Inna Kyallu ta dawo ta tadda bata nan.. Malama Ta bita da kallo cikeda tausayawa har Ta b’ace ma ganinta.. Allah ya gani rayuwar yarinyar sosai yake bata tausayi.. ** Koda Kyallu ta isa gidan gonar sassafe tasa aka rufesu a d’aki daga ita sai Aunty Nurah, tai mata hayak’i da surace na magani.. Ta ciro wasu layu guda biyu ta bama Aunty Shemau tace a saka cikin matashin da Aunty Nuratu ke kwanciya.. Shemau Ta amsa tanai mata godiya.. Nan take sanar da Aunty Shemaun idan bata sami zuwa Washe gari ba zata turo d’iyarta ta bata maganin dan ita kusan ko yaushe fama take da masu karb’an magani.. Aunty Shemau tace babu damuwa za’ayi dik abinda Kyallu tace d’in.. Koda suka fito Daddy na parlor yana jira ya shiga yayi sallama da matarsa dan a yau d’in zai koma Abuja.. Koda Daddy yaga Kyallu tsareta da idanu yayi dan haka kurum yaji mata mai maganin bata wani kwanta masa ba amma yasan ba daga appearance na mutum bane kyaun magani.. Kuma basu san a Ina maganin Nuratu yake ba.. Idan aka dace sai maganin wannan matan yayi mata aiki.. Shemau dikda tasha jinin jikinta da ganin Daddy zaune yana jira a parlor hakan bai hanata wayancewa ta risina tana gaida Daddy had’ida introducing Kyallu mai magani.. Daddy ya amsa masu da sakin fuska ya kumayi ma Kyallu godiya.. Har zasu shige Daddy ya tsaida Shemau, ya ciro kud’ad’e da dama yace a k’ara wa mai maganin.. Kyallu ta kanne idanu tana duban tulin kud’in da aka bata.. Tuni ta Washe baki ta shiga yima Daddy godiya da addu’an girma.. Lokaci guda tana kuma gwad’a maganinta da fad’in nan da k’ank’amin lokaci zasuga canji jikin Nuratu.. Daddy yace Allah yasa haka kafin ya nufi d’akin.. Kwance take fuskarta Ta kuma yin fayau Sai hancinta da d’an bakinta kake hangowa, Ya k’ura mata idanu k’walla fal idanunsa.. A hankali ya duk’a ya d’aura hannunsa guda saman nata. Cikin rawar murya yake furta “Bansan ko na cika alk’awarin da na d’aukar ma d’anuwana ba cewa zan kula da bayansa.. I don’t know why I’m feeling this way.. Like I failed somehow.. Ban cika alk’awarin dana d’aukar ma d’anuwana cewa zan kula da bayansa ba.. It’s been 15 long years kina kwance cikin jinya ba tareda Kinsan a Ina kike ba.. And.. And Ikram..” Kuka ya hana Daddy ci gaba da magana, kansa kife gefen Nuratun, yake furtawa cikin murya irinta mai kuka “I failed to protect his family.. Na kasa kula dasu as I promised to.. Na kasa..!” Mu’azzam yai tsaye bakin k’ofa yana duban yanda Daddy ke kuka kan mahaifiyarsa yana fad’in ya kasa kula dasu.. A hankali yake takowa cikin d’akin har ya k’araso yanda Daddy ke duk’e.. Yakai hannu ya dafasa. Daddy na d’agowa da yaga Mu’azzam d’in sai ya kuma jin rauni can k’asar zuciyarsa.. A hankali Mu’azzam ya duk’a ya rik’o hannayen Daddy cikin nasa “Baka gaza ba Daddy.. What was meant to happen happened. Kuma Ka kula da bayan mahaifina kaman yanda kayi alk’awari.. Daidai da rana guda baka fasa cika alk’awarinka ba.. You’re true definition of a good brother Daddy... You’ve been taking care of us ever since my father passed.. You’ve become a father to his children and a husband to his wife wacce tin sanda ka aureta Allah ya jarabceta da jinya.. I’ve seen a lot of men wad’anda idan matansu Sun kamu da cuta irin haka har gida suke maidasu suje suyi jinya wasu ma auren ya k’are.. But bakayi haka ba Daddy.. Kai d’in ka d’auki d’awainiyar jinyarta kuma ka kula da ita daidai da rana guda baka gaza ba..” Saurin girgiza kai Daddy yai yana mai duban Mu’azzam d’in “Don’t say those words Mu’azzam dik abinda nayi nauyi ne da ya rataya a wuyana and it’s not a favor kaji koh.. Come here..” Ya k’arashe yana rungumar Mu’azzam d’in. Uncle Salman dake tsaye jikin k’ofa da ido ya tsaresu, lokaci guda ya koma da baya ba tareda ya bari sun gansa ba. ** SULEJA Tashin hankali goma da ashirin shine abinda Sadiya da ahalinta ke fuskanta, a yayinda mahaifinsu ko rufa kwanaki uku baiyi ba da mutuwa Tabawa ta kuma sakosu gaba da maganan biyan kud’inta.. Babu yanda Umma batai ba ta bari ko takaba ne ta gama idan yaso sai ta fita ta nemo mata kud’ad’enta ko wani aikin ne sai tayi ta samo mata kud’ad’enta.. Tabawa tace atafau ita bataji

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});