Chapter 192
Chapter 192
min.. Allah sarki gashi da yake yaron kirki ne bai makani a kotu ba balle ya kulleni..” Kiki ta jinjina kai tace “Shiyasa nace miki har yanzu kallon uwa yake miki Mommy, da ace ya daina ganin girmanki da tuni ya kulleki a cell.. Yanzu ma ko kince Addah Feenah ta koma gidansa ne bazai ce komai ba nasan bazai so Inne tasan ya abinda ya samu cikin Addah Safeenah ba balle har Ta fahimci asibitin mahaukata aka kaita.” Mommy ta jinjina kai tace “Haka ne Karima.. Muje ko Allah shi miki albarka.” Kiki ta murmusa kafin ta d’an rungume hannun Mommy guda b’angaren jikinta kafin suka nufi sashen Inne da aka gina mata a cikin gidan. Suna isowa suka tadda kaf d’insu suna Parlorn, Daddy Uncle Salman Mu’azzam harma da Musaddiq. Inne na zaune daga tsakiya saman kujerarta da akasarin lokuta take zama bisa. Duba d’aya zakaiwa Mommy ka fahimci jikinta a matuk’ar sanyaye yake. Ta saci duban Daddy da Mu’azzam taga irin kallon da suke aikata mata musamman Daddy. Amma abinka da gogaggiya sai tai k’ok’arin saita kanta kaman dai babu abinda ke wakana.. Nan ta shiga gaida Inne tana mata sannu da zuwa cikeda ladabi kaman dai yanda ta saba harda cewa batasan tana tafe ba da an girka mata abincin da tafi so. Inne tace “Yanzu ma bai b’aci ba Hajara Kinsan ni bana son abincin nan naku wanda banda ganye babu komai.. Mutum yaita tura ganye zallarsa a cikinsa saikace tsutsa, Yo ganye ya wuce zogale ai ba ganye bane..” Mommy sai murmusawa take kanta a duk’e tana fad’in “Babu komai Inne yanzu za’a shiga kitchen a girka miki naki..” Ta k’arashe maganar tana mai tambayar Inne “Ya kuka baro can gidan.. Ya Aunty Nuratu kuma da jiki..?” Da tsananin mamaki Mu’azzam ke duban Mommy yana jinjina makirci irin nata, matar da ta turata a bata maganin ‘yanrufa ido shine yanzu take tambayar k’arfin jikinta. Bai ma iya sauraron amsar da Inne ta bawa Mommy ba banda kallon mamaki da yake binta dashi baya iya komai, baya fata Inne ta fahimci wani abu sabida kar hankalinta ya tashi, a dole yai k’ok’arin saita kansa. Muryar Inne ya sinkayo tana tambayar Mommy ina Safeenah taga kowa bata ganta ba. Mommy ta d’ago ta dubi Daddy dake aika mata mugun kallo kafin ta d’an saci duban Mu’azzam wanda shima d’in da gani kasan k’ok’arin danne kansa kurum yake. Ta d’an gyara zaman mayafinta tana murmushi kafin tace “Ai Safeenah ta koma gidanta Inne.. Tana can d’akinta..” Shaye da tsananin mamaki Mu’azzam ke duban Mommy yanzu kam. Wai Safeenah ta koma d’akinta. Inne ta dubesa tace “Kai Modibbo haka akai ashe..?” Mu’azzam ya rasa ta cewa, ya d’an jinjina kansa kad’an yana fad’in “Eh.. Haka ne Inne..” Ya k’arashe yana mai aikawa Mommy mugun kallo. Inne tace “Yayi.. Yayi kyau, hakan ai yafi.. Mutuwar aure sai dole balle ma ace auren zumunci irin wann.. Allah ya kad’e fitina ya zaunar dasu lafiya ita da abokiyar zaman nata..” Mommy har na murmushi take amsawa da “Ameen Inne..” Mu’azzam kasa jure zaman parlorn yai dan sosai zuciyarsa ke masa zafi musamman idan ya dubi Mommy da Uncle Salman. Hakan yasa yai ficewarsa daga parlorn cikin sauri.. ** A b’angaren Safeenah kaw tana can Mental Facility yanda take samun kula daga k’wararrun likitoci. Haka Safeenah tai kusan a daren da ya gabata tana bugun k’ofa tana fad’in Su k’yaleta ta fice ita ba mahaukaciya bace da hankalinta. Yanzu ma hakance ta kasance sai dukan k’ofa take tana fad’in suzo su fitar da ita zataje wajen mijinta da D’anta suna jiranta. A haka Ta gaji Ta kwanta saman gadonta hawaye na gangaro mata. Wai ita Safeenah Gamji ce aka kawota asibtin mahaukata aka ajiyeta, kenan da gaske mahaukaciya suka d’auketa bacin ita da hankalinta kuma ta tabbata cikinta na nan bai fice ba, zata haifo D’anta kuma Mu’azzam zai mai da ita.. Har abada bazata tab’a barin Mu’azzam ma wata ba shid’in nata ne.. Haliliyarta ce ita kad’anta. Hawaye mai zafi ya gangaro daga cikin idanunta. Tana jin alamun shigowar nurse cikin d’akinta tai likimo kaman dai bacci take. Nurse d’in ta aje tray d’in magunguna da Ta shigo dashi ta shiga k’ok’arin had’a allurar da zatai ma Safeenah. Safeenah ta kuma kannare idanunta kad’an tana duban Nurse d’in daketa k’ok’arin had’a ruwan allurar. Aiko tana ida had’a allurar ta nufo Safeenah zata mata allurar Safeenah tai kukan kura ta janyo k’arfen lank’aye drip dake gefenta ta rabza ma nurse d’in akai.. Nurse d’in tana fad’uwa Safeenah ta d’auki allurar ta danna mata.. Sauri sauri ta soma k’ok’arin sauya tufafin malamar jinyar da nata. Tsaf Safeenah ta shirya cikin tufafin Malaman jinyar asibiti ta rufe fuskarta da mask, ta inayo nurse d’in da k’yar ta azata saman gadon bayan ta sauya tufafinsu, lokaci guda ta silale ta fita daga asibitin. ** A can gidan Daddy kaw a babban parlorn Daddy suka hallara bayan da suka tabbata Inne ta shiga ta kwanta dan bazasuyi komai a gabanta ba gudun kar hankalinta ya tashi da abubuwan da zataji. Daddy Uncle Salman Mommy sai ko Mu’azzam. Uncle Salman ya girgiza kai a karo na biyu yana duban D’anuwansa Marwan wanda shi ne ya gayyatosa gidan nasa “Marwan Wai meke faruwa ne.. Ka kirani kace na taho cikin gaggawa zamu tattauna matsala da ya shafi companies d’inmu.. Mene kuma nake gani haka.. Idan Mu’azzam nada shares a company naji zai iya tsayuwa a nan a tattauna dashi toh amma mai matarka take a nan..?” Daddy yai gyaran murya kad’an yace “Munada buk’atansu a nan ne Salman shiyasa ka gansu..” Ya d’an gyara zamansa kafin yaci gaba da fad’in “Salman wace takarda ce kake nema wajena wanda har kukayi amfani da Hajara kaida matarka dan kun cimma burinku na mallakar wann takardan.?” Dummm! K’irjin Uncle Salman ya bada wann sautin. Bakinsa ya soma rawa yana furta “Ta..Takarda kuma.. Wace irin takarda..?” “Yarjejeniyar da kace kinyi kaida mahaifina cewa ya mallaka maka Kaso na dukiyarsa.. Shin Ka tuna Uncle..?” Mu’azzam ya k’arashe yana duban Uncle Salman cikin ido. Uncle Salman ya shiga girgiza kai yana furta “Ban.. Ban fahimta.. Wace takarda kenan..?” Mommy tai caraf tace “K’warai kuwa ka sani Salman domin kuwa Shemau ta sanar dani cewa dan na samo maku wann takardan daga hannun Marwan shiyasa ka turo Shemau ta shiga jikina.. A cewarka Marwan shi ya d’auke wann document d’in domin ya cinye dukiyar D’anuwanku Abubakar.. Tabbas anyi haka kuma kaima kasan anyi haka.. Ni bansan da wata takarda ba na yarjejeniya har saida Shemau ta sanar dani cewa wann takardan kuke farauta hannun Marwan kaida matarka Shemau..” Ta k’arashe cikeda k’warin gwiwa irinta mai gaskiya. Daddy ya girgiza kai yana duban Uncle Salman da gaba d’aya ya daburce kafin yace “Salman wace takarda ne wann..? Sannan Maiyasa kace takardan na hannuna bayan ni bansan da wata takarda ba..?” Mu’azzam ya k’araso gaban Uncle Salman sosai wanda gaba d’aya gumi ne ke karyo masa dukda sanyin AC dake busawa cikin parlorn. Lokaci guda yake furta “Sabida ka cimma burinka na mallakan takardan yasa kukai tarayya kaida matarka harma da Mommy kuka d’auko wa mahaifiyata mai magani na bogi..? Sabida ka mallaki wann dukiyar ne da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243