Chapter 159
Chapter 159
Musaddiq ya d’an fuzar da fuci yace “Wai baka ganin Mommy Ta tsira abubuwan da batai ba a baya ba. Batayi wad’ann abubuwan zamanin k’uruciya ba sai yanzu da girmanta muma da girmanmu.. Haba Mu’azzam wann ai rashin dacewa ne.” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Na Sani Musaddiq. But still Mommy mahaifiyarka ce.. Kar kace zaka d’aga mata murya ko zaka mata tsawa.. Iyaye ko ba musulmai bane ba’a d’aga masu murya Musaddiq.. AlQura’ani mai girmama wajaje da dama yayi umarni da cewa a kyautata ma iyaye. Wann zai tabbatar maka iyaye ba abun wasa bane.. Girman hakkinsu ya shige abinda za’ayi wasa dashi.. Musamman uwa wacce takeda girman hakki akan D’anta kaso uku kafin uba wanda yake da guda d’aya kaman yanda yazo a hadisin Annabin rahama (S.A.W).” Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Ko nasiha zakai ma iyaye kwantar da kai ake da lallami da kwantar da murya da lallashi.. Ba’a yima iyaye ihu Musaddiq.. Sai Mommy ta d’aga maka k’afa ka shiga Aljannah.. Kaje ka bata hak’uri anjima kuma ka lallasheta.. Ni nasan ba halinta bane kawai zafin abinda naima d’iyarta Safeenah ne yasa take duk wad’ann abubuwan.. But I believe Mommy tanada zuciya mai kyau tinda ta rik’emu bisa gaskiya da amana ta kuma d’auki tsawon shekaru tana jinyar mahaifiyata. Wacce duk zatai haka akwai goodness a cikin zuciyarta.” Musaddiq ya d’an jinjina kai kad’an yana had’e fatun bakinsa “Shikenan zanyi yanda kace.. Zan bata hak’uri..” Mu’azzam ya murmusa yana dubansa, Sai ya tuna sab’anin da suka samu a Gidan Gona. Ya kuma murmusawa yana jin dad’in yanda al’amra suka soma daidaituwa tsakaninsa da D’an uwan nasa. Ya d’an bubbuga kafad’ar Musaddiq d’in guda kafin suka soma tafiya suka nufi b’angaren Musaddiq d’in Mu’azzam na fad’in “muje mu buga PS mana na d’an lallasa maka kad’an.” Video game din suka d’anyi tare wanda suka jima basuyi ba, Musaddiq d’in sosai yaji dad’in samun time da D’anuwansa da yayi wanda suka kwana biyu basuyi hakan ba. Haka Musaddiq ya lallasa wa Mu’azzam a game d’in. Mu’azzam ya aje control pad d’in yana d’ago hannayesa biyu alamun surrender. Musaddiq ya dara kad’an yana fad’in “Haba Officer ka bada gari kenan..?” Mu’azzam ya tab’e baki kad’an yana d’aga kafad’unsa “Ni yanzu bayan bincike I guess babu abinda na iya.” Yai maganar yana mai mik’ewa tsaye. Musaddiq na nan rik’e da control pad d’in yana ci gaba da darawa idanunsa kan TV. Mu’azzam ya d’an matsa gefe yana duban D’anuwan nasa. Take tunanin B.A.T ya fad’o masa. D’an kauda fuska yai yana k’ok’arin kauda tunanin. Kaman ance ya dubi saman kujerar dake bayansu ya hango hular Musaddiq mai d’aukeda B.A.T ya k’arasa a hankali ya d’auki hular yana juyata. Musaddiq dake ci gaba da buga game d’insa d’an juyowa yai yana duban Mu’azzam rik’eda hularsa ya k’ura mata idanu. Murmushi yai yana furta “Duk wanda ya sanni ya sanni da son wann hular.. Idan baka mance ba a wani Kanti muka saya a London nida kai wani rakiya da mukayi wa Aunty Nuratu.” Tin a shagon na d’auki hular sanyin na gwada akaina.. Kuma na kasa rabuwa da ita har yanzu.. Kwanaki da ban ganta ba har na soma tunanin ko na rasata ne ashe a laundry na saka.” Mu’azzam ya murmusa kad’an yana mai jinjina kai kafin ya aje masa hular. Lokaci guda zuciyarsa tana tuhumarsa Maiyasa zai tunanin Musaddiq nada wata alak’a da Danger bayan hula ce kawai ya gani mai kamanceceniya data Musaddiq d’in.. Company zata iya yin dubanninsa. Aje hular yai yana fad’in bari ya shiga nasa d’akin yana zuwa. Musaddiq ya jinjina masa kai yana mai bin bayansa da kallo.. Aje control pad d’in shima yai kafin ya k’arasa ya d’auki hular yana juyata. Cikin sauri ya nufi d’aki hular tana nan dunk’ule cikin hannunsa. Wardrobe ya bud’e ya turata can ciki yana mai shafe fusakrsa da duka tafukan hannayensa. D’akinsa na samartaka ya shige abubuwa cunkushe cikin zuciyarsa, ya rasa Wanne tunani zaiyi. Drawers ya soma k’ok’arin dubawa ko zaiga yanda ya aje wann coin mai kamanceceniya da wanda ya samu hannun k’anin Sadiya wanda yakeda tabbacin su Danger sunada alak’a da wann coin d’in. Sann idan haka d’in ne zasu iya zama sunada alak’a da mutuwar mahaifinsa. Toh amma tin mahaifinsa nada rai ya tab’a samun coin d’in cikin stuff d’in mahaifin nasa.. Toh kodai akwai abinda wad’ann kalaman na jikin coin d’in suke nufi ne..? Ko maybe wata K’ungiya ce da ta shafi su Danger.. Mahaifinsa was a successful business man. Watak’ila su Danger da Association d’insu sun jima suna bibiyan ahalinsa.. Watak’ila akwai dalilin da yasa suka sace Ikram.. Yai shiru hab’arsa saman hannayensa da ya dunk’ulesu waje guda yana tunani. A hankali ya mik’e had’ida tura hannayensa cikin aljihu yana taka d’akin yana nazari. Mai Maleeka take son sanar dashi.? Take zuciyarsa ta basa amsa da fad’in “So take ta sanar dakai ga makashinka.” Ya k’ara jefo tambaya ma kansa “Wanene Makashin Maleekar.?” Zuciyarsa ta kuma basa amsa “Ka bud’e kalaman da Maleeka ta sanar dakai a dunk’ule zaka iya fahimta.” Ya d’an shafe hab’arsa kad’an kafin yana mai k’arasawa jikin window. Sai yaji kaman mostin mutum ya fice daga bayansa. Ya d’an waigo yana dubawa baiga kowa ba. Shafe fuskarsa ya kumayi yana jin duk tunaninsa ya k’are. Bai samu coin d’in ba hakan yasa ya fito yai sallama da Musaddiq. Bai tsaya jiran Daddy ba ya nufi gida dan yanada abubuwan yi da yawa. Bincike ne da yake so yayi kan mutuwar Maleeka wanda baya so yai involving kowa ciki harda abokan aikinsa. ** Ta gama jera komai saman dining table tana jiran zuwansa. Saida ta k’ara tsala wanka ta shirya cikin wata riga off neck ruwan d’aurawa wanda ta tsaya daidai cinyarta. Tayi kyau sosai kaman ka sure ka gudu. Ta k’araso kan kujera tai kwanciyarta tana bud’e shafukan zumunta dake cikin wayar nata. Facebook taje ta duba account d’in k’awarta Sabeera ko zataga ta amsa mata sak’on da ta tura mata tun kwanaki amma shiru bata amsa ba ga wayar Sabeeran sam ya daina shiga. Ta lumshe idanunta tana addu’an Allah yasa da rabon su sake had’uwa da Sabeera. Tana nan a kwance taji k’aran bud’e masa k’ofa. Ta mik’e da sauri ta k’arasa jikin window tana lek’ensa. Murmushi saman fuskarsa take dubansa. Har ya ida rufe motar nasa waya mak’ale kunnensa na hagu. A ranta tace sarkin waya ba, shi ko gajjiya bayayi.. Gashi a zahiri baida hayaniya baida yawan magana amma idan abinda ya shafi aiki ne tana tsammanin zai iya kwana yana waya. Ya turo k’ofar ya shigo yana mai k’are mata kallo dan Ta masa kyau sosai. Sauri sauri yai rounding wayar nasa kafin ya bud’e mata hannaye alamun ta taho. Aiko nan ta taho a guje Ta haye cikin jikinsa. Cak ya d’agata kaman wata baby yana juyi da ita. Ya mak’aleta tsam cikin jikinsa yana fad’in tayi kyau. Ta d’an rufe idanunta da tafukan hannayenta tana murmushi. Hannayensa yasa ya cire nata hannayen daga saman fuskarta yana kuma tsareta da rikitattun idanunsa. Hannayenta cikin nasa suna fuskantar juna yake fad’in “Beautiful bazaki daina rikirkita mun lissafi a gidan nan ba. Naga alama yanzu ke kike bani Assignments d’in
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243