Chapter 50
Chapter 50
da gashi.. Aci gaba da kid’a aci gaba da juya mazaunai wacce batadashi haushi ya kasheta.. Ahayyee yiririri nanaye sama mataaa..!” Ta k’arashe tana mai juyi da baya. Cikin zuban hawaye Sadiya ta fito zata janye mahaifiyarta aiko nan Tabawa ta fincikota ta jefata tsakiyar fili suna rawa suna zagayeta.. Duk’awa tai wajen tana kuka mai ban tausayi tana rok’onsu su fice masu daga Gida suji da abinda ke damunsu amma kaman cewa take su k’ara. Umma ta isa ta janye d’iyarta suka koma gefe suka rungume juna suna hawaye, Azo har gidansu afi k’arfinsu sabida kawai basu dashi. ** A can gidan Alhaji Isyaku kaw yaci uban wanka yasha gayu cikin sabuwar d’inkin babbar rigarsa, yadai zuba shiga irinta angwaye sai zuba k’amshi yake bakinsa har kunne sabida Farin ciki. A haka ya fito ya tadda Maman Sabeera da Sabeera a parlor sunyi jigum jigum hawaye saman fuskar Sabeera dake kwance cinyar Mamanta. Kallo guda ya masu ya wani d’auke kai irin ko a jikinsa. Maman Sabeera ta mik’e ta nufesa “Alhaji Wai yanzu dan Allah bazaka fasa auren yarinyar nan ba..? Fisabilillahi yarinyar nan fah ‘yar cikinka ne..” Katseta yai da fad’in “Kar ki sake cewa ‘yar cikita ce balle ki haramta min matata.. Ni ban haifeta ba bani ne ubanta ba kin fahimta..” Maman Sabeera ta goge hawayen da suka gangaro mata “Amma ko baka haifeta ba ka haifi Aminiyarta, Kai yanzu ko gudun maganan mutane bakayi kawai ka tashi ka auro mana k’awar d’iyarka aminiyarta.” “Gudun magana.? Toh waye yake sauraron maganganun mutane.. Ai bari kiji Rahina Idan kika ce zaki tsaya sauraren abinda mutanen duniya zasu fad’i akanki ne kina tareda babban aiki.. Ke bari kiji na fad’a miki babu uban da ya isa ya hanani Auren Sadiya.. Ko Ubanta ne ya taso daga kabari bai isa ya hana auren nan ba.. Matsa ki ban waje kar Malam Liman suyita jirana an had’a mutane a masallaci.. Shirirtar banza da wofi.” Ya k’arashe yana bangajeta gefe. Maman Sabeera ta fad’i nan k’asa wajen tana mai sakin kuka tana kiran mijinta ko kulata baiba ya sunkumi bak’ar leda wanda kud’ad’en da zai biya bashin Sadiya da mahaifiyarta ke ciki.. Sabeera tuni ta K’araso ta duk’a ta rungume mahaifiyarta su duka biyun suna masu sakin kuka mai ban tausai. Yana fitowa daga gidan nasa ya shiga aza babbar rigarsa shi kad’ai ya nufi motarsa dan dama a waje hai parking d’inta, Baba Mai gadi yace dashi a dawo lafiya.. Baban Sabeera yana shiga Mota sai gani yai wasu k’artan maza guda uku fuskoki rufe da bak’ak’en masks sun bud’e motar suma sun shigo.. Cikin tsananin firgici da tsoro Baban Sabeera ke fad’in “A’a.. A’ah su waye ku.. Mai nai maku..? Dan Allah kar ku cutar dani.. Wllhi nid’in Sabon ango ne yau ake Bikin aurena.. Dan Allah Kuji tausayi na kar ku cutar dani..!” Yai maganar hularsa tana karkacewa hannayensa rok’onsu dasu sai rawa suke. Wanda yake zaune a backseat ya buga ma Alhaji Isyaku k’asar bindiga a k’eyarsa yana fad’in “Shut up.! Rufe mana baki and keep on driving..!” Jiki na matuk’ar rawa Alhaji Isyaku ke tuk’a motar, a haka har suka fice daga layin. Sun d’auki hanyar barin gari kenan motar dake bayansu tasha gabansu, lokaci guda suka firfito daga cikin motar suna pointing d’insu da bindigogi suke fad’in “This is the police, freeze..!” Tuni suka soma bata kashi da mutanen da suka kira kansu ‘yansanda wanda suma ba kayan ‘yansandan bane jikinsu da kuma mutanen da sukai abducting Alhaji Isyaku. D’aya gardin ya finciki ledar kud’in Alhaji Isyaku suka ci gaba da harbi tsakaninsu da ‘Yansandan kafin suka nufi daji a guje.. D’aya D’ansandan yai k’ok’arin bin bayansu yayinda d’ayan ya k’arasa wajen Alhaji Isyaku dake duk’e hannayensa ta bayan kansa ya kifa Kan nasa Sai b’ari jikinsa yake sabida tsaban tsoro da hargitsin Bindiga da yaji ya kuma gani. D’aya daga ‘yanta’addan ya harbi D’asandan da yabi bayansu a hannu wanda hakan yasa dole ya dakata da bin ‘yanta’addan ya dafe hannunsa dake fitar da jini yana cije baki. A haka ya dawo wajen d’aya D’anuwan nasa da Alhaji Isyaku dake duk’e wajen. Alhaji Isyaku ya d’ago yana dubansu yana fad’in “Na gode na gode maku.. Kun ceceni hannun ‘yanta’addan nan.. Wllhi nid’in sabon ango ne yau ake d’aura aurena. Muyi sauri Mu k’arasa Amaryata da Malam Liman suna jirana, dikda B’arayin nan sun sace kud’ad’en zansan yanda zan nemo wasu kud’ad’en..” Kafin yai shiru d’aya mutumin cikin wanda sukai acting kaman ‘yansanda suka kuma taimakesa ya murmusa yace masa “Not too fast Alhaji..!” Yana ida fad’in haka ya buga ma Alhaji Isyaku k’otar bindiga a k’eyarsa. Tuni Alhaji Isyaku ya fad’i sumamme. Nan take suka jefasa cikin motarsu sukai tafiyarsu. ** Tun su Malam Liman suna jira har dai suka gaji da jira, Tun ana k’irga mintoci hardai aka koma k’irga awanni, babu Alhaji Isyaku babu dalilinsa, su Tabawa kaw ana can gidansu Sadiya ana tik’an rawa. K’arshe Malam Liman ya dubi ‘yan committee na masallaci yana basu hak’uri kan rashin zuwan Alhaji Isyaku da ya tarasu a wajen nan ya kuma sab’a alk’awari.. Malam Liman yaci gaba da fad’in “Mai yuwa ya canza shawari ne bazai iya biya masu wannan tsugugun kud’ad’en matsayin bashi ba.. Yanzu bansan mai zance wa yarinyar nan da mahaifiyarta ba.. Bansan mai zan sanar dasu ba domin kaw mahaifiyarta ta damk’a min ragamar auren yarinyar a hannuna matsayin awalinta.. Bayin Allah Kuji tausayin wad’annan bayin Allah ku biya masu wannan bashi zaku sama lada wajen Ubangijin..” Shiru babu wanda yakeda wad’ann tsugugun kud’ad’e, babu wanda zai iya biyan wad’annan kud’ad’e.. Kud’i ba naira dubu ba wuri na gugan wuri har Naira Miliyan d’aya da rabi.. Nan fah mutane suka soma k’ok’arin watsawa daga masallaci Liman na k’ok’arin dakatar dasu ko Allah zaisa Alhaji Isyaku ya canza shawari yazo ya biya masu bashin nan.. Ana tsaka da watsewa Malam Liman ya mik’e yana fad’in “Bayin Allah ku dakata.. Ku dakata Kuji tausayin na k’asa daku idan akwai mai kud’ad’en nan ya taimaka ya biya bashin nan.. Shin babu wanda zai iya sauk’e nauyin bashin nan..?” Kaman daga sama Malam Liman yaji wata murya “Akwai wanda zai biya bashin..!” A tare Liman da ‘yan tsirarun da suka rage a masallacin suka juyo suna duban mutanen da suka shigo cikin masallacin. Wani matashi ne sanye da bak’ak’en kaya suit fuskarsa rufe da bak’in glasses saidai suna shigowa harabar masallacin saurayin ya zame glasses d’in dake mak’ale idanunsa fuskarsa Ta bayyana, taredashi wani mutumi ne wanda shi ya d’an manyanta sannan manya kaya ne sanye jikinsa shi. Cikeda tsananin mamaki Assad dake zaune wani b’angare a harabar masallacin ya b’adda kama yana monitoring duk abindake faruwa cikin masallacin gameda auren Sadiya da Alhaji Isyaku kaman dai yanda Mu’azzam ya saka sa, ya mik’e in a shock yana duban Mu’azzam da sam baisan yaushe ya iso garin ba. Assad ji kawai yai bakinsa na furta “Unbelievable.!! You.. Are.. Unbelievable.. Mu’azzam Gamji..!” Mu’azzam da Uncle Salman suka ci gaba da takowa cikin masallacin a natse, suna K’arasowa suka mik’a ma Malam Liman hannu sukai masabaha. Malaman Liman ya koma ya zauna yana nuna masu waje cewa su zauna suma. Uncle Salman a Mu’azzam
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243