Chapter 231
Chapter 231
Aleeyou...✍🏽* A haka mutumin yake k’arasowa cikin parlorn Sallama saman bakinsa. Muryar mutumin Baida banbanci dana mahaifinsu musamman kafin girma ya riski mahaifinsu. Uncle Salman ne ya iya samun zarafin k’arasawa ya mik’a masa hannu sukai masabaha Daddy kam mamaki ya kasa sakinsa ganin fuskar Mahaifinsa tsaye gabansa. Take mutumin ya soma gaida mutanen dake wajen, Mu’azzam ya k’araso Shima sukai masabaha yana hango kamannin Kakansa a tareda mutumin. “Jauro..!” Inne ta furta tana dubansa lokaci guda tana nunasa da hannunta dake matuk’ar rawa. Mutumin ya dubeta Sai yai murmushi ya girgiza kai “Sunana Ramadan ba Jauro ba..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Allah yasa nan ne gidan Alhaji Marwan Gamji..?” Sai sann Daddy ya samu zarafin jinjina masa kai yana mai nuna masa wajen zama “Bismillah.. Ga wajen zama.. zauna ni ne Marwan Gamji..” Kafin ya kaiga zama sai ganin Inne sukai ta duk’o gaban mutumin tana kuka tana fad’in “Ka yafeni.. Ka yafeni.. Wllhi kai jikinshi ne.. Wllhi kai d’ansa ne.. Fuskar nan tasa ce.. Dan Allah ka yafeni Bawan Allah ni ce na rabaka da mahaifinka.. Na tabbata kaine d’an Harira da Ta fice Ta tafi da cikinka..” Gaba d’aya jikkunansu sukai sanyi ganin abinda Ke faruwa. Cikin tsananin sanyin jiki mutumin ya kamo Inne yana fad’in “Dan Allah ki daina.. Kar ki duk’a gabana.. Nida mahaifiyata mun yafeki..” Yai fasali sanda shima ya duk’a gabanta. Lokaci guda ya d’ago yana dubansu “Tabbas ni d’in d’aya ne daga cikinku amma banzo nan domin na amsa sunan ahalinku ba.. Nazo nan ne domin na tafi da d’iyata wacce aka tabbatar min tana nan a nan..” Da tsananin mamaki suke dubansa. Daddy ya girgiza kai yace “D’iyarka kuma..? A nan gidan..?” Mutumin ya jinjina kai yace “K’warai d’iyata Jiddah..!” Ganin basu gane ba sai kallon kallo suke ya sanyasa sakin murmushi kafin yace “D’iyata Ajidde wacce Kyallu ta rabani da ita..” Sai snn Aunty Nuratu ta girgiza kai tace “Ajidde.. Ta ya ka zamto mahaifin Ajidde..?!” Ya jinjina kansa kafin ya soma fad’in “K’warai Ajidde d’iyata ce wacce Kyallu ta rabani da ita da kuma mahaifiyarta..” Mamaki ya cika illahirin mutanen dake parlorn. Ciki harda Mommy dake duk’e nan wajen wacce ake shirin tafiya da ita station. Mu’azzam ya shiga nanata sunan Ajidde cikin kansa dan yama rasa wacece ma Ajidden.. Kai wann wani irin Al’amari ne daga wann sai wancan. Abubuwan al’ajabi dai bai k’arewa a wann ahali nasu. Wajen zama Daddy ya nuna masa kafin ya mik’e ya zauna. Kowa ya zuba masa idanu alamun ana jira aji yanda al’amarin ya kasance. Saida yai gyaran murya wajen ya kuma yin tsit kafin ya soma fad’in “Da farko dai sunana Ramadan.. Mahaifiyata mai suna Harira ta haifeni a wani gari dake can gabacin jihar Kaduna. Tinda ta haifeni sai ta tafi ta barni tareda mutanen da Ta zauna wajensu na d’an lokaci. Akai sa’a mutanen masu dattako ne da sanin ya kamata.. Koda aka wayi gari mahaifiyata ta tafi ta barni sai suka kula dani suka rik’eni amana har na kawo girma.. Tinda na taso sai kowa ya hanani aure a garin sabida a cewarsu babu wanda yasan asali na.. Mahaifiyata yada zango kawai tai ta haifeni ta k’ara gaba. Hakan yasa Iyayen rik’ona suka bani auren d’iyarsu wacce Ita kad’aice d’iyarsu mace sauran maza ne. Bayan na auri Hauwa muna zaune Ina tab’a kasuwanci na dan dama tinda na taso nakeda zafin nema da buga can buga nan.. Muna nan a haka muna zaune da Hauwa Allah bai bamu haihuwa ba tsawon shekaru.. A haka dai har na d’auki Hauwa tare dani muka taho cirani yanda muka yada zango a wani gari mai Sunana Fufore can jihar Adamawa. Tinda nazo garin naji hankalina ya kwanta a garin.. Naji Ina matuk’ar k’aunar zaman garin ba tareda nasan cewa wann garin shine Tushena da asalina ba. Muka had’u da wata mata a kasuwa mai tallan magani mai suna Kyallu.. Kyallu sai ta bani masauk’i Nida iyalina.. Ashe tinda Kyallu ta k’yalla idanu akaina sai ta apka soyayya na.. wann dalili ma yasa ta bamu masauk’i.. Muna zaune nida matata Hauwa a nan gidan Kyallu mai warka warka tamkar dai muna a GIDAN ARO. Kyallu tace zata bawa Hauwa maganin haihuwa tinda ta fuskanci bata haihuwa, sai muka nuna rashin amincewarmu daga ni har Hauwa tinda munsan haihuwa abu ne wanda Allah Ke baiwa wanda yaso a lokacin da yaso. Kyallu dai bata janye kudirinta na cewa zata bamu magani ba, dan muna ganin masu amsar magani suna shiga da fice a gidan Kyallu.. A haka ta dinga hure wa Hauwa kunne ba tareda munsan cewa Hauwa na d’auke da juna biyu ba ma ashe.. Hauwa ta soma amsar tayin maganin kyallu a b’oye ba tareda tasan cewa tuni tanada juna biyun ba.. Koda na fahimci tana amsar maganin Kyallu raina Sai ya b’aci nace da ita zamu tattara mu tafi.. Kyallu taita magiya tace na tsaya na gani idan maganinta baiyi aiki ba Ta yarda na d’auki matata na tafi.. Hauwa ma ta nuna damuwarta na cewa saidai mu tsaya.. Nan kuwa Rahmatu ta fara nuna alamomin masu juna biyu.. Kyallu tace maganinta ne ya soma aiki.. Nace atafau ba maganinta bane domin kuwa ita bata isa ta saka ko ta hana ba.. Iko ne na Allah. Sann idan ma maganin nata yayi aiki ta sani ba yinta bane Allah zai iya nuna k’udararsa da isarsa ya sanya maganin nata yayi aiki domin yaga zatai imani ko zata tab’e. A haka na dinga k’ok’arin nusar da Kyallu tauhidi amma sai tai k’ememe tak’i d’aukan wa’azin da nake mata. Ni kuma na kasa barin garin na kasa d’auke matata mu tafi ba tareda nasan dalili ba.. Sai na alak’anta hakan da cewa Watak’ila Allah ya nufi nazo garin ne domin na had’u da wann mushirikar matar mai suna Kyallu nai mata wa’azi ko zata wa’aztu.. Tafiya yayi tafiya har lokacin haihuwar Hauwa yai wanda zai kuma tabbatarwa Rahamatu tanada juna biyu muka taho garin ba maganin Kyallu bane yai aiki, domin kuwa bamu cika watanni tara a garin ba Ta soma nak’uda.. Kyallu ita ta amshi haihuwar Hauwa yanda muka rasa Hauwa a wajen haihuwa. Ta haifo d’iyarta mai kama da ita na maida mata sunan Hauwa (Jiddah).. Nayi kukan rashin Hauwa dan bansan mai zanje na sanar da iyayen Hauwa ba.. Na yanke shawarin d’aukan d’iyata Jidda na tafi da ita, amma sai Kyallu ta dage saidai na zauna na aureta mu raini jidda tare.. Ni kuma Sai nak’i aminta da hakan.. Kyallu sai ta rik’e Jidda tace bazata bani ba.. A ranan taita min kururuwa ta had’a mun mutane tace ni b’arawo ne zan sace mata d’iya.. Inaji ina gani Kyallu tasa aka mun korar wulak’anci a garin Ta kuma goye d’iyata a bayanta Ta hanani d’iyata ta bini da sharri cewa d’iyarta ce nida ita munyi aure zan d’auketa ne na gudu na shiga duniya da ita. Kuma wani ikon Allah ban iya aiwatar da komai akai ba bansan wani k’ullin Kyallu tai akaina da d’iyata ba. Koda na dawo gida na sanar da iyayen Hauwa cewa mun rasa Hauwa sai sukai tawakkali amma na kasa sanar dasu abinda ya samu d’iyarmu da Hauwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243