Chapter 11
Chapter 11
zai iya wulak’anta Safeenah, koda ace baya sonta zaiyi hak’urin zama da Ita.. Mommy da Daddy sun cancanci ya rik’e masu d’iya da amana..Alk’awari ne da ya d’aukar ma kansa.. Muryar Inne ya sinkayo tana ci gaba da fad’in “Jinya yak’i ci yak’i cinyewa.. Idan ban b’ata lissafi ba yau a k’alla kusan shekaru shabiyar kenan Nuratu na fama da jinyar nan, ni ban tab’a gani ko jin had’arin mota irin nasu ba..” Mu’azzam ya d’ago yana dubanta “.. Ina makarantar Kwana a lokacin, aka sanar dani Mamy ta auri Uncle Marwan saidai a hanyarsu Ta tafiya Abuja daga Adamawa sunyi accident.. She survived the accident amma tana cikin critical condition.. Condition d’in da bata fice daga ciki ba har rana mai kaman Ta yau.. Ance motar da Mamy na take ciki kowa ya mutu ita kad’aice tayi rai a ciki..” Ya k’arashe cikin yanayi na ban tausayi. Sauk’e ajiyan zuciya Inne tai tana mai d’an goge hawayen da ya mak’ale mata cikeda tausayin Mu’azzam d’in.. “Modibbo ina k’aunar Mahaifiyarka tamkar d’iyar dana haifa a cikina wannan dalili yasa na umarce d’anuwan mahaifinka da ya aureta bayan da muka rasa mahaifinka... Ina tsananin k’aunarta kuma bana so ta bar cikin ahalinmu.. Nuratu yarinyar kirki ce mai tsananin biyayya.. Da ita da Baffanka Marwan sunyi min biyayya kuma Sun cika min burina sun amince da auren juna.. Saidai bansan wannan aure haka zai kasance ba.. Bansan a hanyar zuwa GIDAN Baffanka Nuratu zata had’u da wannan mummunan tsautsayi ba.. Ance had’arin motar bama irin wacce aka saba gani bane.. A samar bishiya aka tsinci motar da mahaifiyarka ciki... Mu’azzam inaji kaman alhakin ciwon mahaifiyarka a kaina yake.. Watak’ila da banyi masu umarni da su auri juna ba itada Marwan da yanzu lafiyarta lau.. Bazan daina jin zafin abun nan ba har na koma ga mahaliccina..” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka. Cikin sauri Mu’azzam ya taso ya duk’a gabanta, ya kamo hannayenta ya dunk’ule cikin nasa “Inne none of this is your fault.. Ki daina d’aura ma kanki alhakin ciwon Mamy, wannan wani abu ne da Allah ya K’addara.. Mutum baya shige k’addarar Sa a rayuwa.. Wani baya iya yi ma wani abin cutarwa ko na amfanarwa face Allah ya k’addari faruwar hakan,.. Baki nufi Mamy da komai ba face Alkhairi. Had’ari kuma ko ta auri Uncle ko bata auresa ba tuni Allah ya rubuta hakan zai faru.. Ki daina d’aura laifi ma kanki kinji Inne..” Ya k’arashe yana mai goge hawayen fuskar Kakar tasa da ‘yan yatsunsa.. Ta Shafa sumarsa murmushi saman fuskart “Allah shi maka albarka Modibbo na.. Ubangiji ya maka jagora a duk abinda kasa gabanka.. Allah tsare mun kai ya kareka daga sharrin mai sharri..” Sumbatar hannayenta dake rik’e cikin nasa yai yana furta “Ameen Inne na.. Allah ya bar mun ke..” Ya k’arashe yana mai d’aura kansa saman cinyarta.. Dik zafin da zuciyarsa Ke ciki idan yana tareda Kakar tasa Sai ya dinga jin wani sanyi can k’asar zuciyarsa, har wani shagwab’a yake mata, ga wanda yasan zafin sa a waje idan ya gansa da Innensa sosai zaiji mamaki.. Daga wajen Inne Kai tsaye wajen mahaifiyarsa ya nufa... SameenaAleeyou📚 *GIDAN ARO* *05* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ya jima tsaye bakin k’ofa yana dubanta, yana mai tina tattaunawarsu da Inne. A hankali ya soma takowa cikin d’akin har ya k’araso bakin gadon da take kwance.. B’angaren da fuskarta yake duba ya k’arasa, ga duk’a kad’an yana mai k’ura mata idanu.. Su kuma kalan tasu k’addarar kenan.. Da fari mahaifinsa ya rasa sannan mahaifiyarsa ta had’u da tsautsayi na jinya yanzu ga tilon k’anwarsa itama ta tafi.. Tinani yake lokacin ahalinsu ke cike, Daddynsa Mamynsa da kuma ‘yar k’aramar k’anwarsa Ikram.. Ahali mai cikeda Farin ciki da k’aunar juna.. Inama wad’ancan lokutan zasu iya dawowa.. Inama zai bud’e idanunsa yaga mafarki ne duk abubuwan da suke faruwa.. Amma saidai wannan itace gaskiyar, littafin k’addararka a kullum bud’e maka Sabon shafin rayuwa takeyi.. Rayuwar duniyar kenan, duk yanda ka kaiga ganin cewa dad’i kakeji a duniyar nan toh wannan dad’in k’ayadadde ne, aronsa aka baka akwai ranan da zaka wayi gari ka rasa wannan jin dad’in.. Sannan duk yanda ka kaiga ganin wahala kake sha toh wannan wahalan yanada wa’adi akwai ranan da zai k’are.. Duniya ba gidan zama bace gida ce ta jarabawa, dik yanayin daka tsinci kanka ciki a gidan duniya toh kuwa ko shakka babu jarabawa ce kake cikinta.. Gidan duniya gidace da aka baka aronta domin a jarabceka a cikinta, ba gidan Sharholiya bace sannan ba gidan baje koli bane.. Kai d’in tamkar matafiyi ne da aka baka Aron Gida domin ka yada zango na wani d’an lokaci k’ayadadde.. Babu komai a GIDAN ARO face tarin jarabawa da kuma k’alubale na rayuwa.. Mu’azzam ya lumshe idanunsa yana mai kamo hannayen mahaifiyarsa wacce ga dai idanunta a bud’e tarau amma wani b’angaren take duba.. Bata um bata um um.. A hankali ya soma furta “Mamy inada babban albishir da zan miki.. A yau d’in na soma gano wani abu gameda mutuwar Ikram.. Kuma na miki alk’awari in sha Allah bazan gajiya ba har sai na samo bakin zaren.. Mamy na Sani addu’arki da albarkanki suna tare dani.. Fatana shine Allah ya baki lafiya ya tashi kafad’unki.. Inada yak’inin cewa wata rana komai zai wuce ya zamto labari.. Wanda sukaci zarafin d’iyarki suka kuma kasheta zasu biya.. Zasu biya abinda suka aikata Mamy.. I won’t rest until I get to the bottom of everything..” Ya k’arashe yana mai sumbatar hannayen nata dake rik’e cikin nasa had’ida lumshe idanunsa siririyar hawaye ta gangaro daga cikin idanunsa guda... Yana duk’e wajen yaji hannun mutum a kafad’arsa, sanin ko wanene tsaye Kansan ya sanyasa k’ok’arin saita kansa kafin ya mik’e yana goge fuskarsa da duka tafukan hannayensa.. “Sorry Daddy banji shigowarka..” Ya fad’i yana mai k’ok’arin mik’ewa tsaye. K’ak’aro murmushi Alhaji Marwan yai kafin ya girgiza kai kad’an yace “Babu komai Mu’azzam..” Ya kuma duban Mu’azzam d’un cikeda kulawa kafin ya maidoda dubansan ga mahaifiyar Mu’azzam d’in.. Idanunsu Su duka biyu naga mahaifiyar Mu’azzam d’in Daddy Ke fad’in “D’azu muke magana da Inne cewa tana so Nuratu ta koma Fufore.. Za’a gwada yi mata maganin gida ko Allah zaisa a dace.. Hajara ta fara mun maganar sai kuma Inne ma tazo da batun.. Toh amma a zahirin gaskiya Mu’azzam ni banyi Na’am da maganin gargajiyan nan ba.. Tinda ga abinda likitoci daga manyan asibitoci na duniya suka fad’i.. Zai matuk’ar wahala ta warke a bisa iya binciken da sukayi..So ina tunani kar aje a shiga bata wasu magunguna da babu dosage ba likita bane yayi prescribing aje a k’ara rikita jikin nata.. Toh amma kuma sai nayi tunanin likitocin nan ba sanin gaibi sukayi ba.. Cuta Allah Ke sakashi kuma shi Ke yayewa, saidai yakan bama wasu daga cikinmu ilimin sanin magani domin kuwa bai halicci cutan ba har saida ya sauk’ar da maganinta.. Ba Lallai sai ta hanyar likitoci wanda sukayi karatun ilimin zamani ba.. Wani dake rayuwa cikin daji ma sai Allah ya basa ilimin sanin magunguna a kumayi amfani dashi idan Allah ya nufa sai a dace...Amma Kai mai kake gani..” Shiru Mu’azzam ya d’anyi kaman mai nazari kafin yace “Haka ne Daddy..Abinda ka fad’a gaskiya ne.. And
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243