Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 120

Chapter 120

Gidan Aro Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fuskarta cikin dressing mirror.. Ta kuma tambayar zuciyarta.. Sai kuma ta rintse idanunta cikeda tsoron ansar da Zuciyar nata ke bata.. Ta k’ura ma fuskarta idanu cikin mirror kafin tace “Are you messing with my heart now Mr Inspector..?” Cikin sauri ta lumshe idanunta tana jinginuwa jikin gini. Aunty Larai dake lab’e bakin k’ofa tana dubanta murmushi saman fuskarta, a hankali tai knocking da yatsarta guda. Sadiya tai saurin tattara natsuwarta tana kintsa kanta. Aunty Larai ta shigo sallama saman bakinta, hannunta rik’eda had’in Kankana.. “Maza Zo ki shanye wann..” Ta fad’i tana zama gefen gado. Sadiya ta d’anyi rau rau da idanu dan kusan kullum Aunty Larai da irin had’in da take bata. Ta d’an dubeta kafin tace “Bari dai na miki bayanin menene a cikin wanann.. Kinga akwai Kankana K’wallo d’aya sannan sakwai sabuwar tsamiya k’wara hud’u sannan akwai tafarnuwa curi d’aya.. Ita Kankana tanada tasiri jikin ‘ya mace sannan tsamiya magani ce itama.. Tafarnuwa kuwa Antibacterial ne.. Duk wata cuta da ta shafi mara tana maganceta.. Yana da kyau bayan lokaci ki dinga yi ma kanki wannan had’in dan takan bada kariya daga cuta na sanyi da ya addabemu a gidajen aurenmu.. Sannan ita wann had’in ko wanda ke fama da cuta na sanyi zai iya had’awa ya dinga sha da izinin Allah za’a samu waraka. A had’asu waje guda a dafa a dinga sha safe da yamma.. Kinga ba wani abu mai cutarwa na baki ba maza d’auki ki shanye.” Sadiya ta d’auka ta kafa kanta ta shanye. Duk a kwanakin had’e had’e iri daban daban masu inganta lafiya da matantakanta Aunty Larai ta dinga bata.. Wasu Ta mata bayani wasu kaw bata mata bayani saidai ta sanyata cinyewa ko shanyewa.. Ga gyaran fata na musamman da take mata ita har Ta fara tinanin kodai had’a baki Inspector sukai da Aunty Larai shisa ya dena zuwa gidan.. Taga har alhamis Yayi babu Inspector babu batun tafiyarsu.. Abin har dai ya soma damunta gashi Aunty Larai bata fasa mata abu guda da take mata ba.. Fatarta ya kuma murjewa har wani kyalli da shek’i yake.. Jikinta ya kuma cika dan tana iya jin hakan tattare da ita.. A tak’aice ita kanta tana jin kanta Ta kuma canzawa. Idan ka kalleta dole kaso sake kallanta.. Wasa wasa saida akai kusan sati Inspector baizo gidan ba.. Ba abin Ta tambaya ba bama zata iya ba.. Idan ta zauna haka zatai ta kallon lambar wayarsa tana tinani.. Wasu lokutan ta kwab’i kanta tace k’ila ma ya mance da ita.. K’ila ma ya d’auki d’aya matarsa sunyi tafiyar.. Wannan tunanin shi yafi d’aga mata hankali.. Kardai ya d’auki d’aya matar tasa sun tafi ne tinda yace bazai kuma tilasta mata komai ba.. Maganganun Aunty Larai suka shiga zuwa mata cewa namiji baya son taurin Kai da kafiyar masifa da kuma musu, wad’ann abin sosai suke rage darajan mace wajen mijinta.. Sannan Ta bawa mijinta dama ya zamto babban abokinta kuma abokin shawarinta.. Yanzu ita da Mr Inspector Wai har zasu zamto manyan abokai irin yanda Aunty Larai ke fad’i..? Ta kuma duban fuskarta a madubi kafin zancen Aunty Larai ya kuma zuwa mata cewa Great Mission d’inta shine rayuwar aure dake gabanta, dan aure ibadah ne kuma bautan Ubangiji ne. Duk abinda Ta gani cikin gidan aure ibadah take.. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin ta isa ta kwanta hoton fuskar mijinta cikin idanunta. A ranan da yammaci Aunty Larai tazo da mai lalle Ta zana mata bak’i da ja hannu da k’afa.. Sosai k’unshi yai kyau ya amshi fatarta musamman da shike fatar tata ta d’auki gyara sosai. Idan ka ganta kaman wata sabuwar Amarya ga wani k’amshi na musamman da take duk yanda Ta gifta.. Habeeb ya dubeta yace “Aunty Sadiya kunyi kyau sosai kaman ana bikinki..” Gaba d’aya suka d’an dara Habeeb na kuma cikasu da sururtu. Kafin dare mai kitso tazo tai mata dan harta wanke kai da drying saida Aunty Larai tai mata. Safiyar Washe gari litinin Aunty Larai ta sanyata ta shirya tsaf cikin wani embroidery atampa mai kyaun gaske ruwan cikin k’wai wanda ya tafi da kalan jikinta, d’inkin riga da skirt ne da ya masifan mata kyau cikin kayyakin da su Aunty Larai suka d’inka mata a nan cikin foundation d’in. Dama tin kwanakin baya Aunty Larai ta d’au measurement d’inta ashe Mu’azzam ne ya bama Aunty Larai tai mata d’inkuna masu kyau na zamani.. Sai gani kawai tai Aunty Larai dasu Farida ‘yanmata masu koyar da sana’ar d’inki a foundation d’in suna shigo da kayayyaki kama daga laces zuwa atmapopi hardai irinsu Dubai materials d’in nan. Aunty Larai tasa Farida tai mata light makeup a fuskarta. Dik yanda Sadiya bataso ba haka dole akai mata mai sauk’i dama ita ba gwanar kwalliya ma fuska bace tin tana amsa sunan Sady pretty.. Kaidai barta da gayu ma jiki sai ka rantse d’iyar wata hamshak’i ne.. Dama bata faye fente fuska ba.. Yau d’in Sai abin ya zama na musamman abinka da wacce bata saba ba. Tayi kyau har ta gaji, Farida ta d’aura mata d’ankwalin daidai da kanta. Sai santin kyaun da ta k’ara suke.. Ita dai batace komai ba sai fad’uwa da gabanta keyi dan ko Aunty larai bata sanar da ita ba tanaji a jikinta Inspector ne zaizo, ga Umma ta kauda kai abinta bama ta saka masu baki cikin al’amaransu.. Toh kodai baiyi tafiyar bane.? Ta tambayi kanta tana duban kanta a mirror bayan an ida shiryata. Tabarakallah Masha Allah shine kawai abinda taji zuciyarta na ambata. Ta fito tsaf da ita kaman wata sabuwar Amarya. Tana tsaka da tinanin wayar ya soma ruri. Ta juya tana duban wayar kan gado gabanta na kuma fad’uwa. Tasan idan bashi d’in ba babu mai kiran wayar Dikda cewa ba da lambar da ya sanya mata ba yake kiran. Ta k’arasa a hankali hannunsa sai k’aran awarwaro yake kafin ta d’auki wayar. Bata furta komai ba daga d’aya b’angaren ta sinkayo muryarsa cikin sallama. Ta lumshe idanunta a hankali tana tinanin yaushe rabon da taji Muryarsa. Sallamar tasa ma a zuciya Ta iya amsawa. Shiru kaman babu mai kuma cewa komai. Nan ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Are you ready for your next mission..?” Murmushi ne taji yazo mata wann karon.. Sai ta d’an murmusa tana rufe fuskarta da hannu guda. Mu’azzam yaji sautin murmushin nata ta cikin waya. Shima murmushin yai kafin yace “Ki fito ina jiranki a parlor.” Daga haka k’it ya katse kiran. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana kuma duban kanta. Mayafinta kalan kayan dake aje saman gado ta d’auka ta yafa kaman mai tsoron ganinsa ko kuma wacce basu tab’a had’uwa ba haka nan taji.. Ta kasa fita saima komawa da baya da tai tana sauk’e ajiyan zuciya a hankali. Kusan minti biyar ta kwashe kafin ta daure ta fito cikin taku a tsanake. Tin daga nesa yake dubanta dan musulmin k’amshin da take ne ma ya soma yima k’ofofin hancinsa sallama. Cak ya daina shafa wayar da yake ya mik’e tsaye yana dubanta sanda take k’arasowa. K’afafunsa ta fara hangowa itama nan ta fahimci yau d’in shigar manyan kaya yayi.. Ta d’ago idanunta a hankali tana dubansa. Jampa ce jikinsa kalan ruwan k’asa sai hularsa

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});