Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 128

Chapter 128

Gidan Aro Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

murmushi ya saki da gefen bakinsa still idanunsa akanta.. Bata ida zame jikin nata ba taji ya kuma juyar da ita ya rungumeta ta baya.. Bugun zuciyarta ya k’aru.. Ta lumshe idanunta a hankali.. Cikin rawar murya take fad’in “Dan Allah kayi hak’uri.. Aike na fah akai.. Yanzu idan aka shigo aka ganmu haka fah.? Tamkar zata fashe masa da kuka haka tai maganar. Hab’arsa ya d’aura kad’an saman kafad’arta guda yana kuma shak’an daddad’an k’amshin dake tasowa daga cikin jikinta, idanunsa a lumshe yake furta “This is my grandma’s room babu mai shigowa..” “Toh idan Inne ta shigo fah..?” Ta kuma fad’i kaman zatai kuka. Hannunsa taga ya mik’a saman switch na wuta ya kashe wutan d’akin. Cikin tsoro take furta “Na shiga uku.. Inspector what are you doing..? Dan Allah ka barni naje zasu gaji da jirana..” Bai bari takai aya ba ya rufe bakinsa da nata.. Wata rayuwa ce da bata tab’a tsintar kanta ciki ba, tsantsan k’aunarsa yake nuna mata wanda bata tab’a koda hasasho su biyun a irin wannan duniyar ba. Saida ta sakar masa kuka kafin ya k’ok’arta ya saketa. Ya kunna switch d’in wutan yana dubanta yanda take share hawayenta. Hannayenta ya kuma janyowa kafin yace “Ke kikace kar a ganmu shisa na kashe miki wutan.. Kuma na mance you are afraid of the dark..” Ta d’an dubesa kad’an kafin tasa kai zata shige.. Yai saurin kamota yana fad’in “Wait tsaya mana.. Kinyi fushi ne..? Idan kika fita haka Inne zata fahimci mai kika tsaya yi a d’akinta gwara ma ki sake wann fuskar taki..” Ta mak’ale kafad’a ba tare tace komai ba still baki a ture. Ya d’an kauda kai kad’an yana murmushi kafin ya maido da dubansa gareta “Ok tell me meye aikan sai na kaiwa Inne kar Ta ga fuskarki da hawaye..” “Idan ma Ta gani zan fad’a mata abinda kayi ne.. Kuma ma ai ba kai ta aika ba..” Ta basa amsa kai tsaye. Sosai ta basa dariya amma sai ya d’an gimtse yace “Ok shikenan.. D’auki aikan ki kai mata ina jiranki a nan zamu je ki gaisa da Mamy..” Ya k’arashe yana mai fitowa Parlorn Inne. Zama yai nan kan kujera yana jiranta. Yayinda Sadiya ta k’arasa ma’ajiyan kayanta jiki a sanyaye jin yace zasuje ta gaisa da mahaifiyarsa. Har Ta fita ta kaiwa Ajidde kayan yana nan zaune saman kujera yana duba wayarsa. K’afarsa d’aya bisa d’aya. Sarai yaji dawowarta amma yai kaman baiji ba. Tai tsaye gefe tana jiran mai zaice, shiru baice komai ba.. Ta d’an Langab’e kai kad’an cikin zuciyarta tana fad’in mai hali baya canzawa. Bata ida tinanin ba taga ya mik’e yana zira wayarsa a aljihu. Ya d’ago yana dubanta sai ta sadda nata kan k’asa. Hannunta guda ya kamo ba tareda ya furta komai ba, nan ta shiga bin bayansa kaman rak’umi da akala. Tin daga k’ofar d’akin take jin bugun zuciyarta na ninkuwa.. Wani irin yanayi mai kaman tausayi had’ida rauni sun taru sun cika zuciyarta. Tasan mahaifiyarsa batada lafiya amma bata tab’a ganin yaya jikin mahaifiyar tasa yake ba. A hanya suka had’u da Mama Hindu tana fitowa.. Suka gaisa da Mu’azzam yana tambayarsa mahaifiyar tasa. Mama Hindu tace tana ciki yanzu ta ida mata shirin bacci. Ya jinjina kai kafin ya kuma janyo hannun Sadiya suka shige. Fuskar matar ta soma hangowa kwance saman gado, Fuskar tata tayi Haske sosai irin na wanda ya jima yana jinya. K’afafunta a mimmik’e gwanin ban tausayi.. Baka ganin komai a fuskar nata sai dogon hanci da kwarmin idanuwa alamun jinya Yaci rabonsa.. Ya Allah ka azurta majinyatanmu da lafiya ka k’ara mana lafiya da zaman lafiya a cikin al’umman musulmi. Hawaye ne taji sun ciko idanunta tab.. Ta tina cewa wannan matar da take kwance babu abinda take nema face lafiya.. Da za’a ce ta bada komai nata dan ta sami lafiya zata bayar.. Ina kai da kake da arzikin lafiya shin mai ka aikata da wannan lafiya da Ubangijinka ya baka..? Shin ka tab’a tambayar kanka lafiyar nan zuwa wane lokaci aka ara maka..? Shin ka tab’a hisabi ma kanka cewa mai ka aikata da wannan ni’ima na lafiya da Ubangiji ya baka..? Shin kasan mutane nawa ne suke buri da fatan su sami lafiya irin naka domin Su bautawa mahaliccinsu da ita.. Allahu Akbar Tabbas Lafiya itace babbar arziki da Allah zaiyiwa Bawa, kuma babu arzikin da ya kaita.. Ina kake mai kukan Allah bai baka arzikin gidan duniya ba, ka sani idan Allah ya baka arzikin lafiya ya gama baka babban arziki wanda mutane da dama Sun saka arzikinsu domin su sameta kuma basu sameta ba. Ina kake mai burin tara abin duniya ka sani idan babu lafiya arzikin da ka taran ma bazaka ji dad’inta ba..Lafiya uwar jiki aka ce babu mai fushi dake.. Idan an d’auke maka ita jarabawa ne.. Haka idan aka Barka da ita duk cikin jarabawa ne.. Allah ka bamu jarabawar da zamu iya ci a rayuwa Ameen. Muryar Mu’azzam Ta sinkayo yana furta “Queen Mother.. She’s my Mum.. My Mamy.. My sunshine.. My Happiness.. My everything..!” Ya d’an sassauta muryarsa kafin yaci gaba da fad’in “Na rasa jin kalamanta masu taushi da dad’in sauraro sama da Shekaru goma sha biyar.. Kunnuwana sun d’auki lokaci mai tsawo basu jiyo albarkan da take saka ma rayuwata ba..” Ya d’an murmusa kad’an still idanunsa akan mahaifiyarsa kafin yace “Do you know, my Dad used to say she cooks the best food.. Sann tanada kalamai masu taushi da zak’i saman harshenta..” Muryarsa ya d’an sark’afe yana k’ok’arin maida k’wallan dake k’ok’arin ciko idanunsa.. “Nayi kewarta sosai.. In fact nayi kewar ahalinmu sosai.. It seems ni kad’ai nai saura cikinsu.. Babu Daddy babu Ikram.. And Mamy tana nan ne tamkar da bata nan.. tana kwance cikin jinyar da Batasan a yanda take ba shekaru goma shabiyar.. An gwada magunguna da dama amma Allah bai mufa za’a dace ba..But Alhamdulillah ala kulli halin shine abinda zamu ce.!” Ya k’arashe yana mai d’aura hannunsa guda saman na mahaifiyarsa. Sadiya ta saka mayafinta ta goge hawayen da suka zubo mata cikeda tsananin tausayinsa. Tabbas idan kaga mutum kar kayi garajen yi masa hukunci dan baka San mai yake going through a rayuwa ba. Watak’ila matsalar da yake fuskanta bazaka iya d’aukan kwatankwacin sa ba idan aka aza maka. Ji yai hannunta guda ya sauk’a saman nasa hannun dake d’aure kan na mahaifiyarsa.. Ya dubi hannayen nasu d’aya bisa d’aya. Nasa saman na mahaifiyarsa saiko na matarsa sadiya da ta aza saman nasa hannun. Ya d’ago yana duban fuskarta da hawaye ke gangarowa. A hankali ta soma fad’in “Allah baya d’aura ma rai abinda bazata iya ba. In sha Allah zata sami lafiya.. Kar ka yanke tsammani daga rahamar Ubangiji kaji.. Da izinin Allah zata sami lafiya ta zamto Tamkar bata kwanta jinyar nan ba.. Muyi fatan jinya ya zamto mata kaffaran kura kurai kaji..!” Tana maganar hawaye na gangaro mata cikin yanayin muryar mai tsananin rauni. Ya jinjina mata kai a hankali yana mai sakin murmushi “In sha Allah..!” Ya furta yana duban idanunta kafin ya d’ago d’aya hannunsa ya shiga goge mata hawayenta. Yana goge mata hawayen yake fad’in “Kinsan cewa itace sanadiyar had’uwarmu..?” D’an duban fuskarsa tai

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});