Chapter 20
Chapter 20
ta bud’e baki tace “Officer idan kuka sami wannan mutumin zaku k’yalemu..?” Assad ya dubeta kad’an yace “Kinga mutumin ne..?” Jinjina masa kai tai kad’an tana furta “ Eh na gansa kuma zan iya ganesa.. A tsakar gidan nan sukai magana da Abba ni kuma ina lab’e kitchen ina hangensu.. Zan iya gane kamanninsa...” Jinjina kai Assad yai yana mai zira hannayensa cikin aljihu “Da kyau, yanzu zaki bimu can ofishinmu dake headquarters, akwai masu ilimin zana kamanni cikin bayanan da aka masu wanda su aikinsu kenan.. Zamuje ofishinmu tareda ke zaki masu bayanin kamannin wannan mutumin su kuma zasuyi sketching d’insa..” Sadiya jin ance zaa tafi da ita police station ya sanyata zaro idanu waje tana duban mahaifiyarta “Umma Wai tafiya dani zasuyi..?” Maleeka da kanta ke kife tana rubutu cikin wata ‘yar k’amar littafi mai yanayi da jotter d’agowa tai Ta dubi Sadiya tace “Kar ki d’aga hankalinki ba tsareki za’ayi a can ba, wasu tambayoyi kawai zaki amsa mana sai kiyi bayanin wannan mutumin..” Assad ya murmusa kad’an ganin yanda tsoro ya cika Sadiyar yace “Ki daina tsoronmu.. Police are your friends kinji koh.. Had’in kanki kawai muke buk’ata domin mu cire gurb’atattu cikin al’umma..” A hankali Sadiya Ta jinjina kai har lokacin tsoro bai bar saman fuskarta ba.. Umma Ta matso da sauri tace “Rankaidad’e dan Allah zan iya raka d’iyata.. Dan Allah ku taimakeni ku barni na tafi tareda d’iyata..” Shiru Assad yai yana dubanta kafin ya jinina Kai a hankali yana mai nuna masu yanda motar take pake.. Gaba d’aya suka d’unguma suka tafi police headquarters.. Zuciyar Sadiya sai tsinkewa take, ta d’aga idanu tana duban dogon ginin.. Oh yau kuma Ita Sadiya ce a ofishin ‘yansanda, abinda takeji take kuma ganina finafinai sai gashi yau yana faruwa da ita.. Tabbas a rayuwa kar kayi ma k’addaran wani dariya domin bakasan da mai gobe zata Zo maka ba.. Tana ganin yanda mutane ke shige da fice. Assad na gaba yana masu jagora yayinda Maleeka ke take masu baya.. Sady dai sai rabe raben idanu take tana kallon kanta a wajen da bata tab’a tsammanin zatazo ba.. Suna tafe ta hangosa yana tsaye k’ofan wani Office kansa kife yana duba wani file.. D’ago kan da zai suka had’a idanu.. Take taga annurin fuskarsa ya kuma d’aukewa, Ta lura mutumin kaman haushinta yakeji, Ta kula baik’i ya sami wani dalilin da zaisa ya jefata kurkuku ba.. Take ta shiga b’oyewa bayan Maleeka tana k’ok’arin b’oye fuskarta tana lek’ensa.. Tana ganin Assad ya isa garesa yana nuna masa wani k’aramin d’aki mai kaman office.. A tare suka shige Assad d’in nayima Maleeka alama da hannu kan su k’araso.. Office ne madaidaici mai d’aukeda table guda biyu, d’aya table d’in wani mutum ne zaune da computer gabansa wanda take tinanin shima d’ansandan ne.. Sai d’aya table d’in kuma wani mutum ne zaune da takardu gabansa da k’aramar cup wanda pens ne da dangin abin rubutu ciki. Umma bata shigo office d’inba saiko Sadiyar. Addu’a take Allah Sa kar wannan mutumin ya shigo.. Aiko bata ida addu’an ba Ta gansa ya shigo yana amsa waya.. Assad yai mata nuni da wani kujera yace ta zauna.. Babu musu ta k’arasa ta zauna. Mutumin dake gaban computer shike tattara bayanan da Sadiya keyi cikin computer d’in yayinda d’aya Mutumin dake zaune gaban table d ya shiga shirya takardunsa alamun yana jira ta suffanta masu kamannin Kawun Sagir.. Assad yai mata umarni data fara bayani.. Yanda take masu bayanin a tsorace yasa mutumin bai fahimci komai ba, tana kuma d’agowa idan ta dubi Mu’azzam sai ta kuma daburcewa ta rasa bayanin da take.. Assad ya lura da hakan, ya d’ago yana duban Mu’azzam ya kuma dubi Sadiya dake satan kallonsa. D’an sosa kunnensa kad’an Assad yai kafin ya dubeta yace “Are you alright..?” Girgiza masa kai tai alamun a’a.. “What’s the matter then.?” Ya tambaya yana dubanta. Satan kallon Mu’azzam da ta kumayi yasa Assad murmusawa kad’an kafin ya k’arasa yanda Mu’azzam yake ya d’an janyo Mu’azzam d’in da har lokacin waya yake yana tsaye jikin window.. Cikin dabara Assad ya fiddashi daga cikin office kafin suka samu full attention d’in Sadiya.. Ai kuwa suna fidda Mu’azzam daga office d’in suka samu full attention d’in Sadiya, tai masu bayanin kamannin Kawun Sagir tiryan tiryan.. Mai zana hoto ya zano kamannin data fad’i.. A daidai lokacin Mu’azzam da ya ida wayan da yake ya turo k’ofa ya shigo.. Bai wata wata ba ya isa table d’in yana duba zanen wanda ba fuskan kowa bane ya bayyana face Danger.. Wani irin huci kurum Mu’azzam yake yana dunk’ule hannunsa, lokaci guda ya bugi table d’in yana furta “I knew it.!” Lokaci guda ya fuzgi takardan ya fice daga office d’in cikin tsananin b’acin rai sai sakin huci yake kaman zai kifa k’asa... Cikin sauri Assad yabi bayansa dan yasan komai ka iya faruwa tsakanin Mu’azzam da Chief Inspector. Hankali tashe Assad ke k’ok’arin taresa ko kula Assad baiba har saida ya daki k’ofan Office d’in Chief.. Chief na cikin waya yana kwance cikin kujerarsa mai juyawa sai ganin Mu’azzam yai akansa yana sakin huci kaman wani mayuwancin zaki.. Babu shiri Chief ya katse wayar da yake yana duban Mu’azzam da tsananin mamaki “How dare you barge into my office.. Who do you think you are..!” Cikin tsananin b’acin rai Chief yake maganar yana duban Mu’azzam dake tsaye gabansa idanunsa babu alamun tsoro.. Lokaci guda Mu’azzam ya d’ago Sketch d’in yana nunama Chief “Do you still have any reason to depend this criminal..?!” Ko ba’a fad’a maka ba tsoro ya bayyana a fuskar Chief Inspector amma Sai ya dake yace “Kai k’aramin maras kunya. Kasan da wanda kake magana.. Naga irinka dubu kuma na gama dasu..” Baikai aya ba Mu’azzam ya katsesa da fad’in “Bakaga irina ba kuma kafin kaga irina sai na tabbatar na gama dakai..” Wannan karon murmushi Chief yai yace “Mind your language boy.. Bakada hujjan cewa na kare mai laifi domin kuwa dani da kai bamu San wanene Danger bamusan he’s connected to crime d’in nan ba sai yanzu...” Ya murmusa kad’an kafin yace “Har yanzu kaid’in yaro ne a gidan nan.. Har yanzu bakasan yanda Al’amara ke gudana a gida irin wannan ba.. You’re lucky, you’re from well known and respective family, I should’ve thrown you out cikin k’ask’anci . Now, get out of my office befor you lose everything .. Including your career as a police officer..!” Ya k’arashe muguwar murmushin saman fuskarsa.. Daidai lokacin Assad ya shigo a rud’e yana neman afuwan Chief on behalf of friend’s behavior.. Mu’azzam kaw har lokacin huci kurum yake yana duban Chief Inspector da idanunsa da tuni sun gama rinewa.. Chief ya dubi Assad d’in yace “Take him out.. Fitar dashi daga nan..!” “Don’t touch me.. Don’t you dare touch me..!” Mu’azzam yai kashedi ma Assad kafin ya dubi Chief yace “Wata rana zamu had’u..! Alk’awari ne..!” Daga haka juyawa yai ya fice zuciyarsa na masa tsananin k’una.. Assad zai magana Mu’azzam ya d’aga masa hannu alamun dakatarwa “Not now Assad.!” Fuzar da fuci kurum Assad yai kafin yabi bayan Mu’azzam d’in... Su duka hud’in suna tsartsaye sunyi carko carko.. Suna kuma duban hoton Danger da ya bayyana cikin sketch d’in.. Assad ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243