Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 171

Chapter 171

Gidan Aro Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Sadiyar ta sakar mata murmushi tace “Ya kika tsaya daga waje.. Mu k’arasa ciki mana.. Allah yasa da alkhairi kika Zo..” Safeenah taci gaba da k’are mata kallo tin daga sama zuwa k’asa kafin ta murmusa tace “Ba shiga nazo yi ba. Zuwa nai na baki sak’o..” Sadiya ta murmusa kad’an tace “Toh banda abinki nan fah gidan Yayanki ne kinga ai bazan hanaki shiga ba matuk’a ba da tashin hankali kika Zo ba..” Safeenah ta murmusa mai sauti tace “Kar ki nuna mun bariki yarinya.. Tar nake kallonki.. Ki gama duk wani iskancin da kutungwilarki na d’an lokaci ne.. Naji dad’i da kika San cewa ni da shi tushe guda ne.. Kece bare a tsakaninmu.. Har abada mu zamu tab’a rabuwa ba.. Domin kuwa akwai jini mai k’arfi da ya had’amu..” Ta saki murmushi tana mai d’aura hannunta saman flat tummy d’inta da kaman babu komai ciki.. Lokaci guda take ci gaba da fad’in “Shin kin tambayi mijinki jiya da wa yake tare a daren jiya..?” Ta wani rausayar da idanu kafin taci gaba da shafa cikin nata tana fad’in “Koda yake naga kinata kiransa amma yanata katse kiran naki.. Toh Maiyasa ma bazai katse ba alhali yana tsaka da jin dad’insa..” Izuwa lokacin k’wallan da Sadiya keta k’ok’arin dannewa Sun gama ciko idanunta.. Safeenah tai murmushin cin nasara ganin yanayin Sadiyar ya sauya gaba d’aya. Lokaci guda taci gaba da fad’in “My Halal bazai tab’a rabuwa dani ba.. Ni da shi are one.. Haka kikazo kika samemu kuma haka zaki fice daga rayuwarmu ki barmu tare kaman dai yanda kika samemu tare.. Kinsan Maiyasa..?” Ta k’arashe tana kuma matsowa kusan Sadiyar kafin ta janyo hannun Sadiya guda ta d’aura saman cikinta.. Murmushi bai bar saman fuskarta ba take duban Sadiyar wacce ta daskare tana kallon hannunta da Safeenah ta aza kan cikin ita Safeenar “Akwai ajiyar shi a cikin nan.. Zan bashi abinda babu wata mace da ta tab’a bashi a duniyar nan.. Product na soyayyarmu ne a cikin nan.. Tab’a kiji da kyau ki tabbatar da hakan... Kar kiga laifinsa , Kinsan mace mai juna tana buk’atar kulawa na musamman sann jariri na buk’atan d’umin mahaifinsa dole ya katse kiranki..” Sadiya tai azaman fincike hannunta daga saman cikin Safeenah tana goge hawayen da suka shiga gangaro mata. Safeenah Ta kuma murmusawa kafin taci gaba da fad’in “ Dama na fad’a miki gidana tamkar GIDAN ARO yake a wajenki.. Mijina nawa ne.. Ni kad’ai.. Ki fara k’irga kwanakin ki a gidan nan domin kuwa kwanakin ki a gidan nan K’ayaddadu ne.. Zaki fice ki bar mun Gida kaman dai yanda na miki alk’awari.. Bari dai muga mai zai faru yanzu..” Ta k’arashe a daidai sanda ta hangi motar Mu’azzam ya karyo layin.. Safeenah Ta silale nan wajen, tai saurin jifa da takalmanta gefe.. Ta kama k’asan rigarta ta keta.. Ta d’aura hannunta guda akai d’aya kuma ta aza saman kwamkwasonta daga nan ya da take duk’e gaban Sadiya. Ta shiga zunduma ihu tana kame cikinta tana kuka “Wayyo sun kwance mun karnuka.. Wayyo cikina.. Wayyo zan mutu.. My baby.. I don’t want to lose my Baby.. Wayyo Allah na..!” Sadiya tai tsaye Cak cikeda mamaki tana kallon wani irin makirci da bata tab’a arangama da irinsa ba.. SameenaAleeyou📚 *GIDAN ARO* *63* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Hango Safeenah zaune darshan a k’asa da yai ya sanyasa saurin taka birki. Babu shiri ya bud’e marfin motar ya fito ya nufosu cikin sassarfa, ga Sadiya tsaye gabanta tamkar wacce aka dasa. “Feenah.. Ke Safeenah lafiya.. What’s going on here..?” Ya tambaya yana k’arasowa. Safeenah ta kuma kame bayanta tana nishi da k’yar “Wayyo.. Wayyo Allah na.. Karnuka Ta sakar mun.. Wayyo na shiga uku.. Wayyo zan mutu.. Bayana.. Marata..” Cikin kuka taci gaba da nuna Sadiya tana fad’in “Gata nan.. Itace tasa mai gadinka ya kwance mun Karnuka.. Ni banyi niyyan zuwa gidanka ba amma dashike inada appointment da Dr tau shine na taho muje tare tinda kaima Kanada iko akan D’anka kuma ka canci kasan dik abinda ake ciki... Shine wann matar taka tasa security man ya kwance mun Karnuka.. Dama ba yau bane kawai Ta tab’a mun haka.. Ranan ma ta mun haka harda cewa ni mayya ce Ina bibiyanka bayan ka sakeni.. Ai ko da ace Babu aure tsakaninmu nan fah gidan D’anuwana ne zan iya zuwa gidan nan..Amma shine ta kwance mun Karnuka saikace wata b’arauniya, wllhi da k’yar nasha.. Wayyo cikina..!” Ta kuma kurma wani ihun daidai sanda Patrick ya fito da Karnuka.. A nasa tinanin Safeenah ta tare Sadiya ne da fad’a shine ya fito da Karnukan dan ya mata barazana kaman yanda suka mata wancan ranan. Patrick ya turo gate yana rik’eda Karnukan yake fad’in “Ma’am Ta tafi ko na sakar mata su Danny su tayata shawagi..” Yai birki wa kalamansa sakamakon hango Mu’azzam da yai. Safeenah ta kuma sakin ihu tana rarrafawa Ta isa bayan Mu’azzam Ta rik’e k’afafunsa tana b’uya tana fad’in “Ka gani ko.. Kaga abinda nake fad’a maka koh.” Wani irin tsawa ya dararawa Patrick wanda saida yasa Patrick sakin chain d’in wuyan Karnukan dan tsoro dan shi sam baisan Mu’azzam d’in ya iso ba.. “Are you stupid.. Ashe kai mahaukaci ne..!” Cikin fad’a fad’a yake maganar wanda zai tabbatar maka ransa a b’ace yake. Patrick fad’i yake “Sorry Sir.. I.. I didn’t know.. You..” “Shut up.. Just shut up.!” Mu’azzam ya kuma daka masa wani Tabawan. Sadiya dake Hawaye bud’e baki tai da niyyan magana ya dakatar da ita ta hanyar d’aga mata hannu “Banson jin komai, ki shige gida yanzun nan.!” Ta saki baki tana kallon ikon Allah. Ta girgiza kai tace “Amma...” “Bakiji mai nace bane..? Ko kurma ce ke..? Kina iya adana bayanan ki har na dawo..Please.” Ya k’arashe yana mai janye idanu daga barin dubanta. Take taji hawayen na zuwa mata gadan gadan, Jiki babu laka Ta nufi cikin gidan, yayinda Patrick keta k’ok’arin basa hak’uri yana janyo igiyan wuyan Karnukan. Ta jikin gate Sadiya Ta mak’ale tana hange Safeenah dake kuka Mu’azzam na tambayarta ko zata iya tashi.. Wani sabon kuka ne taji yazo bakinta. Safeenah ta girgiza masa kai tana hawaye “I can’t.. I can’t walk.. Wllhi bazan iya ba.. Ni da nasan Karnuka za’a kwance mun a gidanka wllhi da bazanzo ba in the first place..” Kuka ya hanata ci gaba da magana, tana hawaye tana shafa cikin take fad’in “Our Baby Mu’azzam.. I don’t want to lose our child.” “Ya isa haka Kimin shiru..” Ya fad’i yana d’aukanta Cak cikin hannunsa. Sadiya Ta kuma fashewa da kuka ta nufin cikin gidan a guje kukan na fin k’arfinta. Patrick ya bita da kallo cikeda tausayawa dan shi kanshi yasha mamakin tuggun da Safeenah ta k’ulla. Motar Safeenar Mu’azzam ya shigar da ita gefen mai zaman banza kafin ya zagayo ya zauna a mazaunin driver. Sai matse ido take kaman da gaske tana jin jiki, tana yi tana satan kallonsa yanda ya kai matuk’a wajen tsimewa. Ya daidaita zamansa saman kujeran ya soma driving. Safeenah na kuma sakin sabon kuka tana fad’in cikinta. Birki ya taka wanda saida ya sanyata had’iye kukan nata cak, ta d’ago tana dubansa a tsorace. “Safeenah..!” Ya fad’i a hankali idanunsa naga kwalta. Ta saci kallonsa kad’an. Lokaci guda yaci

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});