Chapter 215
Chapter 215
a halin yanzu.. Shekaru sunja amma shi gani yake Noor d’insa bata canza ba, itace dai wancan Noor d’in da ya tsinceta ya kuma ambaceta da *Haske*.... Kuka yaci k’arfin Daddy dake binta da kallo daga sama zuwa k’asa tayi shiga tsaf cikin tufafi irin na Larabawan k’asar Sudan.. Mu’azzam dake takowa da k’yar yana jin kaman bazai iya jan k’afafunsa ba.. Tsananin Shock d’in da ya tsinci kansa ciki baki Bazai iya fad’i ba. “Ma..Mam..Mamy.. Mamy.. It is you.. You.. You can walk again..!” Ya fad’i cikin tsananin rawar murya mai rarrabewa lokaci guda ya rungume mahaifiyarsa yana mai fashewa da wane irin kuka, kuka mai ban tausayi.. Kukan da ya jima tare cikin k’irjinsa.. Kukan da ya jima yana son ya fidda.. Kukan da ya tara for over 15years.. Yanda kasan k’aramin yaro haka ya rungume mahaifiyarsa yana kuka sosai kuka mai sauti wanda ya sanyaya jikin duk wani mahaluk’i dake wajen. Itama d’in rungumesa tai sosai tana kuka saidai nata kukan maras sauti ne ba kaman na Mu’azzam da ya kasance mai sauti ba wanda kowa ke iya sauraro. Ta tallafo fuskar Mu’azzam da har lokacin akwai alamun jini, Ta kai dubanta ga kafad’arsa yanda shima akwai alamun ciwo.. A hankali ta saka yatsarta tana goge jinin dake fita daga gefen bakinsa hawaye saman fuskarta, ba tare da ta furta komai ba take tallafe da fuskarsa tana ci gaba da goge masa hawayen fuskarsa da ya had’e da jini. Ya tallafi fuskarta shima yana dubanta hawaye naci gaba da gangaro masu Su duka biyun. “Mamy.....” ya kuma furtawa cikin tsananin rawar murya yana dubanta.. Sake rungumar mahaifiyarsa yai wani kukan na kuma kufce masa. Abun ne tamkar ba a zahiri ba tamkar dai a mafarki. Daddy da kansa ke kife, a hankali ya d’ago hawaye na gangaro masa yana duban Mu’azzam da mahaifiyarsa gwanin ban tausai. Kowa a wajen dubansu yake cikeda tausayawa hawaye na gangaro masu. Harta Uncle Salman dake tsaye gefe shima saida yai hawaye. Mama Hindu dake tsaye gefen Mamyn hawaye ne itama ke gangaro mata cikeda shauk’i... Kai harta Ajidde da tak’i jinin Kofur Zalimu saida taji hawaye na gangaro mata.. Dik son kallo irin na Ajidde balle ma ta tsinci kanta a gida irin wanda bata tab’a gani ba a zahiri kayan tausayin da taci karo dashi bai barta Ta tsaya kalle kalle ba. Allahu Akbar! Allah abin godiya, buwayarsa gagara misali. Yau ga Nuratu tsaye kan k’afafunta cikin gidan da akai mata lak’abi da GIDAN ARO. Farkawan da Mommy zatai sai ganinta tai kwance saman carpet a tsakiyar parlorn Daddy.. Ta soma d’ago kai tana duban mutanen dake zagaye da parlorn d’aya bayan d’aya. Fuskar Daddy Ta soma gani kafin ta dubi na Mu’azzam, ta dubi na Inne dake zaune daga can angle d’in, sann ta dubi Uncle Salman... Lokaci guda kuma Ta sauk’e dubanta kan Nuratu dake zaune gefen mijinta Mu’azzam na zaune daga k’asa gefen k’afar mahaifiyar tasa. Irin duban da Mommy taga yana mata yasa hanjin cikinta murd’awa. Mommy na zaune wajen sai ta soma k’ok’arin fashewa da kuka tana girgiza kai ganin yanda kowa ya zuba mata idanu alamun farkawarta ake jira. Tabbas yau rana ce na tonan asiri. Allah ka rabamu da jin kunya duniya da lahira. Ameen. Mommy ta aza hannayenta aka Ta soma kururuwa tana fad’in ta shiga uku. Sai kuma ta mik’e zataci gaba da hauka. Tana fad’in “Ba haya..! Ba haya zanyi.. Ku barni na fice kar na zuba a nan..!” Saidai ko gizau babu wanda ya motsa sai dubanta da suke. Wann karon Nuratu ce ta taso ta matso kusan Mommy daketa tsalle tana kame cikin Ta tana ihun ba haya. Ta saka hannayenta duka biyu ta rik’o hannayen Mommy dasu. Mommy ta Ware idanu tana duban Nuratu da yanda Ta rik’ota. Murmushi saman fuskar Nuratu take furta “Baki tunanin yayi kusa Hajara.. Yaushe garin ya waye balle har daren yayi..?” Cikin wane irin yanayi Mommy ke duban Nuratu dake murmushi tana rik’eda hannayenta. Tai yunk’urin cire hannayenta daga cikin na Nuratu amma saidai bata sakar mata ba. Ta tsareta sosai da idanu “Ni ce fah Hajara.. Kishiyarki da kika kwashe shekaru ak’alla shabiyar Kina d’awainiya da ita.. Maiyasa zakiji tsorona..? Maiyasa zakiji gujeni..? Ki kwantar da hankalinki Abubakar ya tafi gidansa na Gaskiya ya bar GIDAN ARO kuma bazai tab’a dawowa ba.. Ya tafi yanda dani dake da koma wanene bamuda haufin wataran duk zamu tafi..” Mommy ta girgiza kai cikeda daburcewa tana fad’in “Amm..Amma Maiyasa kika sanya fararen tufafi kika shigo motar sa.. Na tabbata Kinyi haka domin ki razaneni ki kuma fiddani daga gidana kaman yanda na fiddaki.” Ta fad’i cikin rawar murya irinta mai kuka. Aunty Nuratu Ta murmusa kafin tace “Allah sarki.. Ashe har akwai abinda zai baki tsoro a wann duniyar Hajara.? Lallai wann abu ba k’aramin abu bane.!” Mommy ta shiga girgiza girgiza kai tana hawaye “Bai kamata ki tashi ba Nuratu.. Boka yace tashinki na nufin kwanciyana ne.. Nuratu Maiyasa kika tashi bayan na mik’a ki ga masu magani na bogi, ‘Yan bori da rufa ido Wanda nakeda Tabbacin babu abinda maganinsu zai miki saidai ma ya k’ara miki kan uk’ubar da kike ciki.. Nuratu gidana da mijina sun haramceki Maiyasa kika dawo cikinsa.. Kin mance na fad’a miki gidana tamkar GIDAN ARO yake a wajenki zaki fice, kuma kin fice kaman yanda na miki alk’awari.. Amma ban miki alk’awarin zaki dawo cikin gidana ba Nuratu.!” Ta k’arashe tana girgiza kai hawaye d’aya na bin d’aya. Aunty Nuratu ta murmusa tana duban Mommy wacce itama d’in ita take duba suna fuskantar juna “Kin mance cewa waraka baya hannunki Hajara.. Na Allah ne mai yin yanda yaso dabayinsa.. Dani dake da duk wani abin halitta a GIDAN ARO muke Hajara.. Duk daren dad’ewa zamu tafi gidan da kikaita k’ok’arin turani, amma saidai Watak’ila lokacin tafiyan nawa ne baiyi ba.. Hajara, tsawon shekaru goma shabiyar da kika kwashe da sunan Kina min abinda duk akewa majinyaci, ina sauraronki da duk sunbatunki akaina.. Sann na rok’i Allah da ya nuna min ranan da zaki bud’e bakinki ki fad’i duk abubuwan da ki aikata ma ahalina kafin na bar GIDAN ARO..” Ta d’an juyo ta dubi Daddy daketa dubanta, Sai kuma ta maidoda dubanta ga Mommy tace “Ba gidan mijina ba. Ina nufin duniya, wanda dani dake da koma waye zamu bari dik daren dad’ewa.” Mommy Ta had’iyi miyau da k’yar tana mai rimtse idanu, tana jin wani abu kaman k’urji ya tokare mata mak’oshi. _WAIWAYE_ Tin bayan da Marwan ya auri Hajara babu wata aba mai suna soyayya tsakaninsu, dama auren nasu ba wai yana so bane ya kasance sai dan babu yanda ya iya da tayin da abokin Babansa yai masa wanda shine Baban Hajara. Marwan yakan kai aike Daga wajen mahaifinsa zuwaga Baban Hajara Malam Ba’i wanda shi dama baida wani k’arfi. Abinka da mutanen da, ga yawan alheri da kamanta rik’o da uzumunci tsakani da Allah... Yawan aike gidan da yake kaiwa daga wajen mahaifinsa zuwa wajen Baban Hajara dake Birnin Yola dan dama su Hajara a cikin garin Yola suke, a nan Hajara Ta k’yalla idanu akan Marwan, nan taji gidan duniyar nan babu wanda take so irin Marwan, shi kuma tinda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243