Chapter 228
Chapter 228
Ta k’arashe cikin rawar murya. “Dama bata k’ullaceku ba.. Kin San maiyasa sabida bata yarda Bokanku da malaminku zasu iya cutar da ita ba face abinda Allah ya k’addara zai sameta.. Kije ki rok’i Ubangijinki gafara domin shi kuka sab’a.. Allah ya datar damu baki d’aya.” Hajiya Faty Ta kuma jinjina kai tana hawaye. Daidai lokacin driver d’inta ya k’araso dan Dama kusa yake. Ta kuma yima Mu’azzam godiya ta wuce. Shafe fuskarsa ya kumayi kafin ya shige motarsa ya d’auki hanyar gidansa. Wanka yai ya shirya cikin k’anan kaya kafin ya kuma fitowa ya d’auki hanyar Annoor Masjid dan yaji dad’in karatun da ya saurara wancan ranan, ya k’udiri niyyan da izinin Allah karatun bazai dinga shigesa ba, da yawan maza idan suka d’an girma suka zama samari sai kaga shikenan sun daina neman ilimin addini wanda wasu sam basu ma samu wadataccen ilimin addinin da k’uruciya ba. Ba’a girma ma neman ilimi musamman na addini.. Kar mutum ya shagala da neman duniya, ya kamata ya sami lokaci na musamman ya ware domin tanadi ma gidansa na Gaskiya. Tare dashi akai karatun bai bar masallacin ba sai bayan isha.. Daga nan kai tsaye gidan Daddy ya nufa. ** Umma tai K’uri tana duban Yayarta yanda ta gyara ma Kiki dake kwance saman gadonta kwanciyar nata, ta rufa mata bedcover tana shafa kan yarinyar a hankali cikeda tausayawa. Umma sai dubanta take tana murmushi tana tuno lokacin da suke yara yanda Aunty Nuratun Ke kula da Ita kaman dai yanda yanzu take kula da Kiki. Umma Ta bud’e murya tace “Baki canza ba Yaya.. Har yanzu Kina nan da zuciyarki mai kyau, Kina saka Farin cikin kowa a sama da Naki.. Sai na tuna a lokutan baya yanda kikaita d’awainiya dani.. Tin mahaifan mu suna da rai Kina kula dani sann ko bayan da basu nan baki fasa duk abinda kikeyi ba sai ma k’arawa da kikai.. Mu’azzam takes after you.. Bayan babu Ibrahim shi yaci gaba da kula damu..” Aunty Nuratu ta k’araso tana murmushi kafin ta kamo hannayen ‘Yaruwar nata cikin nata “Haka ya kamata mu kula da junanmu, wann shine cikan zumunci..” Ta d’anyi fasali kafin taci gaba da fad’in “Shin Kinsan Sadiya ta kula dani a lokacin da nake kwance a can Fufore.. Bansan dalili ba amma inajin nastuwa had’ida k’wanciyan hankali tattare da ita na d’an lokacin da mukai tare.. Ashe kusancinki ne nakeji a tareda ita.. Babu wanda ya kaini farin ciki da d’iyar ‘Yaruwata kuma mai sunana Ta zamto matar Mu’azzam.. Allah ya albarkacesu da Zuri’a d’ayyiba wanda mu dasu da al’umma baki d’aya zasu amfana dasu.” Umma ta kuma murmusawa kafin tace “Ameen Yaya..” Ta gyara mayafinta tana k’ok’arin mik’ewa. “Wai da gaske tafiya zakiyi Aysha.. Shin bazaki zauna a nan ba.. Su Asheer da Habeeb sai a kawo su nan duk ku zauna a nan gaba d’aya.” Umma ta murmusa kad’an tace “Bari dai al’amara su gama daidaita Yaya.. Da sannu zakiga Habeeb da Asheer, nima ba don naso zan tafi na barki ba..” Ta d’anyi fasali kafin taci gaba da fad’in “Kinga ga yanda yanayin gidan yake ciki komai a rikice.. Abubuwa suna kan faruwa, ya kamata mu baku sarari har Allah ya daidaita al’amran ahalin..” Aunty Nuratu ta murmusa kad’an kafin tace “Haka ne, kuma kawo Asheer da Habeeb a wann hatsaniyar da ake ciki bazai ma yaran dad’i ba duba da yanayin da ake ciki a gidan, ko Ina jami’an tsaro ga Hajara bamusan makomarta ba har yanzu dan babu alamun nadama tattareda ita. Allah dai ya iyar mana ya kawo mana k’arshen tashin hankalin nan.” Umma Ta amsa da Ameen Yaya. Daidai nan Aunty Larai tai sallama a k’ofa.. Mamy ta bata izinin shigowa.. Nan take sanar dasu Adnan na jiransu. Umma ta dubeta tace “Sadiya fah.?” “Bacci take can b’angaren Inne.. Inne tace a barta kar a tada ita.” Umma ta girgiza kai kad’an tace “Oh shikenan tanata yawo tsakani, daga gidanta ta tafi can yanzu kuma ta taho nan..” Aunty Nuratu ta katseta da fad’in “Nan da can da gidan nata duk d’aya ne.. A k’yalemun d’iyata dan dama ko zarafin gaisuwa bamu samu ba balle muyi hiran yaushe rabo.. Kudai kuje abinku ku bar mana ita a nan..” Umma ta d’an girgiza kai kad’an tana furta “Shikenan Dama d’iyarki ce kunfi kusa.” Suka d’an murmusa gaba d’aya kafin suka nufo waje suna kuma sallama da juna kaman kar Su rabu. ** Tsaye yai k’ofan store d’in da Mommy Ke kulle yana sauraron surutanta. “Dan Allah kuyi hak’uri.. Wayyo hannu na.. Wayyo Kaina..! Wayyo bayana.. Kar ku tab’ani.. Wayyo.!” Ta kuma sakin wani ihun. Mu’azzam yana bud’e k’ofar ya hango Mommy tsugune tana rok’on a k’yaleta. Amma da shike gogaggiya ce tana ganinsa sai ta d’auke kai gefe tana sakin huci. “Fito” ya Fad’i daga nan yanda yake tsaye. “Mahaukaciya ce ni da zan fito ka sunkuceni ka tafi dani ofishinku.. Tsaf nasan a Rashin mutuncinka zaka aika Mu’azzam.” Jinjina kansa yai kad’an kafin ya soma k’ok’arin janyo k’ofar.. Da sauri ta rik’e k’ofar ta fito tana fad’in “Nuratu ce tamin turen makarai dan su hanani zaman Gidan nan.. Kuma wllhi bazan fice daga gidan nan ba.. Zama daram babu uban da ya isa ya fitar dani.. Yo ko Marwan wllhi bai isa ya fiddani ba balle Nuratu.” “Idan basu fitar dake ba dama ni zan fitar dake.” Ya bata amsa daga nan yanda yake tsaye. Ta murmusa kad’an tana dubansa tsegege “Zaka fitar damu dai.. Dan kana kamani zaka kama kakarka.. Yo ai itace mai laifi.. Nikam burin Marwan da Nuratu na cika zasu samu daman kasancewa k’ark’ashin inuwa guda bayan amanarsu da mahaifinka yaci.. Mai za’ai da ahali irin wann wanda banda ‘yantadda da maciya amana babu komai cikinsu.. Kakarka criminal Babanka betrayal wanda yaci amana D’anuwansa.!” “Ya isheki.. Ya isheki haka..!” Ya dakatar da ita cikin tsnanin fuci. Lokaci guda yaci gaba da nunata da ‘yar yatsa “Don’t you dare mention my Dad..! Kar ki sake.!” Mommy ta rakasa da harara yanda yasa kai ya fice cikin sauri. Dogon tsuka taja kafin ta nufi saman Daddy tana fad’in “Na rantse da Allah Marwan baka isa kaci amanata da Nuratu ba.. Ina nan na kasa na tsare.. D’akinka ma zan shige na jira shigowarku ayi komai akan idona. Maciya amanan banza.!” Ta k’arashe tana mai tura k’ofar d’akin Daddy. * Mu’azzam na ficewa ya k’arasa saman kujerun shak’atawa dake a haraban gidan, yai zaune yana tunanin maganganun Mommy, Babansa maci amana ne yaci amanan D’anuwansa.. Ya saka tafukan hannayensa duka biyu yana mai shafe fuskarsa dasu. Daddy shine asalin masoyin mahaifiyarsa amma sai Dad d’insa ya aureta.. Shin da gaske Dad d’insa maci amana ne..? Bai kaiga samo amsar ba yaji hannun mutum saman kafad’arsa. D’agowa yai yana duban Daddy dake tsaye saman kansa. Bai iya furta komai ba Sai sadda kansa k’asa da yai. Daddy ya zauna gefensa kad’an yana mai d’aga kai sama had’ida duban hasken Farin wata da ya fito tarau. Suka b’ata lokaci a haka kafin Daddy ya soma fad’in “Shin kasan ko wani namiji ana halittan matansa ne daga ribs d’insa.?” Mu’azzam ya d’ago ya dubi Daddy da mamaki dan gani yake kaman Daddy ya fahimci tunanin mai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243